← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 190

Sashe 17

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai karfe goma da rabi Suhail ya shiga part din mom dinshi, upstairs ya hau ya gan mom dinshi bata nan yasan Tana part din dad dinshi, downstairs ya dawo ya wuce kan dining ya hakimce yana jiran breakfast, suna ganin shi kan dining sukayi saurin fara jera mashi breakfast dinshi kan dining sai da suka gama murja tazo serving dinshi ya daga mata hannu alaman ta dakata, tsayawa tayi Tana jiran next command dinshi Don tasan ba da kaishi zai zuba abincin ba.
"-–-11222222222222Kirawo Dayan...." Ya fada mata atakaice, murja ta gane abinda yake nufi, da sauri ta bar wajen while binto da asabe suka kalli juna.
Daki murja ta shiga har lokacin Maryam Tana bacci saboda kukan data sha, ahankali murja ta Dan bugi shoulder dinta, cikin kasala Maryam ta bude idanuwanta,
"Yace kije...." Murja Ta fada mata, da sauri Maryam ta wace idanuwa Tana cewa
"Waye..again..." Ta fada gabanta na faduwa,
"Suhail..." Ta amsa mata,
"Na...shiga....uku..." Ta furta kaman zatayi kuka, nan take ta hada Kai da gwaiwa gabanta na Kara dukan uku2,
"Ki taso..baya son jira, Ta fada mata, jiki ba kwari ta daga Kanta da idanuwan ta da suka kada sukayi ja, kaman Mai maye ta biyo murja har lokacin Tana sanye da Kayan bacci da hijab, duk ta susuce suna fita falo ta hangi suhail dake zaune kan dining fuskan daure kaman bai taba dariya ba, daga Kai yayi suka hada Ido ya Kara murtuke fuska haka nan yanajin wani Abu game daita dake sashi ji kaman ya dinga dukanta, so he thinks. Yanda ta Saba tafiyan ta ta taka ta karaso inda yake zaune, kusa dashi tazo ta tsaya, daga inda yake zaune yana ganin yanda jikinta ke rawa,
"Save me..." Yayi commanding dinta, jikinta na rawa ta isa kan dining din ta bude abincin, hannunta sai rawa kawai yake, daga Kai yayi ya kalli sauran yan aikin sukayi saurin watsewa, jikinta na rawa ta fara zuba Irish potatoes, rabi cikin plate rabi kan dining, suhail harde hannuwanshi kan kirjinshi yayi yana kallon ikon Allah, Kwai ta zuba mashi sama Tana kyarma, hannu tasa zata dauki flask da ruwan tea ke ciki kamshi ya bugi hancin shi, dukda ta dade bata yi amfani da perfumes dinta ba she doesn't smell bad saboda ya Kama mata jiki already, ruwan tea ta zuba cikin cup Dan kadan kaman yanda ta Saba Shan nata, madara ta bude ta fara zubawa cikin ruwan, sai data cika Dan karamin ruwan da madara ya koma Kama custard sannan ta tura gabanshi, suhail zama kawai yayi yana kallon abun mamaki tea kaman koko, saida ta gama ta mike tsaye, ahankali yayi mata hannu alaman tazo, Dan Matso kusa dashi tayi sannan ya kalli tea da dankali dake kan dining yace
"Daman haka matsiyata suke...nasu dukiya na mutum banza,... Dan ubanki kin taba ganin tea haka?..." Ya daka mata tsawa, jikinta na rawa ta girgiza mashi Kai dukda ita paste takeyi da tea dinta ta dinga lashewa ahankali kaman Tana Shan ice cream, lumshe idanuwa tayi Tana sauraron abinda yake cewa
"When am talk about to you look at me...." Ya daka mata tsawa, da sauri ta bude red eyes dinta
"Nace haka ake tea?..." Ya sake tambayan ta cikin fada, da sauri ta sake girgiza mashi Kai, tsaya kallon tender hands dinta data rike cikin juna yayi sannan ya maida idanuwashi kan face dinta yana cewa
"Kin San ba haka ake tea ba shine kika hadamin haka Dan ubanki?... Wato tunda bana ubanki ko uwarki bane even if it's wasted babu komai kou?.. Tou tunda na lira ke yar raini hankali ce special treatment zan baki gidan nan...and now kin kwace wannan Irish din kin cinye..." Ya fada yana nuna mata na kan dining, hannunta na rawa ta saka ta fara daukan daya tana kaiwa bakinta, rike mata hannu yayi, cikin second daya ya saki hannun saboda abinda yaji, ha shocking sannan hannunta kaman cotton wool dukda bai taba hannun mata yasan ba haka hannunsu suke ba,
"Park all and eat..." Ya umarce ta, da sauri ta kwace duka ta Kai bakinta, Dan karamin bakinta ta bude ta fara turawa cikin bakinta, shuru suhail yayi yana kallon ta, Abu guda saya da bai gane ba shine at this moment he don't mean what he's doing to her amma kuma he enjoys watching her,
"Get out..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta bar wajen, direct bathroom ta wuce ta saki abincin cikin sink Tana fashewa da kuka, she can't just believe yau tayi kuka sau biyu because of same person. Bakinta ta wanke ta dawo dakin ta zauna bakin katifan, wayanta ta dauka tayi dailing number dad dinta, ringing ya dingayi amma baiyi piçking ba, bayan kaman minti biyu sai ya message cewa yana meeting that he will get back to her, tasan ba lallai bane ya kirata a wannan ranar Don mostly excuse da yake bata kenan.

Salman ya dawo da Kaya cikin Leda ya bawa alhaji, lokacin still suna tare da hajiya, nan yake fada mata Kayan islamiyya Fatima ne, batace komai ba taja bakinta ta tsuke.

Har karfe biyu Maryam bataci komai ba, wanka tayi ta Sam gown ta koma ta kwanta. Alhaji bai samu kadaici ba sai da zashi sallan zuhr, sai lokacin ya dauki wayanshi ya Kira Maryam yana tafiya, Tana piçking ya gane something is wrong
"Daughter meke damunki?.." Shine tambayan da yayi mata,
"Babu...komai..." Ta amsa mashi muryan ta narawa sannan hawaye na forming idanuwanta,
"No..ya zakice babu abinda ke damunki while you sound dull...pls daughter ki fada min..." Ya daka yana tafiya ahankali,
"No...just missing my daddy...." Tana kaiwa nan sai ta fashe da kuka
"And baba rabi...." Tayi adding,
"Am so sorry daughter...zansa a maido baba rabi nan ba da dadewa ba...have you eaten?.." Ya tambayeta, sai lokacin ta tuna da ko ruwa bata sha ba yau, shuru tayi babu response
"Daughter kinci abinci?.." Ya sake tambayanta,
"No...Yanzu...zan...ci..." Ta fada mashi,
"Daughter pls kar ki zauna da yunwa...and duk abinda kikeson ci just contact me directly kinji kou?..."
"Yes sir..."
"Nasa an gyara maki dakin kusa da Wanda kika kwana...ki koma chan..sannan duk abinda kikeso ki sa ayi maki...don't stress yourself...hope am understood?..."
"Yes sir..."
"Yes ma'am..." Shima ya fada cikin zolaya, San murmushi ta saki sannan ya kashe wayan, relaxing Maryam tayi Tana tuna irin kirkin alhaji Ismail,
"He's so caring..." Ta dada under her breath, ahankali ta mike ta fito falo tare da shiga kitchen,
"Baki ci abinci ba har na rana y kusa dahuwa..." Binto ta fada mata, murmushi kawai ta sakar mata sannan ta bude fridge, yourght ta gani ta Fiddo,
"Tab ki maida shi..kika sha tou kin shawowa kanki..." Bata nemi Jin ko na waye ba ta maida ta ajiye, cabbage da asabe ke yankawa ta deba ta wanke, ta fara ci haka nan, kallon ta kawai suka tsaya yi
"Bazaki ci abincin da aka ajiye maki ba?.." Binto ta tambayeta, ahankali ta girgiza mata ki Tana Kai cabbage bakinta.

Karfe hudu baba rabi ta dawo gidan, suhail dake zaune compound harara ya bita dashi batare saya amsa gaisuwanta ba. Maryam Tana ganinta taji wani irin dadi Don har hugging dinta tayi saboda farin ciki. Nikam nace baba rabi bata iya Hana Suhail yin what suhail do best.

One love💙❤💙💛💚
8💙❤💜💛💚
Wulakanci dodone...
💚💜💛💙❤

® zuwairat (ummumaryam)

0⃣8⃣

Dearies dont forget to be voting ohhh, wai NA CUCE ta have over 220k views amma ko 20k vote ban samu ba😥😥😢😢, ni inyi wahala amma you can't take just a second kuyi voting 😭😭😭. Nidai Yanzu iya voting dinku iya samun new post 😾.

Suhail fita yayi daga gida Don daman yana zuwa football field da su sadeeq ranar Sunday, a chan aliyu ke ta bayanshi Ina bakuwar gidansu, baki ya tabe sannan yace
"Inside my trousers..." Ya amsa mashi yana Shan bottle water, tsoki aliyu yaja tare da juyawa suhail baya, gabanshi suhail ya zaga sannan ya daga gaban gajeran wandon daya saka yace
"Kalli she's in side..." Banza aliyu yayi dashi.
"Ni dai pls kar kayi maltreating wannan yarinyan, she looks nice...." Yusuf ya fada mashi, suhail dake sanye da jessy na bacelona ya rufe marfin ruwan ya ajiye cikin bag daya taho dashi sannan ya tsaya kaman Mai tunanin wani abu, Kawai sai ya saki dariya, kallon shi sukayi ya fara cewa
"Allah wannan yarinyan muguwar yar rainin wayauce...wai ta hada min tea sai ta tuka min madara kaman tuwo...can you believe that?.." Ya fada fuskan shi dauke da murmushin da in ba friends din ba babu Mai ganinta, dariya sukayi Banda aliyu
"Maybe haka ta Saba hada tea..." Inji sadeeq, baki suhail ya tabe tare dacewa
"Babu wani...kawai rainin hankali né...wallahi ni dai haka nan I feel like in kamata in dinga duka...Allah what I feel for her banajin shi kan sauran yan aikin...." Ya fada Fuskanshi babu walwala,
"Wai yar aiki ce?.." Aliyu ya tambayeshi
"Yes...to me..."ya amsa mashi atakaice,
"Amma seriously ka bar zaluntar wannan yarinyan...there's something about her...she look unique...Allah nidai yarinyan nan tayi min...if I have chance Ina iya aurenta..." Inji Yusuf, suhail kura mashi Ido yayi sannan ya kauda Kai without saying a word,Dan murmushi ya Kara saki yana cewa
"Allah dukda she's annoying ta iya ban dariya...yau da safe da gudu ta bar part Dina...." Ya fada wearing a killer smile,
"Me tayi a part Dinka?... Kar dai ka zama Dan iska..." Yusuf ya fada sounding surprised,
"Allah forbid...ko ina Dan iska ai duk wannan gidan babu mate Dina...dukkan su are under me..."
"Enough about her..." Duk maganar da suhail keyi yana batawa aliyu rai amma yayi shuru kaman bai damu ba, kawai he has his plans
"Ni daga nan gidanku zani..." Inji aliyu,
"You're welcome..." Suhail ya fada mashi.
Chapter 17 · 0% Book details