← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 190

Sashe 83

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 5 min read

Wace gari a Nigeria alhaji Ismail né zaune yana waya da alhaji Mahmoud, abinda kunnuwanshi ke jiyo mashi yasa ya kasa bude baki balle yayi magana sai hummmming kawai yake yana sauraron abinda alhaji Mahmoud ke fada mashi,
"So a amshi passport dinsu a kaiwa alhaji yasir...nayi magana dashi..he will take care of the rest, and nan da hour daya kudin zasu iso sai ka bashi...but pls don't say it's because of my daughter..." Alhaji Mahmoud ya karasa maganar, dariya alhaji Ismail yayi ya fara jerawa alhaji Mahmoud kirari Wanda yasa alhaji Mahmoud dariya sosai,
"Ai wannan naka ne...kayi kokari sosai din kullum maryama cikin fadin alkairin take, kuma another amazing thing shine yanda ka bawa danka tarbiya...ga respect...he never looked me in the eye, ajiyan zuciya alhaji Ismail ya saki tare dacewa
"Maryam Allah yayi maki albarka da kika rufa min asiri..." Y fada cikin ranshi,
"Naji yace he just finished his masters...kilan nan gaba Dani zaiyi aiki a nan..." Idanuwa alhaji Ismail ya sake budewa Sannan yace
"wow,.,thank you sir..." Inji alhaji Ismail, Dariya alhaji Mahmoud ya saki Sannan yace
"Stop greeting me..ai yiwa kaine..he's a son already..." Ya fada mashi, ba karamin dadi alhaji Ismail yaji ba wai suhail will be useful Sannan yaji dadin yanda Maryam bata tona asiri halin hajiya da suhail ba, bayan sun gama waya alhaji Ismail ya fara cewa
"Who ever said doing good is bad is definitely wrong....alkhairi dankone...you will surely pick it inda bakayi tsamani ba...haka shima sharri..." Ya fadawa kanshi, shuru yayi yana tunanin makudan kudin da za'a bawa Salman,
"That will make him rich for  a life time..." Ya fada wearing a smile,
"Am going to miss you my loyal boy..." Alhaji Ismail ya fada yana relaxing, kofa aka bude Salman ya shigo kallon shi alhaji yayi wearing murmushi, file Salman ya ajiye mashi yana cewa
"Sir from alhaji mandawari...wani ya kawo..." Ya fada not looking at alhajis face
"Ok...the young millionaire ..." Alhaji ya fada yana dariya, ahankali Salman ya daga Kai ya kalli alhaji bai ce komai ba ya Dan saki murmushi ya juya zai fita,
"Salman..." Alhaji ya kirashi, ahankali ya juyo, kujera alhaji ya nuna mashi alaman ya zauna, takowa yayi ya dawo ya zauna yana kallon alhaji face dinshi dauke da girmamawa, bayan ya zauna alhaji Ismail yace
"Son Yanzu assuming an Baka million hamsin me zakayi dashi?.." Ya tambayeshi Don yasan it's good ya fara bashi clue kar ya samu nervous breakdown in kudin sun zo Don because yana Jin stories kan mutane da za'a basu makudan kudi kuma ya zama ajalinsu, Dan murmushi Salman ya saki Sannan yace
"Sir...ni kam wa zai bani 1 million balle 50 millions?..'" Murmushi alhaji ya saki Sannan yace
"Kawai just imagine an Baka 50 millions me zakayi dasu?.." Ya sake fada mashi, Dan ajiyan zuciya ya saki Sannan yace
"Well Bari inje dream land...na farko iyayena suna hayan gidan a bridged...zan saya masu sabon gida Don kullum bani da gurin daya wuce in ga mom Dina cikin Jin dadi...Sannan I will start a business for my mother and my dad...Ina da kanne maza uku zanyi establishing sauran kudin a business Wanda dukkan mu zamuyi tare..." Ya fada kanshi kasa, Dan murmushi alhaji yayi Sannan yace
"In kudin sun Kai 100 millions fa?.." Alhaji ya sake tambayeshi yana relaxing, ahankali ya saki dariya ya sake cewa
"Ai makeken gidan zan siyawa iyayena...mansion...Dan zanyi international business..." Alhaji kallon shi kawai yake,
"You will be a good businessman kenan..." Ya fada yana dariya, shima Salman dariya yayi bai ce komai ba,
"Misali in Allah yayi maka arziki who will you turn to for advice...nasan bazaka rasa mentor ba ai..." Da sauri salma yace
"Kai mana...Kai me uban gidana nor matter what...Kai né zaka bani shawara saboda kaine ka bani dama lokacin da all others turn away...even my own uncles..." Gira daya alhaji ya daga tare dacewa
"Daman kana da uncle Mai kudi né?.."
"Eh mana...yana da school a garin mu Niger...Dana gama school babban mu yace inje ko zai bani aiki amma Ina zuwa sai cewa yayi babu vacancy wai in koma sai an samu vacancy zai kirani and har yau bai kirani ba alaman baison Inyi aiki a organization dinahi' ..." Ya karasa maganar cikin sanyinmurya
"That's very bad of him...in Baka taimaki naka ba wa zaka taimaka?... If you don't hey ours grow then babu Wanda zaka taimakawa...." Alhaji ya fada yana kallon Salman,
"Allah yasa manyan mutane su gane taimakon na kasa dasu ko da ba family dinsu ba....you don't know where help might come from someday..." Alhaji yayi adding
"Only the people with good heart knows that...wasu tarawa kawai suke not even remembering death...wasu da billions a account dinsu while wani bai da ko dubu daya..." Inji Salman,
"Allah yasa arzikin mu ya zama sanadin shigar mu aljanna..."
"Amen sir...am hoping so for you because you're a good man..." Inji Salman dariya alhaji yayi Sannan ya sake cewa
"Talking about business wane irin type of business zakayi if you have kaman 170 millions..." Alhaji ya tambayeshi, Salman murmushi yayi yana mamakin why Alhaji ke Kira mashi such huge amount of money while ko dubu hamsin na kanshi bai dashi,
"I love electronic..kaman duk appliances da zaayi amfani da shi from kitchen to office..." Salman ya fada within courage, dariya alhaji yayi sanna yace
"Yes it's a good business..." Hira sukayi kaman na minti talatin Sannan Salman ya koma bakin aikinshi.
Kudin na isowa Alhaji ya Kira bank dinshi ya shaida mashi account da za'a tura kudin.
Wajen Karfe biyar na yamma har lokacin suna office kasancewan Alhaji bai Bari suka tashi da wuri ba because yasan soon life din Salman will change. Salman na cikin typing wasu papers da alhaji yasa yayi Wanda ko kadan basu da amfani amma he want him to be busy, messages né suke shiga wayar shi amma bai duba ba har saida ya gama abunda yake sanna ya duba, nan take gabanshi ya fara faduwa,millions and millions ya gani cikin account dinahi, da gudu ya shiga office din Alhaji ya nuna mashi Don ko kadan bai iya magana, dariya alhaji ya saki Sannan yace
"It's all yours..." Idanuwa Salman ya zaro kawai sai ya maidasu ya rufe yayi baya, ji kake tim ya fadi, da sauri alhaji ya mike yaga har ya suma.   
Chapter 83 · 0% Book details