← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 190

Sashe 67

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 5 min read

zafin da kakeji zai ragu...besides remember Maryam da kake maganar ta always..she might be in to you.." Dariyar karfin Hali suhail yayi yana cewa "Wai why kuke maganar Maryam?.. I talk about maryam kafin in San Fatima...now Fatima is all I want...pls ku gane abinda nake ciki..pls ku kyaleni Inji da abinda ya dameni..." Suhail ya fada yana kwantawa tare da bawa sadeeq baya, "Sorry if am disturbing you...kawai banason dad yace bamu bin umarnin su...kasan it hurts..." Bai idaba suhail ya sake mikewa zaune afusace yana cewa "Yes it hurts amma dad yana kallon yanda nake Shan wahala amma he can't tell me inda take..all because ya dauki flimsy amana..." Da sauri sadeeq yace "Kai stop that...wallahi tallahi amana it's not flimsy...wallahi it's better ka shiga irin wannan situations din sau billion da ka Bari dad ya ci amana all because of you...gaskiya nayi mamakin wannan statement din naka..." Inji sadeeq, suhail shuru yayi saboda yasan sadeeq is right kawai ya Bari son Kai ya rufe mashi Ido amma yasan amana ba abunci bane, "I know...amma in ba gan Fatima ba ban barin kasar nan.." Ya fada atakaice yana Kara komawa ya kwanta, "Nidai pls kar ka yi wa dad gardama...pls I beg of you..." Sadeeq ya fada yana mikewa, suhail banza yayi dashi, "Zan tafi..Allah ya Kara lafiya..." Inji sadeeq, ko kallon inda yake suhail baiyi ba balle ya amsa mashi. Fita yayi ya nufi part din dad, falon ya tarda sho zaune yana operating system, kasan carpet sadeeq ya zauna yayi wa alhaji bayanin yanda sukayi, haushi alhaji ya karaji ya sallami sadeeq, afusace alhaji ya fita ya shiga part din hajiya ya fada mata taje ta fadawa suhail ya shirya ya tafi abroad ko kuma ya bar mashi gidanshi, ita Kam hajiya cewa tayi oho. Alhaji komawa yayi part dinshi ya zauna tare da tagumi, he knew suhail too well yasan he's no is no, tunda ai ba tun yau yakeson yayi aiki ba amma kememe yakiyi, ya rasa inda zai sa Kansa yaji dadi Don ko kadan bai iya fadawa alhaji Mahmoud cewa bai zuwa Sannan rasa yanda zaiyi suhail yaje, for sure yasan bazai ci amana mutum ta Allah taci shi ba Sannan ba yanda zaiyi ya fadawa alhaji Mahmoud cewa suhail yace he's not coming dukda baisan dalilin dayasa ya kirashi ba, mikewa yayi tsaye yana Kai da kawowa cikin falon, bude kofa akayi salima ta shigo cikin long hijab har kasa, hannu alhu a ware mata Ta fada jikinshi Sannan ta daga Kai ta kalleshi tare dacewa "Kaman da akwai abinda ke damunka..." Ta tambayeshi cikin sanyinmurya, dariya alhaji yayi tare dacewa "Kece ke damuna...muje in nuna maki..." Ya fada yana daukar ta Don ko kadan he doesn't want to show his anger ko gazawar shi a gabanta. Suhail kam sadeeq na fita ya maida headphone dinshi ya cigaba da sauraron voice dinta har Allah yasa ya samu bacci. Da asuba ya mike ya watsa ruwa as usual sannan ya fito yayi sallah nan cikin dakinshi, komawa yayi ya kwanta, ji yayi an bude Kofan falon shi, he can feel it's his father, da sauri ya sake lullubewa kaman yana bacci, alhaji na shiga bedroom din yaga suhail kwance, zama yayi bakin gadon sannan ya taba legs dinshi, ahankali suhail yayi mika kaman Mai bacci, yaye blanket din yayi ya kalli alhaji tare dacewa "Dad good morning..." . "Morning..kayi sallah?.." Ya tambayeshi calmly, "Yes dad.." Ya amsa mashi suhail yana tunanin why he's calm Don ko kadan he's not expecting that, "Ya jikinka?.." Alhaji ya sake tambayan shi, "Da sauki.." Ya amsa mashi " tashi muje falo zamuyi magana man to man..." Inji alhaji yana mikewa, ahankali suhail ya sauka daga kan gado sanye da jallabiya dake jikinshi, falo ya fito ya tarda dad zaune shi kuma ya samu waje kasan carpet ya zauna, ajiyan zuciya alhaji ya saki Sannan ya e "Son why kakeson watsa min kasa a Ido?..." Shine tambayan da yayi wa suhail, suhail Dan daga Kai yayi ya kalleshi Sannan yace "Never dad...bazan taba haka ba"." "Wani irin never?... Gashi face to face nace kaje abroad ka ce no?... Sannan you're stanb y your word kan bazaka je ba?.. Why?.. Shin ban Isa da Kai ba?.." Ya dada cikin bacin rai, ahankali suhail yace "Daddy ka isa Dani..." Ya fada kanshi kasa, "Then in na Isa da Kai ka shirya later za'a zo daukanka.." Alhaji ya fada mashi, shuru suhail yayi for a moment Sannan yace "Dad...ni gaskiya nasan ko naje I will be useless...my heart is left here.. I don't want to be a disappointment..nidai if only I can talk to Fatima ko kuma Jin muryar ta..I will be okay.." Ya fada inform of blackmailing, dariya alhaji yayi yana kallon shi, he just wish zai iya fada mashi cewa he's going to her amma amana ta Hana hakan, "Ok na gane... Can I promise you something?.." Ya fada wearing a smile, suhail daga Kai yayi ya kalleshi yaga irin murmushin da yake, Dan sadda Kai kasa yayi Sannan yace "Pls daddy..." Bai idaba alhaji yace "Just listen mana..." "Ok dad..promise me..I know you're a man of integrity and a man of your word..." "Good...kaje if what you fine didn't please you nayi maka alkawarin zan kaika har inda Fatima take..." Ya fada sounding serious, suhail kallon shi yayi Sannan yace "Dad wayau zakayi min kou.." Ya fada kaman zaiyi kuka, dariya alhaji ya sakeyi yace "Not at all..just trust me..." "But dad you said if want I find doesn't please me... Ban gane ba..." Hannu alhaji ya daga mashi yana cewa "No questions...do we have a deal?.." Suhail rolling idanuwa yayi kaman mace Sannan yace "Deal.." Ya fada mashi amma deep down he's not happy at all.
Chapter 67 · 0% Book details