Sashe 26
Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon shi tayi tare da kauda kanta gefe, feeding namiji ba komai bane wajenta tunda mostly Tana feeding dad dinta sannan in suna tare da Erick Tana feeding dinshi amma ko kadan batason feeding suhail, ba karamin haushinshi take ji ba,
"I said feed me!!" Ya daka mata tsawa, da sauri ta dawo hayyacinta, Dan matsawa kusa da dining din tayi ta saka hannu ta dauko meatball da toothpick zata Kai bakinshi ya kauda Kai tare dacewa
"Sit..." Ya umarce ta, Fuskanshi kaman bai son ko ganinta, ajiyewa tayi ta jawo kujera ta zauna, sai bin hannunta yake da kallo, sai Yanzu ya ga nails dinta da kyau, suna da kyau sannan Tana barin fingers, da ganin nails dinta kasan ba na yar wahala bane, sai da ta zauna ta Kara dauko ta Kai bakinshi, sai lokacin ya bude baki ya amsa yana kallon face dinta, Sam babu walwala tattare daita, shima daure fuska yayi sannan yace
"Amma ke arniya ce kou..? " ya tambayeta, shuru tayi Don batasan ma'anar arniya ba,
"Baki jina..?" Ya tambayeta yana kallon fingers dinta dake rike da toothpick, daga Kai tayi ta kalleshi taga fingers dinta yake kallo, da sauri ta ajiye toothpick din ta maida hannunta kasa,
"Kina sallah." Ya tambayeta, kaman ta fashe saboda takaici, Kai,ta daga mashi alaman eh
"Amma kike barin fingers haka kaman kafira?..." Sai lokacin ta gane abinda yake nufi, sadda Kai kasa tayi tare da Kara boye fingers dinta,
"Feed me and don't let me ask again..." Ya fada mata, da sauri ta dauki toothpick ta Kai meatball bakinshi, amsa yayi yana tauna yana kallon ta, sai da ya cinye naman tas yace
"Ke kika dafa?..." Kai ta sake girgiza mashi, mikewa yayi yana cewa
"Stay right there..." Ya fada mata sannan ya shiga bedroom dinshi. Bai dade ciki ba ya fito da set din nail cutters, ajiyewa yayi gabanta, ahankali ta daga Kai ta kalli abinda ya ajiye, yana nufin ta yanke fingers, which is impossible Don dad dinta ma yayi ya hakura, kan seat dinshi ya koma ya zauna yana kallon ta without saying a word, Don yasan ta gane manufar shi, ko daga Kai batayi ba balle ta dauki nail cutter daya ajiye mata, hannu yasa ya Kara tura mata nail cutter din, still bata daga Kai ba, daukan set din yayi ya bude ya Fiddo abun yanka fingers ya mike ya zagayo inda take zaune, gabanta né ya fara faduwa Don her nails are so precious to her, bata ankara ba taji ya Kama hannunta da take boyewa, da sauri ta fixge tare da mikewa tsaye,
"Wow...wato bazaki yanke su ba kou?...to in kin ga kin fita daga dakin nan kin yanka fingers dinki ko kuma Inyi maki dukan tsiya...arniya kawai..." Ya fada sannan ya Kara kai hannu zai Kara Kama mata hannu ta Kara fixgewa tana ja da baya, kaman zatayi kuka tace
"Sorry..." Ta fada muryar ta na rawa,
"Sorrin ubanki?... Wallahi sai kin yankesu...now bani hannunki..." Ya fada yana stretching hannunshi gaban ta, Maryam Kara ja da baya tayi tare da boye hannunta a bayanta, bai tsaya bata lokaci ba ya kamata ya tura ta kan kujera, nan take ta fashe da kuka,
"Sorry..." Kawai take fada mashi Tana kuka, hannunta data boye a bayanta ya fixgo da karfi, ta Kara fashewa da kuka Mai karfi, bayan Dayan hannunshi yasa ya buge mata baki yana cewa
"Rufe min baki danubanki...shegiya arniya...." Da sauri ta rufe bakinta amma hawaye na zuba, mother finger dinta ya Kama ya Dora nail cutter, kuka ya kara kufce mata data ga da gaske yake
"Sorry...." Ta fada cikin kuka, tsaya kallonta yayi still yana rike da hannunta, yana mamakin dalilin da yasa take irin wannan kukan saboda nail,
"Amman ke jakka ce...saboda akaifa kike irin wannan kukan?... Tou wallahi kiyimin shuru ko kuma in ballaki..." Ya daka mata tsawa, da sauri ta Kama bakinta. Finger dinta yake yankewa amman kaman zai cire da fatanta, sai kuka take. Bai saki hannunta ba sai da ya gama yanka fingers dinta tas, Tasha kuka har ta gaji sai sauke ajiyan zuciya take bakin ciki kaman ya kasheta saboda Tana kaunar fingers dinta unconditionally. Bayan ya gama ya kalli yanda take shessheka ya saki tsaki tare da girgiza Kai, mikewa yayi daga inda yake a durkushe yace
"Oya tashi ki gyara min dakina...." Ya fada mata atakaice, ahankali ta daga red eyes dinta ta watsa mashi kallon haushi da tsana,
"Oho dai...na yanke...and babu abinda zakiyi...." Ya fada tare dayi mata gwalo, ciki bedroom ya koma ya barta nan zaune Tana share hawaye. Bayan Kaman minti ashirin bai ji motsin ta ba ya sake fitowa ya hangeta zaune sai sauke ajiyan zuciya take Tana kallon yatsunta,
"Wai ke Dan uwarki baki kwashe wayan nan dirty fingers dinki daga dakina?... Ko sai ranki ya baci tukunna...ke baki ma ji dadin ni suhail na yanke maki fingers ba?... Dalla tashi ki gyara min dakina!!!..." Ya daka mata tsawa still again, K'ara daga Kai tayi ta kalleshi new tears suna fitowa, shima kallon ta yayi suka hada Ido, sai yaji Sam bai jidadi yanda take zubda hawaye ba, amma Sam Fuskanshi bai nuna haka ba
"Wai bazaki tashi ba?.." Ya fada yana nufo inda take zaune, da sauri ta mike tsaye ta fara kwashewa. Bayan ta gama ta koma main part. Kafin ta iso har su baba rabi sun kusa gama mata wani meatball. Bata ko shiga kitchen ba ta koma dakinta ta kwanta ta rungume hannunta sai kuka take daga nan bacci yayi gaba daita.
A katsina kam alhaji yayi magana da salima, inda ta nuna indai zai tayata rike marayunta zata aure shi Don Yanzu basu da kowa, Nuna mata yayi wannan ba matsala bane. Shima nuna mata yayi yana da wata yarinya yar shekara sha takwas da yake so ta zauna wajenta in har Allah ya yarda anyi auren. Nan dai suka tsaida magana kan zai aiko magabata a tsaida rana tunda ba wani wasting time za'a tsaya yi ba tunda su ba yara bane ba. Hannu yasa cikin aljihunshi ya Fiddo kudi ya mika mata Ta amsa cikin ladabi Wanda hakan ya burgeshi sosai, ya tashi tafiya ta rakashi har bakin motanshi ya shiga sannan sukayi sallama, Salman na tukashi alhaji dake zaune baya sai murmushi yake Don gani yake dukda ba auren soyayya zasuyi ba yana ganin zasu zauna lafiya Don ya Dan ga wasu behavior da yake so tattare daita. Wurin innan shi ya koma ya fada mata yanda sukayi da salima, ba karamin dadi inna taji ba har cewa take
"Ni ko gobe né ayi...Don banason ka Chanza ra'ayin ka..." Ta fada mashi, Dan murmushi yayi sannan yace
"Inna ki kwantar da hankalinki ...insha Allah kaman anyi an gama..." Ya shaida mata. Sai wajen Karfe biyu ya bar katsina ya Kama hanyan Kano babu abinda yake sai tunanin abinda zai fadawa hajiya Don deep down yana ganin ya karya alkawarin da ya daukar mata.
Har Karfe uku Maryam Tana bacci, baba rabi ce ta shiga dakinta a karo na uku ta tardata still Tana bacci, ahankali ta shiga dakin da plate na meatball a hannunta, ajiyewa tayi kan table sannan ta tada Maryam, ahankali Maryam ta bude idanuwanta da sukayi mata nauyi, murmushi karfin Hali ta sakar wa baba rabi amma har cikin ranta Tana bakin cikin tadata da takeyi,
"Yau Kinsha barci...har lokacin sallah zuhr ya wuce..." Baba rabi ta fada mata, Maryam bata ce komai ba ta mike ahankali ta shiga bathroom, hannu ta saka zata bude tap sai ta tuno fingers dinta da suhail ya yanke, baki ta tale kaman zatayi kuka Tana kallon hannunta,
"I will not forgive you...wicked creature kawai..." Ta fada kaman zata sake Sabon kuka.
A bangaren suhail kam Maryam na fita daga dakin yayi saurin mikewa daga inda yake zaune ya shiga inda dustbin dinshi yake, ahankali ya saka hannun hagunshi ya fara dauko nails dinta data share ta zuba ciki, saida ya tabbatar ya tsinto su goma duka sannan ya koma bedroom, jerasu yayi kan gadon sannan yayi kneeling gaban gadon yana kallon fingers din, ahankali ya dinga daukan su yana kaiwa saitin bakinshi yana yi masu kiss, saida ya jerawa dukkan su kiss sannan ya daukesu ya saka inda yake ajiye important documents dinshi ya rufe ya koma kan gado Fuskanshi dauke da murmushi, idanuwa ya lumshe tare da cizon lebenshi na kasa, kawai sai ya Dan saki dariya
"Fingers takewa kuka kaman nace zan yanka ta..." Yafada yana dariya Don babu abinda yake tunawa sai yanda Maryam ta bare baki Tana kuka yana yankan fingers dinta, tunawa yayi da hannunta cikin nashi, sai ya daga hannuwanshi biyu ya rungume a kirjinshi tamkar Maryam din ce rungume dashi ahaka bacci ya Kara daukeshi.
Sai da zuhr ya mike ya shiga bathroom yayi wanka ya sake Kaya zuwa Jean da Riga sannan yaje masjid yayi sallah ya dawo, car keys dinshi ya dauka ya tafi hospital Don dauko mom dinshi. Suna kan hanyan dawowa mom dinshi ta kalleshi tare dacewa
"Wai jiya me ya bata maka rai?..." Ta tambayeshi Tana kallon shi bata ko kiftawa, shuru yayi bai amsa mata ba, sai da ta Maimaita tambayan sannan yace
"Ni Raina bai baci ba...kawai gani nayi she don't deserve Marin da ki kayi mata tunda ba laifinta bane...ni na fasa kofin ...." Yafada yana tuki batare daya kalleta ba balle yaga irin kallon da take mashi, hajiya kallon surprise tayi mashi Don tamkar ba shi ba
"Ba dai rufa mata asiri kake ba?... Kirikiri yarinya tace ita ta fashe min cup Kai kuma ka dauki laifinta ka dorawa kanka?... Gaskiya something is wrong..." Ta fada atakaice,
"Nothing is wrong... " ya amsa mata hankalinshi kwance.
"Jiya dad Dinka yayi wata magana da ban gane kanta ba...kuma na tambayeshi dalilin hakan bai amsa min ba..." Inji hajiya, kallonta suhail yayi sannan ya maida kanshi gabanshi tare dacewa
"Me yace?.." Ya tambayeta
"Wai yarinyan amana ce agareshi tunda banason yaci jarabawan zai samo wacce zata taimaka mashi...." Ta amsa mashi,
"Tou mom me hakan ke nufi?...ni ban gane ba" ya fada mata
"Nima ban gane manufar sa ba..." Ta amsa mashi cikin sanyinmurya.