← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 190

Sashe 19

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 7 min read

The following day same thing da ya faru jiya ya sake faruwa, asabe taje gyarawa suhail daki ya korata wai ta Kira Maryam, Tana cikin bacci aka tadata taje tayi mashi aiki, yau ma bata gaidashi ba, kyaleta yayi sai da ta gama sannan tazo wucewa gabanshi, har lokacin yana zaune falo, kawai sai ya samata kafa ta fadi, da sauri ta mike zata tashi galla mata harara
"Baki iya gaisuwa ba kou?.." Ya fada Fuskanshi kaman bai taba dariya ba, shuru tayi cikin ranta tan kome zai faru bazan taba bude bakina in gaidaka ba,
"Baki iya gaisuwa ba?.." Ya sake repeating question din, still banza tayi dashi,
"Come here..." Ya daka mata tsawa, jikinta na rawa ta karaso inda yake, mikewa yayi ya Kama kunnenta,
"Kunnen kanshi gareki kou..." Ya fada yana Kama kunenta da karfi, hannuwanta ta fara yarfawa Tana fashewa da kuka, bakinta ya buge tare dacewa
"Shush..." Da sauri ta Dora hannunta kan bakinta hawaye na zuba,
"Dan ubanki ki gaidani ko in cire maki kunne..." Maryam kuka ta cigaba dayi amma batace komai ba, tsayawa yayi yana kallon yanda take zubar hawaye sannan yana tunanin why gaisuwanta matter to him, just two days a gidan amma kaman tayi shekara,
"Amma ke yar iska ce kou...tunda naga gaisawa ma kike da maza...tou mu gaisa..." Ya ski kunnenta tare da mika mata right hand dinshi, Maryam Dora hannunta tayi kan kunnenta Tana kuka, ganin bata da niyyan mika mashi hannu yasa ya daga left hand dinshi ya bugi keyanta, wani Abu yaji kulle awajen, San bata fuska yayi tare dacewa
"Me kika daukar min?.." Ya fada yana Kara Jin abinda ke kulle a keyanta, ko kasan bai yi zaton gashin kanta bane,
"Wato daga ki gyara min bedroom har kinfara kulle min kaya kina fita dasu kou...now bring it out..." Ya daka mata tsawa, Maryam kuka kawai take Tana Jin yanda yake Kama gashinta data kulle baya yana ja da karfi,
"Bude Dan ubanki!!', ya fada da karfi, bata San lokacin da Ta fada hijab dake kanta ba, da sauri ta warware ribbon dake kanta, nan gashinta ya bazu bayanta, da sauri suhail yaja baya saboda tsoro Don bai taba ganin gashi a gabanshi haka ba, still Maryam bata tsaya ba sai da ta saka yatsunta cikin gashinta ta bazasu yanda zai gan babu komai cikin kanta sai gashinta, baya suhail ya Kara ja, Maryam najin shuru tayi saurin tattare gashinta baya ta dauki hijab dinta ta saka ta bar dakin, suhail yafi min goma bai dawo sense dinshi ba saboda abinda ya gani,
"My Allah..." Ya fada under his breath, ahankali ya koma ya zauna yana kallon Kofa data bi ta fita.

Da kuka Maryam ta shiga dakinta, baba rabi ta ganta, da sauri tabi bayanta Tana tambayanta abinda ke damunta,
"Yace....ni...ba..ra..wo...me Maryam a thief" Ta fada cikin kuka, ahankali baba rabi ta Dora kanta kan shoulder dinta,
"Ki bar kuka...haka yake..sai hakuri..." Baba rabi ta fada mata sannan ta Kara da cewa
"Zan fadawa ubanshi...tunda ya bani amanarki..." Da sauri Maryam ta girgiza mata Kai,
"Tsoro..." Ta fada mata atakaice,
"Babu abinda zaiyi maki...zan fadawa babanshi ya ja mashi kunne,," still Kai Maryam ta girgiza mata, baba rabi bata Kara cewa komai ba ta shiga bathroom din dakinta ta hada mata ruwan wanka. Shiga tayi tayi wanka Tana kukan takaici da bakin ciki. Tea baba rabi ta hada ta kawo mata ba tare da kowa ya sani ba Don masu aiki basu Shan tea amma yanda alhaji ya nunawa baba rabi muhimmacinta yasa ta sawa ranta zatayi duk abinda ya kamata don kar ta sha wahala kaman sauran masu aiki gidan.

Karfe 8 alhaji ya tafi office nan ya fadawa Salman ya dawo gida ya jira Maryam ta shirya ya kaita islamiyya, dadi Salman yaji Don he will have a chance yayi magana da Maryam ko da word daya né. Karfe 8 p da rabi suhail ya Kai mom dinshi wajen aiki, cos kullum shi ke kaita aminu Kano teaching hospital ya maidota gida. Yana tuki ya kalli mom dinshi
"wai mom meye relationship din mu da wannan yarinyan?.." Ya tambayeta , Dan baki mom dinshi ta tabe before saying
"Your father said yar cousin dinshi ce..." Shuru suhail yayi kaman Mai tunani,
"anything ?" Ta tambayeshi,
"Nothing mom..." Ya fada cikin sanyinmurya, kallon shi tayi Sannan ta dauke kanta, suhail tuki kawai yake amma ya rasa abinda ke mashi dadi.

Sallama Salman yayi lokacin daya shiga falo bayan ya ajiye alhaji a office, baba rabi ce ta fito, gaisawa sukayi sannan yace
"Dan Allah ki fadawa Fatima zan kaita islamiyya da Karfe tara..Yanzu sauran minti ashirin.." Ya shaida mata,
"Tou shikenan...Bari in fada mata.." Baba rabi ta fada sannan ta juya ta koma dakin Maryam, nan ta fada mata abinda Salman yace. Kaman Tana jira ta mike ta saka Kayan islamiyya tare da saka long hijab har kasa, tsayawa tayi Tana kallon kanta, kawai sai ta Dan saki murmushi Tana cewa
"Unbelievable...." Ta fada Tana fita daga dakin. Wurin baba rabi taje tayi mata sallama sannan ta fita waje, Salman na zaune cikin mota yana jiran zuwanta, yana ganinta yayi saurin fita daga motan ya bude mata ta shiga, shima ya shiga yayi suka bar gidan. Yana tuki ya kalleta ta cikin mirror tare dacewa
"Pls zaki iya fadamin sunanki?.." Bata yi wasting time ba tace
"Fatima... " Ta amsa mashi babu wani Jan aji daman abinka da tashin turai
"Nice name,...am Salman...nine driver alhaji..." Ya fada mata yana kallon reaction dinta ta mirror, gani yayi bata wani Chanza face ba
"That's nice..." Ta fada mashi, Dan murmushi ya saki sannan yace
"Daga Ina kike?.."
"Jos..." Ta amsa mashi, cikin ranta Tana
"I will surely visit this Jo's some day..."
"Ni kuma daga Niger nake...amma parents Dina suna nan Kano...kefa?.." Ya tambayeta yana tuki
"My mother is late...daddy kuma yana.....jos..." Ta fada kaman she doesn't want to talk. Shuru me ya Dan biyo baya sannan yace
"Jiya da yau naga kina fitowa daga bangaren suhail kina kuka...me yake maki?..." Ya tambayeta Kai tsaye, shuru tayi Tana wasa da yatsunta for a while sannan tace
"Don't want to talk about it...." Daga ki yayi ya kalleta ta mirror sannan yace
"Kin taba zama abroad né?.." Da sauri ta daga Kai ta kalleshi Sannan tace
"Why do you ask?" Dariya yayi sannan yace
"Naji kina turanci ta cikin hanci kaman turawa..." Itama dariya tayi bata Kara cewa komai ba,
"Pls in tambayeki wani abu?..."
"Yes.."
"Will you be my friend?.." Ya tambayeta, without wasting time tace
"Why not..." Ta fada ba tare da ta damu ba, turawa suna iya ajiye friends maza kala amma babu batun so, Don haka Don aliyu da Salman sunce suna son zama abokin ta bata dauke shi wani Abu ba, she feels it's normal, dadi Salman yaji
"Friend me kikeso in sayo maki in zan zo daukanki?.."
"Don't worry...nasha..tea..."
"I insist..."
"I love ice cream..." Ta fada Tana dariya kaman sun dade da sanin juna, dadi yaji tare dacewa
"Amma kina da kyau sosai...." Ya fada yana kallon ta ta mirror, murmushi ta saki ta kalleshi ta mirror tare da cewa
"Thanks..but I have heard that like a million times..." Tafada Tana dariya shima dariya yayi yana cewa
"Am jealous..."
"Don't be...they're all friends..." Ta fada atakaice, kafin su Kai islamiyya har har sun sha hira kaman sun dade da sanin juna, daman Maryam is lonely saboda rashin abokin hira Don ko jiya da ta zauna cikinsu murja ba dukan abinda suke cewa take ji ba. Tare suka fita kaman wasu couples suka isa office din shugaban makarantan. Nan yasa aka kaita aji sannan Salman ya koma yana tafiya yana murmushi.

Suhail na dawowa daga inda ya Kai mom dinshi ya shiga main falo, kiran da yasaba yayi masu suka fito,
"Ina Fatima!.." Ya tambayesu atakaice
"Ta tafi islamiyya..." Binto ta amsa mashi, daure fuska yayi tare da Jan tsoki ya Kama hanya ya bar falon. Falon shi ya koma ya kwanta kan kujera tare da Jan tsoki. Bai fin minti biyar sai yaja tsoki. Ahankali na taka zuwa inda yake kwance na danyi tapping shoulder dinshi ya daga manyan eyes dinshi ya kalleni
"What's wrong?.." Na tambayeshi, tsoki ya sake ja tare dacewa
"Ban sani ba!!!"

One love 💜💛❤💚💙
9 💛💜❤💙💚
Wulakanci dodone
💛💚💙💜❤

® zuwairat (ummumaryam)

0⃣9⃣
Chapter 19 · 0% Book details