← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 190

Sashe 160

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 7 min read

A maiduguri kam Maryam duk ta tada masu hankali saboda yanda take kuka babu gaira babu dalili, duk tagumi sisters din mom dinta sukayi Suna kallon ikon Allah,
"Wai jamaa ku kiramin mahmouda ya fadamin abinda yayiwa jikata...Don wannan kukan ba haka nan bane..." Inji grandma dinta, wata mata da bazata wuce 40 ba ta mike ta dauko waya tayi dailing number alhaji Mahmoud Tana kallon tsohuwar  dake zaune Tana kallon Maryam, ringing wayar ta dingayi ba'a daga ba, sake Kira akayi amma bai daga ba,
"Baba bai daga ba...." Matar Ta fadawa tsohuwar,
"Oh ni rabi wannan yarinyar zata saka min hawan jini..." Inji tsohuwar, sallama akayi a makeken bedroom din da suke wata mata babba ta shigo, da ka ganta kasan anty din Maryam ce saboda suna Dan yanayi, Tana shigowa ta gaida baba Sannan ta juyo ta kalli Maryam tace
"Wai wa ya tabamin Sarauniyar mata..." Ta tambayesu Tana takawa zuwa kusa da Maryam,
" Wallahi tunda suka zo da babansu take wannan ...Yanzu kusan hour uku kenan da zuwansu amma bata sha ko ruwa ba...sai kuka Kawai take..." Inji wata budurwa, Don a dakin yanmata sunfi su takwas Sannan sai manyan mata uku da baba, matar Kama hannunta tayi Tana cewa
"Nasan da akwai abinda kukayi mata...zo muje ki fadamin gimbiya..." Ta fada mata Tana janta, cikin kuka Maryam ta mike ta bi bayanta, duk binsu sukayi da kallo saya daga cikjnsu tace
"Gaskiya da akwai abinda ke damunta...ji duk yanda ta koma..." Inji saya daga cikin yanmata Mai suna nana,
"Kilan aure ke bataso..." Inji wata, Bata karasa ba baba tace
"Dalla rufemin baki..." Ta dakawa yarinyar tsawa, baki yarinyar ta turo ta mike ta bar masu dakin,

Wani daki matar ta ja Maryam ta zauna ta zaunar daita kan kafarta kamar wata karamar yarinya sanna ta daga hannunta ta gogewa Maryam fuska tace
"Gimbiya fadamin abinda ke damunki...nasan bazaki boyemin komai ba..." Matar ta fada mata, kuka Maryam ta cigaba dayi without saying anything,
"Pls ki fadamin.,,banason ganinki haka...musamman na taso ganinki..." Matar ta fada Tana goge mata face,
" mommy ni banason aure..." Ta fada mata, surprise look matar tayi mata Sannan tace
"Saboda me?..."
"Ni mommy...I don't want to get married..." Ta sake fada mata cikin matsanacin kuka,
" tou bakison shi né?.." Ta tambayeta,
"Eh banason shi...daddy yace dole in Fiddo miji...amma ni Wanda nakeso da ban..." Kallon mamaki hajiya habiba tayi mata tace
" tou me yasa baki Fiddo Wanda kikeso ba?.." Ta sake tambayan ta, cikin kuka Maryam ta bata labarin komai, shuru tayi Tana sauraronta, sai da ta gama ta Dora kanta kan shoulder dinta Tana cewa
"Kiyi hakuri....komai sai in Allah ya yarda zaayi...maiyuwa shi ba alkhairi bane...amatsayinki bai Kama ace kina kuka saboda namiji ba,.,kefa daban kike cikin mata...you're special...namiji ya kamata yayi maki kuka ba ke ba..,Yanzu ki bar kuka...ki barshi da uwarshi...irin wannan iyayen ba'a Jin dadin zama dasu...nafison ki auri Wanda hankalinki kwance..."
"Ai mommy inason shi...shima yana sona..., "
"tou ya zakiyi tunda wacce ta haifeshi tace batason ki...irin wannan kiyayyar har kan jikoki yake komawa...kawai ki kwantar da hankalinki ki...komai zai yi daidai...kinji kou?.." Ahankali Maryam ta daga mata Kai amma bata bar hawaye ba,
"Yauwa my gimbiya...kinsan Yanzu dole a kula dake tunda  kin kusa aure...mu matan maiduguri abun alfahari né ga mazajenmu...Don haka ki kwantar da hankalinki a gyara ki...kinji kou..." Ahankali Maryam ta sakedaga mata Kai dukda she don't really understand inda words dinta suka dosa,
"Yanzu zan shiga bathroom in hada maki ruwan wanka Sannan in dawo in Dora maki abinci in dafa maki da Kaina kici kinji kou..." Ahankali Maryam tace
"Mommy am not hungry..."
"Aa dole kici abinci..kinga yanda kika koma kuwa?... You look terrible...dole ki kwantar da hankalinki ki maida jikinki kafin ayi aurenki "" hajiya ta fada sannan ta mike ta shiga bathroom din dakin da take tahada mata ruwan wanka ta fito ta umarceta ta shiga Sannan ta je inda yan gidan suke Ta fada masu su taimaka mata a hadawa Maryam abinci Mai rai da lafiya.

Shi kam aliyu bai Taba ganin irin wannan rayuwa ba...rabon da yaga Maryam har ya mance, bata piçking calls dinshi, babu wani communication tsakanin su, he's still wondering if the wedding will hold, yaje gidan several times Don ya gode mata for paying for his hajj fees amma sai salima tace Tana bacci ko koma bata nan, he's so tired,
"Nifa wannan abun ba dole bane...it's not by force at all...sun nace min in aureta Yanzu kuma they're leaving me hanging..." Ya fadawa kanshi.

Alhaji Mahmoud kam zaune yake cikn elder brothers Dinshi sai ruwan balai suke zuba mashi,
"Mun samu labarin Maryama Tana nan kasar...Sannan ance ta kusa shekara uku cikin kasar nan...amma dayake mu bamu da daraja shine ko a kawota ta gaishemu..." Inji wani elderly man dake zaune kan wata kujera irin na saurauta,
"Ai yaya ba zancen ta gasishe mu ba...ya kamata a kawota nan cikin dangin mu...da dama basu San junansu ba...koma dai meye dalilin da zaisa ace ba nan aka kawota ba..." Wani ya sake adding, alhaji Mahmoud daddaure face yayi yana tunanin in kawota ku karasa bad intentions dinku kanta kenan,
"Wai wa ya fada maku Tana nan kasar...wannan ai is a lie...jiya muka Iso Kano daita sai ta ce Tana son zuwa wurin mommies dinta...sai nasa a kaita chan....kuma ni abinda yasa na taraku nan shine inason tayi aure..Sannan iyayen yaron zasu zo nan...kunji abinda nakeson fada maku..." Ya fada masu atakaice,  kallon mama ki suka watsa mashi wannan ke kama da babbansu yace
"Ai wannan maganar taka kaman kana bamu umarni...tunda Kai Mai kudi né ai dole kayi mana magana yanda kakeso..."daga Kai alhaji Mahmoud yayi ya kalleshi yace
" me ya kawo maganar kudi Yanzu?., indai maganar bazai yuwu ba a barshi kawai...ni banyi maganar kudi ba..." Ya fada yana kokarin mikewa,
"Kunga irinta kou...he's walking out on us....wai Dan yaro yayi kudi sai ya nemi raina na gaba dashi..." Wani yayi adding, babban cikinsu kallon alhaji Mahmoud dake saka shoes dinshi yayi yace
"Yanzu Mahmoud duk samarin dake gidan nan basu da ajin da za'a hada aurensu da Maryama shine zaka aura mata bare?.." Mutumin ya fada, alhaji Mahmoud bai Kara cewa komai ba ya fita ya barsu nan tsaye, wayarshi wani daga cikin guards dinshi ya bashi ya duba yaga miss calls, bai tsaya bin ta kansu ba ya Kira number hajiya habiba , bayan tayi piçking sun gaisa ya fada mata ta tafi da Maryam gidanta...Sannan kar a barta ta fita...ya Kara cemata ko wanshi yazo ganinta kar a basu izinin ganinta...
"Kuma a fadawa su baba kar su fadawa kowa inda take...Yanzu zasu magana da iyayen yaron...za'a saka rana ayi komai da wuri su bar kasar nan...duk abinda kike bukata kiyi min magana..." Ya fada mata, tou kawai Ta amsa mashi sannan ya kaste wayar shi, ya shiga cikin jet ya umarci pilot dinshi ya maidashi Kano..

Hajiya na fita daga part din alhaji ta nufi part dinta da sauri,  kitchen ta shiga ta rasa abinda zata dafawa suhail, tsayawa tayi kaman Mai tunani Sannan har lokacin bata bar hawaye ba, da sauri ta sake fita ta Kama hanyar part din salima, cikin kuka ta shiga da sallama, salima dake breastfeeding baby Maryam ta amsa tare da mikewa saboda yanda hajiya ta shigo, baki hajiya ta bude zatayi magana kuka yaci karfinta,
"Anty lafiya .." Salima ta tambayeta, kasa magana tayi har saida kukan ya Dan tsaya Sannan ta kalli salima tace
"Dan Allah...ki Dan dafawa suhail abinci kadan...naga yana cin. Abincin ki..." Ta fada cikin voice da bai fita,  da sauri salima tace
"Suhail ya dawo né?..." Ta tambayeta, ahankali ta daga mata Kai,
"Tou shikenan...me zan dafa mashi, ..." Ta tambayeta,
"Anything..." Hajiya ta amsa mata Sannan. Ta mike ta bar dakin, da sauri Salima ta mikewa Inna baby ta shiga kitchen,
"Oh ni...jiya jiya Maryam ta bar gidan nan shi kuma yau ya dawo..." Ta fada Tana kunna  gas cikin ranta Tana tunanin ta fadawa Maryam ko ta barta, tasan in har ta fadawa Maryam suhail ya dawo confirm zuwa zatayi, hakan zaisa ta ki bin umarnin iyayen ta,
"Kuma zan zama Mai  laifi ...kawai Bari Inyi shuru da bakina..." Ta fadawa kanta.
Chapter 160 · 0% Book details