← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 190

Sashe 59

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Maryam kam har Dan bacci tayi cikin jet kafin su isa, Tana bude idanuwanta taga jet din na kokarin landing, wani irin ajiyan zuciya ta saki Tana lumshe idanuwa, daga nesa ta hangi dad dinta tsaye wearing three quarters da expensive polo hannunshi biyu cikin aljihunshi yana kallon jet dake landing, ahankali ya taka ya nufosu ita kuma she can't wait jet ya tsaya, bayan ya gama landing aka bude mata kofa, da gudu ta sauka cikin long hijab dake jikinta ta nufi dad dinta daya ware hannu yana tahowa, he can't just believe his eyes wai Maryam ce cikin long hijab har kasa,
"Thank you Allah ..." Ya furta under his breath adaidai lokacin da Ta fada jikinshi, dagata sama yayi Kama wata doll ya dinga rolling daita a sararin samaniya, sai da ya juyata son ranshi sannan ya direta ya sake hugging dinta, babu abinda bakinta ke fada sai
"I miss you dad...pls don't take me back..." Kawai take maimaitawa, ahankali alhaji ya daga jaw dinta yana kallon how dark and rough her is,
"Baby ansha Nigeria..." Ya fada cikin zolaya, nan take Maryam ta fashe da kuka Tana buga legs dinta kasa kaman yanda ta Saba yi mashi da, dariya alhaji Mahmoud yayi yana cewa
"I really miss this..." Ya fada yana Dora ta kan shoulder dinshi, bai direta koina ba sai cikin dining room inda almost duk maaikatan gidan ke tsaye holding flowers of different varieties, da sauri ta fada jikinsu daga Mazan har Matan Tana yi masu kiss tare dacewa
"I miss you..," su ma suna fada mata sunyi missing dinta, dining din ya kalla ta her favorite food jere kan dining, alhaji Mahmoud folding hannunshi yayi yana kallon how adorable she is wearing hijab, mika mata flowers suka dingayi Tana amsa Tana ajiyewa tare dacewa
"Thank you.." Duk Wanda ta amshi nashi sai ya fita, ahaka ta gama amsa duk suka fita ya rage daga ita sai dad dinta, babu abinda alhaji Mahmoud yake sai kallon flesh and blood dinshi then face dinshi dauke da wata murmushin Jin dadi, itama kallon shi kawai take, kallon rashes din face dinta yayi tare dacewa
"Baby skin color dinki have changed...weather Nigeria ya amsheki..." Ya fada yana driya, Dan buga kafatayi kasa Tana cewa
"Daddy...you're..." Bata idaba yace
"dear kina Kara turanci zan saka ki a jet ki koma Nigeria..." Yafada mata still smiling, da sauri tace
"Na daina turanci..."
"That's my baby...Yanzu Bari Inyi serving dinki..." Ya fada yana mikewa, ahankali Maryam tayi relaxing Tana kallon yanda dad dinta ke zuba mata abinci kawai sai suhail da mom dinshi suka fado mata, kawai sai ta saki murmushi, sai da ya gama serving dinta ta mike ta cire hijab tare da folding dinshi ta ajiye gefe daya Sannan ta jawo plate of delicacy dake gabanta ta hau ci kaman hungry lion da bai taba cin Nama ba, alhaji sai kallon ta kawai yake, sai da taci ta koshi tayi nat sannan ta kalli dad dinta dake kallon ta without blinking tace
"Nayi missing Kayan dadi wallahi.." Ta fada sounding funny, dariya yayi ya mika mata hannu, ahankali ta Kama, hannu ta komo kusa dashi, fuskantar kanshi yayi da kujerar ta yana kallon ta, hannunta ya kalla sai yaga babu nails, surprised look yayi mata tare dacewa
"Wow baby...kinbar ajiye gidan shaidan?... Kai am so happy..." Ya fada yana dariya, sa sauri ta rufe face dinta Tana murmushi sai suhail ya sake fado mata, she remembered irin kukan data sha ranar daya yanke mata fingers, hannunta ya cire yayi mata kiss yana dariya
"Now ki fadamin ya Nigeria..."
"Lafiya lau..." Ta amsa mashi,
"Tell me...oh baby na mance..kije kiyi wanka an freshen up sai kizo mu sha hira..." Ya fada mata, da sauri ta girgiza Kai tare dacewa
"No dad...inason fira da Kai..dad nayi missing Dinka...kuma ba kullum kake daukar call Dina ba..." Ta fada Tana turo mashi baki, dariya yayi yana cewa
"Am sorry baby na...the more Ina magana dake the more Ina missing dinki...now fadamin...waya tabamin ke a Nigeria?... Just tell me in kullesu duka..." Ya fada mata yana murza yatsunta, murmushi ta saki suhail ya sake fado mata for the third time in a roll,
"Ba kowa..." Ta fada mashi, dariya ya sakeyi yana cewa
"Baby hausar ki is so melodious...pls Yanzu ki dinga yi min Hausa har ki koma kinji?.." Da sauri ta marairace fuska tare dacewa
"Yanzu sad zan sake komawa?..." Ta fada kaman zatayi kuka, dariya alhaji yayi yana cewa
"yA mukayi dake?...kince you want to come Don birthday dinki...Sannan kinsan I always fulfill your birthday wishes...so baby zaki koma tunda har Yanzu people that want you dead are not apprehended ""." Ya fada mata, sake marairacewa tayi taNa turo baki tace
"Pls dad..inason zama nan ...I promise bazan fita ba..." Ta fada kaman zatayi kuka,
"Dear kawai ki kwantar da hankalinki...amma zakiyi min alkawarin bazaki fita ba...bazaki saka anyhow clothes ba..bazaki fadawa kowa kin dawo ba Sannan above All zakiyi duk prayers dinki on time..." Da sauri tace
"Dad I promised...bazan fita ba..zanyi duk yanda kace..."
"Ok dear...then zakiyi wata daya nan kafin ki koma..." Fashewa tayi da kuka Tana cewa
"Pls daddy...nidai am not going back..." Ta fada cikin kuka
"Aa...zaki koma...sai kin kusa shekara zaki dawo ...nasan by then na sa an Kama duk masu hannu cikin abinda ake aikatawa,..." Ya fada yana goge mata face dinta,
"Tou Inyi wata uku..." Tafada cikin kuka, Dariya alhaji yayi tare dacewa
"no way...remember birthday kawai nace kizo kiyi...Yanzu kuma na Kara maki 1 month plus 2 weeks to the birthday ai kusan wata biyu kenan...shima sai in kin cika alkawarin sa kika dauka zamu Kai wannan lokacin tare.." Ya shaida mata, kallon shi tayi ta sake fashewa da kukan shagwaba,
"Yauwa baby ki fadamin about Wanda kikace zaki zo dashi...waye shi?.." Shine tambayan da alhaji yayi mata, gani yayi ta saki wani irin murmushi Mai wuyan fassara, bata dai ce komai ba sai murmushi gefen baki kawai take,
"Boyemin zakiyi kenan...remember bamu boyewa Juna komai..." Ya fada yana rike da hannunta, still bata ce komai ba sai murmushi kawai take,
"Hmmm nayi shuru tunda bazaki fadamin ba...Yanzu tell me ya sukayi treating dinki?..2 My maryama...oh na mance Ashe Fatima ce..." Ya fada yana dariya, boye face dinta tayi cikin laps dinta
"Hope alhaji Ismail ya kula dake?.." Ya tambayeta,
"Gaskiya dad he deserves award...Allah yana da kirki sosai..."
"Matar shi fa?.." Ya sake tambayan ta, shuru Maryam tayi for a few seconds Sannan tace
"Amarya is nice amma first wife batasona...ta tsaneni because ya karo aure..." Zama alhaji Mahmoud ya gyara tare dacewa
"Bangane ba..,how is it your fault?..."
"Nima I don't know..." Tafada Tana marairacewa, at the same time Tana tuna irin duka data sha hannunta, tasan inda zata fadawa dad dinta Yanzu Allah kadai yasan irin hukunci da zai yanke and she's sure zai affecting alhaji Ismail and har ga Allah batason abinda zai taba shi domin ita shaida ce he's a good man.
"Hope batayi maki komai ba.." Alhaji Mahmoud ya tambayeta yana kallon how lost in thought she is,
"Nope dad..." Ta fada wearing a smile,
" naji alhaji Ismail yana da son...hope shima he's nice?..." Ya tambayeta, Dan murmushi ta saki before saying
"Ai shine...zai zo..." Ta fada Tana murmushi, idanuwa alhaji Mahmoud ya zaro yana cewa
"Really?... " ya fada sounding so excited, Dan daure face tayi Tana murmushin gefen baki,
"Dear daga zuwa shine har kun zama besties?..." Shine tambayan da alhaji yayi mata, kallon dad dint tayi Tana tunani, tasan in har Ta fada mashi abubuwan da suhail yayi mata he will deal with him unconditionally amma hakan will not favor her, she wants to handle him herself, she want to show him what real word is, ba wannan small word dayake thinking babu irin shi ba,
"kaman dai my daughter ta girma...naga Yanzu you think...now tell me yaushe kikeson yazo?..." Alhaji Ya fada yana dariya, Dan murmushi ta saki tare da sadda Kai kasa, Dan turban dake kanta tadanja baya alhaji ya kalli goshinta yaga har alaman sallah ke da akwai a gaban goshinta, murmushin Jin dadi alhaji Mahmoud yake, he can just explain how happy he is, baisan irin kyautar da zaiyiwa alhaji Ismail ba, ahankali Maryam ta mike Tana cewa
"Dad Bari Inyi wanka...zan fito Yanzu...." Ta fada mashi sannan ta Bari dining din ta hau upstairs zuwa wurinta, tun kafin ta karasa takejin wani irin sweet fragrance, Tana bude Kofar taga komai new, baki ta bude Tana karewa falonta kallo, she can't  just imagine nawa aka kashe wajen gyara part dinta amma tasan ba kananun kudi bane, shiga dakin tayi ta wuce bedroom dinta, nan ba abun kallo né, kan mirror ta kalla taga new set of her cream da su shrub da sauran Kayan gyaran jiki da take amfani dasu kafin ta bar nan, kan gadonta ta duba taga new Apple laptop sannan ya old one dinta ajiye gefe daya, like wise handset sabuwa da tsohon, tsalle Ta daka ta fita daga dakin da gudu ta je wajen dad dinta tayi mashi kiss tare da rungumshi, 
"Sunyi maki kou?.." Shine tambayan da yayi mata yana rungume daita, da sauri tace
"Sosai ma....nagode daddy......" Ta fada sannan ta sake shi ta koma dakinta da gudu. Direct bedroom ta wuce Tana cewa
"Let's wash Nigeria out of my hair and body..." Tana cire Kayan jikinta, gaban mirror ta tsaya daga ita sai pant and bra' kanta take kallo da kuma how much she have changed,  black mark dake jikinta na tsawun bulalan hajiya ta kalla tare da Shafa wajen ahankali, tambayeta a dad dinta yayi mata game da yaushe takeson sunyi ask ya sake fado mata, kallon face dinta tayi Tana cewa
"After I have renew myself..." Ta fada under her breath, shrub ta dauka ta fara murzawa face dinta Tana removing dead skin, daga face dinta sai sauran jikinta kaman yanda ta Saba Don Ada sai ta fi hour Tana murzawa skin dinta shrub daganan ta shafa cleanser shima all over din ita bata yarda da harkar face kadai ba, she prefers all over her body, she normally does this 2 a week
"But am going to do it everyday until my birthday..." Ta shaidawa kanta. Saida ta gama ta shiga bathroom ta wanke kanta ta fito daure da towel.
Alhaji Mahmoud daukar wayanshi yayi tare da dailing number alhaji Ismail.
Chapter 59 · 0% Book details