← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 190

Sashe 159

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 11 min read

A bakin gate din gidan su suhail akayi knocking, da sauri maigadi ya je bakin gate yana cewa
"Waye?" Ba'a amsa ba aka sake knocking, Dan lekawa maigadi yayi ta open space yaga wani tsaye, ahankali ya bude kofa tare dacewa
"Wa kake nema?.." Ahankali suhail ya girgiza Kai ya shiga ciki rike da bag dake hannunshi, bayanshi maigadi yabi da kallo yayi saurin cewa
"Sannu da zuwa ranka shidade...kayi hakuri ban gane ka ba,.." Ya fada yana amsar bag dake hannunshi, ahankali suhail ya daga mashi hannu tare da sakar mashi bag din, bayan suhail dake tafiya Kama iska zai daukeshi yabi yana tunanin me ya samu wannan bawan Allah ya koma haka Don ko kadan bai gane suhail né ba sai da ya kalli bayanshi ya gane shi da yanayin tafiyarshi, part din hajiya ya Nufa yana tafiya da kyar.

Hajiya kam yanda ta ta dare haka taga rana, fadin tashin hankalin da take ciki is a waste of time Don it's written all over her, duk idanuwanta sun kumbura saboda kuka, kawai ji take kaman mutuwa ya zo ya dauketa Kota samu saukin kunyar da takeji, abun haushi ko inda take alhaji bai shiga ba tun jiyar balle yasan halin da take ciki, Tana zaune kan carpet a bedroom dinta aka bude kofa, da sauri ta mike tsaye ganin an unknown man tsaye,

Pls kusan irin Kayan online da zaku saya, some people are 419ers' wasu zasuyi maka tallan Kaya sai sun turo maka kaga ba irin shi bane ko su tura maka rubbish, not all oo buts wasu suna zalunci, adai ji tsoron Allah.

Remember to cast your vote oooo be wise and stay vigilant, Allah bless our obgodo yibo Nigeria, ameen
[2/16, 8:57 PM] 0mmr Farouk: 51💜💚💙💛❤
Wulakanci dodone...
💚❤💛💜💙

® zuwairat (ummumaryam)

5⃣1⃣

Don't read if you didn't pay...

Ahankali hajiya ta dinga takawa Tana kallon idanuwan suhail which is the only thing that make her recognize him, shima shigowa yayi yana nishi Kama Wanda yayi Gudrun tsere,
"Eyeballs..." Hajiya ta kirashi cikin tashin hankali, Tana tallabo face dinshi, ahankali ya saki jikinshi a kan shoulder dinta, cikin voice da bai fita sosai tace
"Eyeballs what happened to you..." Ta tambayeshi Tana daga face dinshi daga kan shoulder dinta Tana kallon face dinshi Don ta tabbatar it's her son Don the change is beyond recognition,
"Na shiga uku...eyeballs talk to me..," Ta fada da karfi, suhail sai nishi yake saboda upstairs daya hau, yanda yake nishi yasa hankalin hajiya ya Kara tashi, ahankali ya zauna bakin gadon ta har sai da ya gama sauke ajiyan zuciya while hajiya na tsaye ta Dora hannu bisa Kai Tana kallon shi hawaye na fita idonta, ahankali ya daga Kai yace
"Hi mommy..." Ya fada mata muryar shi na tsinkewa kaman Mai asthma, da sauri hajiya dake kuka sosai tace
"Eyeballs what happened to you?.." Ta tambayeshi Tana dukawa gabanshi,ahankali ya tallabo face dinta yana murmushi zai bude baki yayi magana sai ya fara tari which take about two minutes to stop, da sauri hajya ta dauko mashi ruwa daga cikn fridge ta zuba a cup ta Kai bakinsh, ahankali ya bude baki ya kurba sau daya Sannan ya kauda Kai, ajiye cup hajiya tayi still crying, kallon suhail take batako kiftawa' ajiyan zuciya suhail yayi Sannan yace
"Mommy...rashin lafiya nayi..." Ya fada mata calmly saboda bai iya magana da karfi, volume hajiya ta karawa kukarta Tana cewa
"Dana am sorry..." Da sauri suhail ya Kama mata hannu yana cewa
"No...mommy.." Ya fada mata yana girgiza Kai, kanshi ta rike Tana cewa
"Dana na zama uwa Mai bakin ciki da ci gaban danta....eyeballs why Baka fadamin Fatima Maryam ce ba?.." Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, ahankali suhail ya girgiza Kai yana cewa
"Amana mommy...amana..." Ya fada voice Dinshi na rawa, kuka hajiya ta dingayi Tana rungume da suhail, shidai suhail baiyi kuka ba Don yasan he has shed enough tears to last him a life time,
"Dana na shiga uku..." Ta fada Jin yanda jikinshi ke rawa,
"Wane irin ciwo ya maida min Kai haka?." Ta tambayeshi, ahankali suhail ya Dora hannu kan chest dinshi yana cewa
"Heart.." Ya fada, hannu hajya ta Dora a Kai Tana cewa
"Kaicona...wayyo Allah na shiga uku...heart fa kace suhail...you never tell me..." Ta fada cikin matsanacin kuka, cikin shessheka suhail yace
"you..don't...answer..my calls..." Ya fada kaman yana stammering, kafa hajiya ta dinga girgizawa Tana hawaye,
"Wayyo zuciya zai kaini ya baroni...I wanted you to learn your lessons....I wanted you to know am really angry with you.." Tafada Tana kallon glowing eyeballs dinta that is now fading away,
"You took it too far mommy.." Ya fada mata,
"Am so sorry...am sorry eyeballs...sharrin shaidan né...I have never been heartless when it comes to you saboda I never love any child the way I loved you...sai ya kasance raina yana baci in nace kayi Abu ko ka bar Abu kayi min gardama...it breaks my heart...but I was selfish for denying you your love..." Ahankali suhail ya Dora weak hand dinshi kan bakinta, yana girgiza Kai yana cewa
"It's destiny mommy ...not your fault...haka Allah yaso....I will never hold anything against you...you're my mother...stop apologizing..." Ya fada yana counting words, hajiya sake rungume shi tayi Tana hawaye,
"Babyna am sorry...dole in Baka hakuri...dole in nemi yafiyarka...I have ruin my own happiness with my own hands and attitude..." Ta fada cikin matsanacin kuka, shima suhail riketa yayi yana cewa
"Mommy..am sorry....I might not have much time..." Da sauri hajiya ta rufe mashi baki,
"Duk inda Maryam take zanje in bata hakuri...zan je Inyi crawling gabanta har sai ta yafemin ta dawo gareka..." Tafada cikin kuka har da majina, Kai suhail ya girgiza yana cewa
"I beg aliyu to accept her...I won't take her from him...let me patiently wait for my time...nasan Allah zai bani mafiyinta achan..." Hajiya Kara danne mashi baki tayi Tana cewa
"Don't ever say those words again..." Ta fada cikn zafin Nama Sannan ta sakeshi ta bar dakin da gudu, kanta babu dankwali ta fita zuwa compound sai kuka take, yau babu wannan effizy da jijji da Kai, she was walking like a mad woman ta shiga part din alhaji, ko sallama babu ta shiga Tana cewa
"Alhaji ka taimaka min ka kirawo Doctor...my son is dying...my suhail..." Alhaji najin suhail yayi saurin mikewa, dukda yanda yake Jin haushin hajiya saida yanayin ta ya bashi tausayi because she looks so pale and restless
"Ina suhail din yake?.." Alhaji ya tambayeta sounding so anxious, da sauri tace
"Yanzu yazo..yana part Dina..." Ta fada mashi crying very loud, alhaji bai tsaya sauraron abinda zata sake cewa ba ya fita da gudu yaje part din hajya, da gudu ya hau upstairs, yana bude dakin hajiya yaga suhail, in ba Don hajiya ta fada mashi suhail né ba da bazai taba yarda suhail né ba, ahankali alhaji ya koma baya ya fashe da kuka, kunsan ance there's nothing the eyes will see that will shed blood, amma somethings are beyond our expectations, yanda alhaji ya jingina da bango yana kuka yasa shima suhail fara hawaye, alhaji can't believe wannan suhail né, yarasa me ya maida mashi yaro haka, he can't believe mutum Mai rai zai koma kaman yanda danshi ya koma, hajiya dake kuka ta shigo taga Alhaji tsaye yana hawaye, afusace ya juyo ya kalleta yace
"Wallahi if anything happens to my son..." Bai karasa ba suhail dake kuka yace
"No daddy....komai mukaddari né....komai sai da yardar Allah...ba laifinta bane..." Afusace alhaji da face dinshi e cike da hawaye yace
"Kayi min shuru....da akwai kaddara Sannan da akwai sila...Wallahi if anything happens to you itace sila...and I won't take it likely with her...." Ya fada yana kallon suhail, hajiya dai Banda kuka babu abinda take Don ko voice dinta bai fita da kyau,
"Why Baka fada Baka da lafiya ba?" Alhaji ya tambayeshi, cikin hawaye suhail yace
"Dad am tired of complaining...I felt the death will come easy..." Da sauri alhaji yace
"Nothing will happen to you..." Alhaji yayi assuring dinshi Sannan ya Fiddo waya daga cikin aljihunshi, ahankali suhail ya kalli dad dake latsa waya yace
" pls dad pls don't call anyone.." Ya fada cikin sanyinmurya, ahankali alhaji ya daga idanuwa ya kalleshi Sannan yace
"Doctor zan Kira..." Alhaji ya amsa mashi, kaman yaro suhail ya girgiza Kai ya daga bayan both hands dinshi da sukayi baki saboda injections yace
"Dad I don't want any needle going into me anymore...kawai I want to rest...ganin ku tare Dani makes me better..." Suhail ya fada ahankali, hajiya Kama hannunshi tayi Tana kallon yanda duk jijiyoyin bayan hannunshi sukayi baki, kawai imagining take her son is suffering because of her, she can't believe all this is happening because of her selfish attitude,
"Ko da Maryam ba kowa bace bai kamata in hanaka aurenta ba...bai kamata in shiga tsakanin ku ba..."  Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, tsoki alhaji yaja tare dacewa
"Daga baya kenan..." Yafada sounding so angry,
"Kuyi hakuri...in wani Abu ya sameka Nima dole sai na kashe Kaina...I won't be able to live remembering nice sanadiyar mutuwar only son Dina ba..." Hajiya ta fada cikin matsanacin kuka, ahankali suhail ya dinga girgiza mata Kai yana goge mata hawaye, ahankali ya Dan kwanta baya hajiya tayi saurin cire shoes dake legs dinshi ta tare da Dora kafarshi kan kafarta Tana massaging ahankali, idanuwa ya lumshe, alhaji  dake tsaye yana ta trying number Doctor bai zuwa ya maida phone dinshi cikin aljihu ya taka ya zauna kusa da kan suhail ya Shafa kanshi yana cewa
"Son nothing will happen to you...kullum Ina fada maka namiji is meant to be strong amma saboda irin rainon da wannan matar tayi maka komai makes you vulnerable...da akwai mata da yawa...you can marry 4 today if you wish...in so cutane hakuri né maganinshi..."
"Dad am trying..." Shine abinda suhail ya fada kaman yana Jin bacci,
"No...just learn to be strong...ka manta da komai...am sure you don't want to die without having a child....if you're strong before you know it komai zai zama kaman ba'a taba yi ba...pls be strong for me...I beg you..." Alhaji ya fada yana  kuka, ahankali suhail ya daga Kai ya Dora kan kafar alhaji ya bude idanuwanshi da suka Kara fitowa saboda yanda ya rame yace
"Dad am trying...dad kayi hakuri...ni Kaina na gaji...I feel so restless...I feel so tired...ko makiyaina bana fatan ya shiga halin da na shiga,...I have seen it all...na gaji dad..." Ya fada cikin kuka in a low voice, hajiya sai massaging legs dinshi take Tana kuka,
"Nidai promise me you will be strong for me..." Alhaji yayi commanding dinshi, cikin kuka ya daga mashi Kai, da sauri hajiya tace
"Dan Allah alhaji ka bani address din su...zan je..in durkusa in bata hakuri...pls ka taimaka min..." Hajiya ta fada with her swollen eyes, kallon banza alhaji ya watsa mata without saying a word,
"No mommy..rabon aliyu ce...I don't want to stand in the way of destiny saboda San zuciyata...pls kar kije..."ya fada mata, Shafa kanshi alhaji ya dingayi bayan kaman minti ashirin bacci yayi gaba dashi, ahankali hajiya ta ajiye kafarshi kan gado ta mike, ta koma gefe daya, har lokacin bata bar kuka ba, shima alhaji ajiye kanshi yayi kan pillow ya mike ya bar dakin, da sauri hajiya ta bi bayanshi Tana cewa
"Alhaji pls ka taimaka min da address din da take..." Ta fada Tana biye dashi, banza yayi daita ya shige part dinshi har lokacin Tana biye dashi Tana kuka, afusace ya juyo yace
"Wannan kukan da kike will be nothing compared to Wanda zakiyi in har wani Abu ya samu suhail...ba ke yar Wulakanci da ganin you're classy and better than everyone ba?.. Ke babu Mai aji wajenki sai Wanda kika San asalin shi...babu Mai matsayi wajenki sai Wanda kika San ko shi wanene...you see what your attitude has gotten my only son into...ya rabbi don't let my only son suffer for the sins of his mother...ya rabbi ita da take Wulakanci ta gani gabanta...ita da bata ganin darajan kowa har ni mijinta ta gani a kanta...rabbi don't let her learn her lesson by my son...."  Alhaji ya fada face dinshi cike da hawaye, ahankali hajiya tayi kneeling Tana cewa
"Kayi hakuri...Wallahi ba zan Kara ba..." Ta fada crying very loud, alhaji zama yayi still crying yana cewa
"Somethings are Late to apologize for...har abadan Maryam bazata taba mantawa da halinki ba koda kuwa kin cinza...likewise suhail bazai taba mantawa dacewa ke kikayi sanadiyar rabuwarshi da yarinyar da yafiso ba...that's if he makes it....kullum sharawa nake baki kan halinki amma dayake ban isa dake ba..baki dauka ba..."
"Amma alhaji ai sai ka fada min ko ita wacece...da ka fadamin da Wallahi duk bamu shiga halin da muke ciki ba..." Wani irin kallon banza alhaji ya watsa mata Sannan yace
"Look at what you're saying...wato ke sarauniyar mata ce da zanci amana saboda ke....Salima data rike ta hannu bibbiyu fada mata nayi?... Kawai it's your attitude that is hunting you...duk Wanda yaki ji bazai ki gani ba....this is just the beginning...kawai I just pray my son recover from this..." Alhaji ya fada yana karkada legs,
"Amma nasan ai kilan ka fada mata ko ita wacece...nasan you told her she's the daughter of your boss...daman you care about her more than m..."
"Kedai ba chanzawa zakiyi ba..,halin ki na rashin yarda yana nan tare dake....you think zanci amana saboda inasonta fiye dake?... Ni ba kafiri bane...Don kafiri né kawai baisan mahimmacin amana ba...ko suhail baisan ita wacece ba har saida yaje gidansu ya gano da kanshi.,.and shima dayake Muslim né bai fada maki ba....kawai kedai your bad, arrogant, selfish and stupid attitude have caught up with you....like I said this is just the beginning..." Yafada Sannan ya juya ya shige bedroom dinshi ya barta nan zaune Tana sharbar kuka. 
Chapter 159 · 0% Book details