← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 190

Sashe 44

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji né zaune a office babu abinda yake Sai tunanin halin da suhail ke ciki, physically yana nunawa he don't care amma deep inside he's boiling, tunda yake da suhail bai taba Jin tausayinshi ya Kama shi ba sai Yanzu, mussanman ya da ya fita hayyacinshi saboda ita, the most scary part shine the wuya Maryam ta amince dashi har ta so shi ayi maganar aure. This whole thing is above him, he wish there's something he can do, bai San irin wannan kaddara ba, he remembered duk sanda zai tafi abroad sai suhail yace dad ka gaidamin Maryam and abun mamaki ga Maryam tazo in another form and still he fall inlove with her
"Oh Allah ka Taimaka min...ka tausayawa Dan nan...let him not suffer for love..." Ya fada ahankali, tunawa yayi da alhaji Mahmoud, gani yake alhaji Mahmoud zaiyi tunanin it's a set up. Jiki ba kwari ya dauki waya ya Kira innarshi, bayan tayi piçking sun gaisa yake cewa
"Inna suhail yana nan tafe yau..." Da sauri inna tace
"Aaaaa Ashe yau zanyi babban bako..yau Mai sunan Larabawa zai zo..Kai amma na ji dadi..aikoshi kayi ko haka nan zaizo?.." Ta tambayeshi sounding very excited,
"Wani abune tafe dashi..." Alhaji ya fada cikin sanyinmurya,
"Wane Abu?" Inna Ta tambayeshi, nan alhaji ya fada mata abinda ke faruwa amma bai  fada mata ko ita wacece ba Don ya San girman amana kuma alhaji Mahmoud yace mashi kar ya fadawa kowa ko ita wacece,
"Ikon Allah...to me zai Hana ka fada mashi inda take yaje ko sun sasanta kansu..." Inji inna
"Ai inna yarinyar amanace..." Alhaji ya amsa mata,
"To wai ba'a auren yar amana?... Ai ba iskanci yace zaiyi daita ba...nidai gaskiya in har kana da daman da zaka aurar daita kawai ka bashi Don dukda wannan yaron bai da mutunci banason ya wahala..." Inji inna, ajiyan zuciya alhaji ya saki Sannan yace
"Gaskiya ni bani da daman aurar daita...kawai in yazo ki fada mashi cewa tayi tafiya amma zata dawo rana nan da sati biyu...kinga lokacin anyi bikinmu da salima sai in maidota gidan ta zauna...Dan Allah inna..." Ya fada yana begging dinta, shuru inna tayi for a moment Sannan tace
"Yanzu da tsufana zakasani Inyi karya?.. In ya gano ba da gaske nake ba fa?.. Kasan halin wannan Mara kunyar yaron..banason yazo ya tada min hankali.."
"Inna ki kwantar da hankalinki...babu tashin hankali da zai nuna maki..kawai ki fada mashi abinda na fada maki...in yayi ba daidai ba ki kirani..." Alhaji ya fada mata, ba Don inna taso ba Ta amsa mashi da tou amma har ga Allah tsoro takeji Don bata mantawa yana yaro aka kawosu Hutu ya dinga binta da wuka yana cewa ta Kira dad ya maida su Kano, tun lokacin ba'a Kara kawo su ba sai in su gandaman zuwa, shi kam sai ya shekara uku bai taka katsina ba sai in matsa mashi dad yayi.

Maryam kam Yanzu har Dan kiba tayi Don she's enjoying again, kullum Salman zaikawo masu abinci sau uku sannan Tana baccin enough bayan sallah asuba Don babu zancen gyaran dakin suhail ko bashi abinci kaman yanda ta Saba, agogon dake dakin ta kalla Sannan tace
"Dan Allah baba..if Salman comes ki Bari ya shigo yau..." Ta fada Tana marairace fuska,
"Aa..Alhaji bai amince ba..cewa yayi kar a bar kowa ya shigo...amma ki tambayeshi da kanki in ya Amince shikenan..amanar ki ya bani kuma bazan ci amana ba..." Inji baba, rabi, da turo baki tayi ta mike ta koma dakinta, Tana shi sannan Salman yayi knocking ya kawo abinci amma bata fita ba. Tasan Tana iya fita in taso ganin shi but she want to be a good girl kaman yanda dad dinta yake fada mata kullum.

Wani irin gudu suhail ya dingayi har ya Isa katsina, yana zuwa  unguwar grannies dinshi ya bata rai yana yamutse fuska yana tuki ahankali, daman bai taba son unguwar ba, inshort he can't believe dad dinshi was raise here. Yana zuwa bakin gate din gidan ya saki horn da karfi kaman yanda ya Saba. Inna dake zaune falo Tana sayan fura  Don bata abinci sai shi taji horn da ake bakin gate
"Allah ya kawo shi..." Ta fada, wani irin horn ya Kari da da karfi hajiya ta girgiza Kai Tana cewa
"Ai abun alfahari né danka ya auro mace Mai kyau Don ko ba komai a sama maka jikoki masu kyau amma kyawun hali fa...ha da son kowa kin Wanda ya rasa amma babu mutunci.  Ganin ba'a bude mashi gate ba yasa ya fito afusace yana cewa
"Wai gidan ban maigadi?..." Ya fada yana shiga compound din ta karamin gate, gani yayi babu kowa compound din, tsoki yaja ya za hannu ya ja sakata  gate yana cewa
"Greedy old woman duk kudin da dad ke baki you can't afford a gateman..." Ya fada yana bude gate din da kanshi, hannunshi ya kalla yaga it's dirty, wasu k'aya ya gani an shanya cikin compound din, cikin kasaita ya taka zuwa inda Kayan suke ya jawo daya ya goge hannunshi dashi tare da sakin Kayan kasa sannan ya dawo juyo ya koma waje ya shiga mota ya shigo da mota, bai tsaya maida gate ya rufe ba ya fito ya kama hanyar falon hajiya, yana shiga ya tarda masu fura uku gaban inna ita kuma sai Washe hakorantake wai ga  jikanta, ko kallonta baiyi ba ya bi masu furan da disgusting look suma sun zuba mashi idanuwa suna mamakin waye wannan gorgeous guy din,
"Ga Mai sunan Larabawa..." Hajiya ta fada sounding so excited, kujerun ya tsaya kallo yana néman inda zauna at the same yana bata fuska kaman Mai Jin warin wani abu,
"Ka zauna mana..Mai sunan Larabawa.." Inna ta fada mashi, kaman baiso ya Dan dosana bombom dinshi kam kujera, kallon masu furan yayi Sannan yace
"Ku tashi ku bawa mutane waje..." Ya daka masu tsawa, da sauri suka tattare suka mike daman inna ta gama siyayya shirin tashi suke, suna fita ya bi bayansu da harara, inna kwalawa Mai aikinta Kira tayi yarinyar ta fito da gudu, zata bude baki tayi mata magana suhail yayi saurin cewa
"Kuna da air freshener?.." Da sauri yarinyar ta  daga mashi Kai
"Je dauko min..." Ya umarceta, da sauri ta juya ta shiga ciki ta fito da Wilson bubble air freshener ta mika mashi, mikewa yayi ya fesa koina inna tayi zaune ta bude baki Tana kallon shi, sai da ya kusa karar da robar ya ajiye sauran tare dacewa
"Inna kin bi kin cika falo da yara sai tsami suke..kuma ahaka zaki sayi Abu hannunsu kici..." Ya fada Fuskanshi dauke da disgusting look, hajiya bata ce komai ba sai kallon shi da take ko kiftawa batayi, har ha Allah ko,sau daya bai taba bata haushi ba Don yana da shiga rai tun yana yaro haka yake,  murmushi inna tayi tare da girgiza Kai,
"Ina wuni.." Ya gaidata,
"Lafiya lau.... Dan Larabawa..ya kake ya Hutu?..." Ta tambayeshi cikin so da Kauna, kaman baison magana yace
"Lafiya lau...inna wurin Fatima nazo..nazo in maidata gidan mu..." Ya fada Kai tsaye,  murmushin karfi Hali inna tayi Sannan tace
"Ayya..ai jiya ta tafi wurin mamanta..." Bata idaba suhail ya hada giran sama d'ana kasa sannan yace
"Habawa..kin ma Fiddo né..." Ya fada yana mikewa, hanyar bedroom ya Kama yana kiran Fatima da karfi, baki inna ta bude Tana kallon ikon Allah,  saida ya duba dukkan rooms dake gidan yaga babu ita sannan ya yarda da gaske me bata gidan, na taje yaji zuciyar shi nayi mashi zafi, afusace ya dawo  yana cewa
"Inna in kina son gani Annabin rahama ki fadamin inda Fatima take...Dan Allah innata...wallahi zan baki ko me kikeso..." Ya fada kaman zaiyi kuka, inna kura mashi Ido tayi sai taji ya bata tausayi, cikin sauri ya dawo kusa daita har yana ball da kwanon furan inna ya zauna gefen ta tare da dafa shoulder dinta yana cewa
"Dan Allah inna..." Ahankali inna ta Kama hannunshi sai yayi saurin zame hannun tare da gogeshi da zaninta,
"Kin taba fura zaki taba ni?.." Ya fada kaman bashi bane Wanda ke begging Yanzu nan ba, ba karamin dariya ya bawa inna ba,  sai da tayi Mai isanta sanna tace
"Ka kwantar da hankalinka..zata dawo nan da sati biyu." Bata idaba suhail ya mike yace
"Nan da sati biyu da kikace?.. Ai lokacin nafi kwana goma da mutuwa Don in ban ganta ba yau da wuya zan Kai gobe...nidai Dan Allah ki taimaka..." Ya fada yana kokarin fashewa da kuka, inna ji tayi duk jikinta babu kwari, sai taji ta tsani alhaji daya kyale suhail yana wahala kan yarinyar.
Atakaice dai da kyar inna ta shawo kan suhail, kuma alkawari tayi mashi kan cewa Tana dawowa zata turota Kano wai kar ya Kara wahala yazo katsina, suhail Amsar number wayar yayi wai zai dinga kiranta yana Jin meye labari Sannan yace in har ta Kai nan da sati biyu bata dawo ba  zai dawo. Nan dai ya shiga mota ya Kama hanyar Kano jiki babu kwari zuciya babu dadi.

Yana dawowa gida ya shiga part dinshi ya kulle kanshi ya dinga rusa kuka Don gani yake hakan zaisa zuciyar shi ta samu sauki saboda irin radadin da yake ji Mara misaltuwa, hajiya na ganin motar shi taje bakin Kofan ta dinga knocking amma bai bude ba sai kukanshi kawai takeji, ba karamin tashi hankalinta yayi ba, masu gadi na zaune suna kallon ta, daman sai labarin abinda ya faru da safe Kawai suke.
Chapter 44 · 0% Book details