← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 190

Sashe 148

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 5 min read

saki Sannan tace "Let me Change...." Ta fada sannan ta juya, ciki ta shiga ta Dan watsa ruwa ta fito sanna ta shirya cikin pink lace Riga da skirt, vail fari tayi rolling Sannan tafito, yana ganinta ya mike tsaye "Kin yi kyau..." Ya fada mata, bata amsa ba ta karaso inda yake tsaye, hannunta yazo kamawa tayi saurin janyewa tare dacewa "Pls no touching...pls,,," Ta fada mashi, "Duk cikin salon rabuwa dani din né kou?... " ya tambayeta, shuru tayi bata ce komai ba, "Muje in dauko car keys..." Ya fada sannan ya fita, juyawa tay ta shiga dakin salima ta fada mata zasu fita tayi masu adawo lafiya sanna ta fito compound, Tana fita hajiya itama ta fito humaira dake sanye da Arabian gown na biye daita na rike da handbag dinta, shima suhail ya fito rike da car keys, hajiya na ganin Maryam ta kalli part din suhail taga ya fito da makkuli, wani irin kallo ta watsawa Maryam tace "Banza ballagaza...shegiya dangin karuwai...uwarki tayi asarar haihuwarki..." Ta fada mata Sannan ta kalli suhail dake tahowa tace "Kai kuma Dan ubanka bani makullin motata...bazai taba yuwu ka saka wannan karamar yar iskar cikin motar dana siya maka da kudina ba.." Ta fada Tana stretching hannunta gabanshi, Maryam sadda Kai kasa tayi Tana hawaye, suhail kallon hajiya yayi not knowing what to say Sannan bai mika mata key din ba, "Dan uwarka give me my car keys..." Ta daka mashi tsawa, ahankali ya taka ya ajiye keys din cikin Palm dinta, da gudu Maryam ta koma ciki Tana kuka, tsoki hajiya taja ta bi bayanta da harara Tana zaginta, "Low class kilaki .." Hajya ta fada Tana bin bayan Maryam da harara, baki suhail ya rike yana kallon hajiya dake wanke Maryam da zagi, he has never been so mad at her amma what can he do, he's a son and she's the mother, sai da Maryam ta shige Sannan hajiya ta juya ta suhail tace "Ni da kaine gidan nan...Wallahi sai nayi maganin Dan iska...sai na nuna maka uwa uwace,..," Ta fada bag dinta dake hannu humaira Ta amsa ta wulla keys din ciki, "Mommy..." Suhail ya kirata cikin sanyinmurya, wani irin kallon banza ta watsa mashi without saying a word, "I have learnt my own lessons....sauran naki..." Ya fada mata Sannan ya juya, "Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Hajya ta fara maimaitawa bakinta bude, "Wato suhail saboda wancan low class yarinyar kake gayamin magana...." Ta fada cikin tsiwa, "Wato nima I will learn my own lesson kenan... To Wallahi ubanka zanci...tunda abin har in yazo ba threat sai kaci ubanka...shege sakare..." Hajiya ta fada afusace Sannan ta Kama inda motoci suke, suhail na shiga ya dauko traveling bag dinshi ya fara diban kaya yana watsawa ciki, sai da ya gama diban enough yanda yake bukata Sannan yayi zipping ya dauki bag din ya fita waje, part din salima ya shiga rike da bag, salima ya tarda falo tayi tagumi Tana ganin suhail da bag tace "Ina zuwa kuma?.." Ta tambayeshi, "Anty zan koma Legos....daga Chan zan wuce..." Ya amsa mata "Har ka gama hutun?." Shuru yayi bai amsa mata "Anty Ina Fatima?.." Ya tambayeta, "Ta shiga dakinta...." Ajiye bag dinshi yayi ya taka zuwa bakin Kofar dakinta, kukan ta kawai yake ji, Kai ya hada da Kofar yana sauke ajiyan zuciya "Baby am sorry...am so sorry...I don't know why this is happening to us but let's take it with faith....zan tafi...I won't let you take another insult because of me..." Ya fada ahankali Sannan ya juya, wurin salima yaje yace "Anty Dan Allah zan samu cash hannunki sai Inyi maki transfer?... I can't waste time going to the bank..." Ya fada mata, "Kaman nawa?....." Ta tambayeshi cikin sanyinmurya Don wani irin tausayinshi take ji, "Ko dubu hamsin....mota zan hau zuwa Lagos saboda banyi booking flight ba..." Ya fada voice dinshi na cracking, "Amma Yanzu mota zaka hau?...me zai hana..." Bata karasa ba yace "Anty yau nakeson tafiya...banason Kara koda hour daya gidan nan..." Ya amsa mata, ahankali ta mike ta shiga bedroom dinta, sai juyawa yake ko Maryam zata fito daga dakinta amma bata fito ba, bayan kaman minti biyar Salima ta fito da wasu kudi "Gasu dubu talatin né da uku...su kadai gareni...." Ta fada mashi, amsa yayi ya turasu aljihunshi ya Fiddo wayarshi yace mata "Bani account numbers din..." Ya fada mata yana latsa wayar, "Bani da account...ka turawa alhaji...sai ya bani..." Ta fada mashi, "Tou shikenan..." Ya fada yana maida wayar aljihunshi Sannan ya dauki bag dinshi. Fita yayi ya nufi bakin titi sai da ya sha tafiya Sannan ya samu adaidaita, " Dan Allah tashar da ake hawan motar Lagos zaka kaini..." Suhail ya fada mashi "Wajen Ina kenan?.." Mutumin ya tambayeshi "Gaskiya Nima ban sani ba...Kai bakasan tashan zuwa Lagos ba?.." Suhail ya watsa mashi tambaya, "Gaskiya ban gane wajen ba..." Mutumin ya fada, suhail bai Kara kallon inda yake ba ya cigaba da tafiya Sannan ya samu wani, yana fada mashi inda zashi mutumin yace ya shigo. Suna zuwa park ya biya ya sauka ya fada masu inda zashi, nan aka ce tafiya wasu sun tafi sai masu yafiyar dare "Ok zan bi wannan..." Ya amsawa Mai yi mashi bayani, kudi ya biya aka saka sunanshi cikin list din matafiya. Gefe da ya koma yayi tagumi, duk Wanda ya ganshi yasan he doesn't belong here, he's so different, waya ya dauka ya Kira aliyu ya fada mashi pls zai hadashi da humaira in case in ta tafi komawa ya nema mata visa zuwa Lagos then to Dubai.
Chapter 148 · 0% Book details