← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 190

Sashe 150

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 10 min read

A Dubai suhail né zaune a falo yana magana da wasu mutane, bai maganar minti biyar sai yayi tari wato coughing,
"Sir I think you should see the doctor again..."Inji daya daga cikin wayanda suke zaune nan cikin falon, shuru suhail da duk ya rame ya koma kaman bashi ba yayi yana sauke ajiyan zuciya daga Tarin sa yayi Don in yayi tari sai ya huta Sannan ya cigaba da magana, bayan sun gama Don da alaman meeting né sukayi suka tafi da minti sha biyar humaira ta shigo da wasu files, signing yayi ta fita dasu Sannan ya koma ya kwanta, idanuwa ya lumshe, tunanin how the pass three months have been for him kawai yake, it's among the longest moment of his life, rayuwa ya zame mashi unbearable tunda Maryam ta rabu dashi for good then hajiya bata amsa wayarshi ko zai shekara yana Kiranta bata piçking, kawai he feels like barin aikin gaba daya saboda Rabin da ya je office har ya mance, komai daga gida yake yi, he's health is deteriorating, sai ya kwana biyu baici komai ba sai liquid abu, kullum sai tunanin why is Allah punishing him this much yake, ya sha Kiran salima Don suyi magana da Maryam tunda Her line is not going, duk sanda ya Kira Salima ta bata sai dai kawai tace yayi hakuri she can't take it anymore, that is the only word da take fada mashi sannan ta maida was salima wayarta. Wayarshi yayi ringing ya daga Kai tare da daukar wayar, alhaji Mahmoud ya gani, da sauri ya mike zaune ya daga wayar tare da sallama, gaida shi yayi cikin girmamawa ya amsa Sannan yace
"Ya jiki?."Alhaji Mahmoud ya tambayeshi, am getting better,
"iin sa anyi maka booking checkup ko yaya?.." Ya tambayeshi,
"Aa sir...am getting better..zanyi kokarin zuwa office gobe...." Ya fada mashi cikin Sanyinmurya, shuru né ya Dan biyo baya for a moment Sannan alhaji Mahmoud yace
"What are they saying is wrong?.." Ya tambayeshi,
"Yar ka ce problem Dina..." Suhail ya fada cikin ranshi Sannan yace
"Sir sunce hawan jini...sai heart problems..." Salati alhaji Mahmoud ya farayi yana cewa
"That sounds bad,...I will talk to one or two doctors...let's see what solutions we will have..." Inji alhaji Mahmoud that sounds so disturbed,
"Ok sir..." Suhail ya amsa mashi sannan sukayi sallama. Shuru suhail yayi yana tunanin gida. Before baiji azaban da yake ji Yanzu ba, but hearing her saying I love you and break up with him is really killing him slowly, yasan ba lallai ya rayu ba because shi kadai yasan yanda yake ji cikin heart dinshi.

Maryam kam a waiting area na labour room babu abinda take sai zarya, ko ita ce Mai haihuwan sai haka, duk nurse data gani sai ta tambayeta ya antinta take, tun suna bata amsa suka fara banza daita, Jin shuru har kusan hour uku yasa ta fara rusa kuka wai ita a barta ta shiga, Inna rarrashinta ta dingayi amma tayi banza daita, after like minti ashirin wata nurse ta fito ta kalli Maryam tare dacewa
"Tou ki kwantar da hankalinki...ta haihu an samu baby girl..." Tsalle Maryam ta daka saboda farin ciki, haka ta dinga cikin hall din da suke Tana girgiza jikinta, duk ta mance da wani zancen Salman, da gudu ta fita waje zuwa wajen motar alhaji duk Wanda ya ganta sai yayi tunanin sabuwar mad person né, alhaji dake zaune ciki mota yayi saurin fitowa ganin yanda Maryam ta taho aguje, da sauri ta rike hannunshi Tana haki tanacewa
"Daddy..it's a girl...daddy macece...ta haihu..." Ta fada sounding so super duper happy, dariya alhaji yayi tare dacewa
"Alhamdulillah...Allah na gode maka..." Alhaji ya fada,
"Daddy muje ka fada masu su dauko mana babyn..,those nurses a kind of rude..." Ta fada Tana rike da hannun alhaji, dariya yayi yace
"Daughter ki Bari a gyara su...zasu bamu..." Alhaji ya fada yana biye daita, wurin labour room din suka koma bayan kaman minti goma aka fito da new baby, da gudu Maryam ta amshe ta Tana kallon face din babyn, she can't just express how happy she is, tunda take bata taba witnessing irin wannan farin cikin ba, bata taba zama da mutum ya samu ciki har ya haifo such wonderful bundle of joy ba, kallon alhaji dake tsaye yana jiran Maryam ta gama ta mika mashi tayi tace
"She have my nose..." Ta fada Tana dariya, dariya alhaji yayi yana kallon yanda take rike da babyn, wata nurse ce ta fito tace
" yaruwa ki rike babyn da kyau mana.,,kin kama kin rike ta kaman ba mace ba?.." Inji nurse din, ahankali Maryam ta juya wurin Inna dake tsaye Tana kallon su tace
"Inna gyara min ita..." Ta fada mata, amsar babyn Inna tayi ta gyara mata, atakaice dai sai da alhaji ya roketa Sannan ta bashi baby, bayan ya gama yi mata adua ya sake mika mata,.
Sai the following say suka dawo gida inda Maryam bata bar hospital ba har aka sallamesu, she loves the new baby so much Don she feels so bond with her, suna dawowa gida ta shiga dakinta tayi wanka ta fito daure da towel, gaban mirror ta tsaya Tana kallon kanta, kawai sai taji saukar Marin Salman a kunnenta, sai lokacin duk abubuwan da ya faru jiya ya dawo mata sabo, she don't just know what to do to him to make her happy, zama tayi bakin gado ta dauki wayarta tayi dailing numbar dad dinta, sai da ta kusa tsinkewa Sannan yayi piçking, sallama tayi mashi ya amsa suka gaisa, nan take fada mashi matar alhaji ta haihu, yanda take magana sounding so happy yasa dad dinta dariya, sai da ta gama maganar haihuwan sanna. Tace
"Dad zan iya amsar kyauta da na yiwa mutum?.." Ta tambayeshi, bai nemi Jin abinda ke faruwa ba yace no, shuru Maryam tayi Jin amsar dad dinta, she just wish zata iya fadawa Salman ya bata every penny data bashi,
"Baby..." Alhaji ya kirata
"Yes dad..." Ta amsa mashi,
"Wai ya maganar mu...najiki shuru..ko dai I should choose for you as our religion permits...." Da sauri tace
"No dad...pls no...I will choose..." Ta fada jikinta na rawa,
"But kin dai Sam bazan wuce days Dana baki ba kou...in har baki kawo ba I will choose anyone for you...na dai baki damanki..." Ya fada mata,
"Pls dad I need more time...pls give me..."
"No..." Taji ya fada mata atakaice then sai yayi offing phone dinshi, nan take Maryam ta wulla da wayarta ta fara kuka, tunawa tayi da suhail tasan assuming mom dinshi is not against their relationship da bata da case din komai, da shi zatayi choosing amma now it's not possible, she can't be a daughter in law to the woman who gives her the insult of a lifetime, pillow tayi hugging Tana kuka, she's missing suhail so much, tunawa tayi da dad dinta will choose a hubby for her, da sauri ta mike Tana goge face dinta tare da cewa
"I have to do something...I can never marry a total stranger..." Ta fada Tana zarya cikin dakinta, shuru tayi for a moment sai tace
"Aliyu..." Ta furta under her breath, idanuwa ta zaro tare dacewa
"Yes aliyu...he's the solution...he's the answer to all..." Ta fada sounding a little bit so excited, tsayawa tayi Tana tunawa da statement dinshi na ranar da sukayi magana last,
"I love you but na barki saboda suhail..." Tayi remembering, idanuwa ta lumshe Tana imaging yanda resemblances dinshi suke, he's height, skin color masculine da komai
"He's cute too..." Ta fadawa kanta, ahankali kuma ta zauna bakin gado ta sake rushewa da kuka Tana Kiran sunan suhail,
"Suhail...suhail...suhail..." Kawai ta dinga maimaitawa Tana hawaye, she can't just believe she will not be with suhail, tasan nobody will allow her marries him after everything, tafi hour Tana kuka sanna ta sake shiga bathroom ta wanke face dinta ta fito ta saka long gown, she have the intention na kiran aliyu amma she wants to tell salima about it first, fita tayi ta shiga dakin salima, mommy suhail ta gani zaune ta Dora kafa daya kan Daya, Tana ganinta taji gaban ta yayi mugun faduwa Don she's so much afraid of her, she has left a mark on her skin and her, wani irin kallon banza tayi mata tare da Jan tsoki,
"Karabiti..." Hajiya ta fada mata, jiki na rawa Maryam ta juya ta bar dakin. Dakinta ta koma Tana hawaye, lekawa ta dingayi ko hajiya ta fita, bayan kaman minti goma taga fatar hajiya Sannan ta goge face dinta Don batason saka salima cikin damuwa, dakin ta koma ta taka zuwa inda baby ke kwance tayi mata kiss a both cheeks, forehead, sai a lips Sannan ta dawo kusa da salima, salima na ganinta tasan tayi kuka,
"Dear kiyi hakuri da duk abinda zatayi maki...ita ke da haushi ba ke ba...kinji kou..." Ahankali Maryam ta daga mata Kai
" Ni wani Abu nakeson yi,.,nace Bari in farafada maki kafin in aiwatar da abun, .." Zama Salima ta gyara Sannan tace
"Ina sauraron ki..." Ahankali Maryam ta saka baki kunnenta ta rada mata..." Idanuwa Salima ta zaro Tana cewa
"Haba Dan Allah ..ina kika taba ganin anyi haka?.. Ai bazai ga darajar ki ba...gaskiya ni ban yarda da wannan shawarar ba..." Salima ta fada cikin bacin rai, marairacewa Maryam tayi tace
"Anty I have no choice...gaskiya ban iya zama dad ya hadani da Wanda banso ba.." Ta fada kaman zatayi kuka,
"In haka né zan yiwa alhaji magana ya bawa Maman suhail hakuri ta Bari kuyi aure da suhail...in yaso in ta gane ko ke wacece ta durkusa ta baki hakuri..." Inji salima, da sauri Maryam ta girgiza mata Kai,
"Aa...banaso...kawai zanyi wa aliyu magana..."
"Ai bazai amince ba...yasan suhail na sonki..."
"Anty in Allah ya yarda zai amince..," Ta fada Tana mikewa, salima shuru tayi without saying a word,
"Bari in kirashi..." Ta fada Tana barin dakin, salima dai bata ce komai ba. Maryam Tana fita ta dauki small phone dinta dake dauke da number aliyu ta kunna Sannan ta dauko number dinshi ta saka a new phone tayi dailing, sai da ta jera mashi kusan miss calls biyar Sannan ya dauka, sallama yayi kaman bai son maganar, amsawa tayi ta fada mashi she's the one, sai lokacin ya warware voice dinshi suka gaisa, nan take fada mashi tanason ganin shi,
"Ki bani nan da hour uku...Ina office..." Ya fada mata, ok kawai Ta amsa mashi ta kaste wayar tana tunanin yanda zatayi confronting dinshi da abinda takeson fada mashi. Aliyu na tashi daga office bai wuce gida ba yazo gidansu suhail, sanye yake da white long sleeve sai black plain trouser, bayan yayi parking ya fito ya nufi part din salima tunda yasan nan take, shiga yayi suka gaisa da maijego Sannan Maryam ta rakoshi waje, jikin motashi suka tsaya ya harde hannunshi a chest dinshi tare dacewa
"Am all ears..." Ya fada hoping yaji tayi maganar ta da suhail, baki ta bude zatayi magana sai kuma ta kasa,
"Pls kiyi magana..,daga office fa nake..." Ya fada yana kallon yanda bakinta ke motsi but nothing is coming out of it.
"I want you to help me with something...." Ta fada mashi,
"Ke ma kinsan babu abinda zai gagareki wajena...just say it..." Ya fada mata sounding so friendly, idanuwa ta lumshe tare dacewa
"Are you sure ko me na bukata zakayi min?.." Ta sake tambayan shi, d sauri ya daga mata Kai yana cewa
"Anything for you..,ai mun zama .." Ya fada mata yana relaxing a jikin mota, ajiyan zuciya ta saki before saying
"I....want...you...to...marry me..." Ta fada mashi word din na fita daga bakinta one after the other, aliyu zaro idanuwa yayi tare da kakkabe kunnenshi Don yana tunanin bai jita da kyau ba yace
"I didn't catch that..." Ya fada Mata,
"I want you to marry me..." This time Ta fada clearly idanuwanta lumshe, wani irin dariya aliyu ya kece dashi Sannan yace
"Sorry to say but am sure you have gone nuts..."
[2/10, 8:23 PM] 0mmr Farouk: 48💚💛💜💙❤️
Wulakanci dodone...
💜💛❤️💚💙
Chapter 150 · 0% Book details