← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 190

Sashe 16

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 6 min read

"Stupid gal ko iya gyara gadon bata iya ba...sai iya kallon maza...idiot..." Ya fada yana shiga bathroom, Maryam sake Sabon kuka tayi dataji abinda yake cewa, Tana ganin ya shiga bathroom ta fito falo da gudu ta wuce waje har lokacin bata bar kuka ba. Lokacin security sun fito likewise Salman, yana daga Kai ya hangi Maryam ta fito daga part din suhail Tana kuka ta shiga part din hajiya, tunda yake ganin su murja suna fita daga part din suhail bai taba Jin abinda yaji yau ba, ji yayi he's heart is beating so fast,ahankali ya zame ya zauna yana tunanin me yayi mata take kuka. Maryam na shiga ta wuce bedroom dinsu, Sabon kuka ta fara, Tana kiran daddy dinta, murja ce ta shigo dakin ta zauna bakin katifan da take kwance Tana kuka,
"Yar uwa kiyi hakuri...karkiyi kuka Don in alhaji yazo ya ganki cikin damuwa ya tambayeki dalili kika fada mashi ..tou wahalal ki sai ta ninka haka...Don haka ki bar kuka kinji kou...." Ahankali Maryam ta daga mata Kai Kai Tana goge face dinta.
"Ki taso muje muci abinci...." Murja Ta fada Mata , ahankali Maryam ta kalli agogon dake jikin bangon dakin taga it's just 7:20am, ahankali ta girgiza mata,
"Zamu ajiye maki naki...." Murja Ta fada mata sannan ta mike ta bar dakin, komawa Maryam tayi ta kwanta Tana tunanin Suhail da irin kalaman dake fita daga bakinshi, bata taba ganin Wanda ta gani yayi mata kyau kaman shi ba likewise bata taba ganin Wanda ta ga munin halin shi kaman shi ba, yanda yake magana cikin command ta tuna dukda she's angry bata San lokacin da murmushi ya zomata ba, Don gani take inda ita yar wata matsiyaciya ce da bakin ciki ya kashe ta amma thank Allah she's among the rich young ladies kaman yanda dad dinta yake fada mata, Tana tuna at times in tayi ba daidai ba sai yace
"Baby the person who is worth billions of dollars shouldn't behave like such...." Takanyi murmushi in ya fadi hakan and she do reply da
"Dad am I really worth billions of dollars?.." Shima sai yayi dariya yace
"in kinyi hankali zan fada maki ko ke wacece....". Idanuwa ta lumshe Tana tunanin if Tana iya zaman gidan, tasan ko kadan she's not the lazy type Don dad dinta baiyi training dinta tobe lazy ba
"The boss shouldn't be lazy..." Shine abinda yake fada mata duk sanda ta nuna gajiyawanta kan wasu abubuwan,
"Always be strong in any situation you find yourself..." Ta tuna maganar dad dinta kafin tazo Nigeria, tunani tayi ko ya San da halin suhail kafin tazo gidan
"No way...." Ta fadawa kanta Don ta San her dad will do anything to make her happy and not the other way round. Tunawa tayi da alhaji Ismail, ji take kaman Ta fada mashi abinda suhail yayi mata just in a day a gidan sai kuma ta tuna da maganar murja, ko kadan batason abinda zai taba mata lafiya jikinta,
"Let's see your game....then it will be my turn..." Ta fadawa kanta sounding firm and strong. Cikin tunani bacci yayi gaba daita.

Suhail na shiga bathroom yaga bata hada mashi ruwan wanka ba, a fusace ya fito amma sai yaga bayanta har ta fita daga part dinshi, kawai sai ya saki dariya
"Idiot..." Ya furta under his breath sannan ya koma ya hadawa kanshi ruwan wanka ya shiga cikin bathtub tare da sakin ajiyan zuciya.

Bayan alhaji yayi breakfast ya kalli agogon hannunshi, karfe 9 da yan minutes, kallon hajiya yayi ya kalli wayanshi, babu abinda yake bukata Yanzu kaman yaji ya Maryam ta kwana a gidanshi, duk sanda ya tuna alkawarin daya daukawar dad dinta sai gabanshi ya fadi Don wani irin nauyin alamarin yakeji, ji yake Ina ma yana iya fadawa family dinshi ko ita wacece Don anyi treating dinta like a princess that she is amma babu daman haka, yasan ko special attention ya bata Yanzu zai sa hajiya ta zargeshi, Dan ajiyan zuciya ya saki tare dacewa
"My hajiya I think zan saka wannan yarinyan a islamiyya..." Irin kallon da hajiya tayi mashi yasa yayi shuru,
"Hana alhaji...do you mean dadewa zatayi gidan nan da har zaka sata islamiyya?... Gaskiya ni shawarata is a kaita wurin wasu family sai ka dinga tallafa mata har tayi aure...amma ni gaskiya I don't feel comfortable with her around..." Ta fada babu wasa, daure face alhaji yayi ya fara cewa
"Hajiya kin San I have given you too much hand da Yanzu kike son maidani mijin hajiya?"" Baki hajiya ta bude zatayi magana alhaji ya daga mat hannu tare dacewa
"Let me finish..." Ya fada tare da sauke hannunshi sannan yacigaba dacewa
"From now henceforth I don't want you making commands....in kuma Dan kishiya kike wannan abun sai in auro so that hankalinki ya kwanta..." Bai idaba hajiya tq Dora hannu bisa kai
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!!!...alhaji..." Still daga mata hannu yayi tayi saurin yin shuru hawaye na taruwa eyes dinta
"I want you to know ba tsoron ki né yasa ban Kara aure ba da zaki hanani taimakawa family Dina saboda kishi...if I want sai in jero uku bayanki amma bani da wannan raayin..but if you continue like this I might change my mind..." Ya fada yana kallon yanda tears ke rolling daga idanuwanta
"Am sorry...ban karawa..." Ta fada gabanta na dukan uku uku Sannan Tana tunanin why alhaji ke mata harsh words saboda wannan yarinyan, Don har ta gane bayason ta soki maganar ta, hannu yasa ya goge mata face yana cewa
"Stop shedding those expensive tears..." Sai da ya tabbatar ta goge face dinta ta dawo mind dinta sannan ya mike yana cewa
"Bari in aiki Salman ya shiga cikin gari ya nema mata good islamiyya..." Ya fada yana kokarin barin dakin, ahankali itama ta mike Tana cewa
"Nima Bari inje part Dina..."
"Ok..in na gama da Salman am coming to your part..." Ya fada mata Don abinda yake so kenan Don yana son ya shiga part dinta yaga Maryam and how she is. Tare suka fita compound ita tayi part dinta shi kuma ya yiwa Salman alaman ya zo da hannunshi sannan ya koma ciki, da sauri Salman ya taho ya bi bayanshi, bayan sun zauna alhaji yace
"Ka dauki mota kaje wannan islamiyya na modibbo kayi wa shugaban makarantan magana...just tell him ni na aikoka kan maganar wannan yarinyan...zasu Baka uniforms ka kawo...sannan pls ka tabbatar kana kaita kullum kana maidota..."
"Ok sir ..." Salman ya fada mashi sannan ya tashi ya fita, cikin ranshi ya jidadi da Maryam ba gida zata zauna ba balle suhail ya takura mata. Sai da ya fita shima alhaji ya fita ya shiga part din hajiya, sai da ya tabbatar hajiya bata downstairs sannan ya leka kitchen yaga binto Tana aiki Don mostly cikin aiki suke saboda kowa da irin kalan abincin da zaici especially suhail Don har time table yayi masu na abincin shi sannan yakan Chanza ta after some weeks. Gaidashi binto tayi ya amsa sannan ya tambayi inda Maryam take, nan binto ta shaida mashi Tana bacci, agogon hannunshi ya kalla yaga few minutes to ten,
"Ina ta kwana?.." Shine tambayan da alhaji yayi mata,
"Dakin mu..." T amsa mashi kanta kasa, daure fuska yayi sanna yace
"Ima sauran yanuwnki?"
"Suna sama suna gyaran wurin hajiya..."
"Shikenan in kin gama ki shiga dakin dake kusa da naku ki gyara...in kin gama ki maida jikkanta dakin..sannan duk abinda dakin ke bukata ki fadawa Salman ya fadamin..."
"Tou..." Ta amsa mashi cikin ladabi. Wucewa yayi upstairs ya tarda hajiya kwance while su murja na aiki, yana shiga sukayi saurin fita daga dakin. After kaman minti talatin ya koma part dinshi hajiya na biye dashi.
Chapter 16 · 0% Book details