Sashe 143
Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read
jikin ki yake batare daya aureki ba?.. Bakisan haramun né sakarwa Wanda ba mijinki ba jikinki...ko kadan ba zai ba darajar ki ba...babu abinda zaiyi marmari...Wallahi abun kunya né ki shiga gidan namijin da ya gama sanin yanda kike..." Salima ta fada mata hannunta cikin na Maryam, "Ba sex mu kayi ba..." Ta fada mata, " "Ai ba dole sai kunyi sex ba...anason ko yanda fatar hannunki yake kar ya sani har sai kunyi aure...zakiga yana zumudi...amma muddin ya gama sanin yanda jikinki ya ke Wallahi ko ya aureki bai da wani zumudin da zaiyi saboda daman ya San yanda kike...gashi har uwarshi ta ganku tare a haka...Yanzu kina ganin zata yi maki kallon mutuniyar kirki?.." Ta tambayeta, Maryam girgiza mata Kai tayi tare da sake fashewa da kuka Tana cewa "Tace...ni yar karuwa ce...she called me all sorts of name...Wallahi Yanzu kunya fita nakeji...anty Dan Allah ki fadawa daddy ya kaini wani wajen...banason zama nan gidan kuma..." Ta fada cikin kuka, "To kin gani kou...Wallahi har Abadan bazata Kara ganinki da mutunci ba...jiki ya mace abin ado né ga mijinta kawai...ki bar Bari kina zubda mutunci pls...daga Yanzu kar ki kuskura wani ya Kara tabaki...ban sani ko hankali me bai isheki ba amma pls kar ki sake amincewa da hakan,..kinji kou?.." Ahankali Maryam ta daga mata Kai Tana hawaye, kawai ita bata dauki haka da wani Abu ba, it's something that she sees everyday, Sannan bata ganin yana rage mata daraja a idon suhail, "Ki fada min Inji...kiyi min alkawarin bazaki Kara Bari wani ya taba ko da hannunki ba...kinsan ke amana ce a guna...kuma duk abinda kikayi dole zan samu kasona na zunubi...Dan Allah ki yi min alkawari hakan bai Kara faruwa..." Salima ta fada mata sounding very frank, "Bazan Kara ba,,." Maryam ta fada Tana kuka, ahankali Salima ta Dora hannu kan face dinta ta goge mata hawaye Tana cewa "Ki bar kuka haka nan kinji kou?.." Ta daga mata Kai, "Nidai in da San samu nane kije ki bawa Maman suhail hakuri..." Bata karasa ba Maryam tayi saurin girgiza Kai Tana cewa "Noooo...Wallahi she will beat me...dazun ma da kyar na tsira...Wallahi anty saboda ita bazan iya kasancewa da suhail ba...kawai zanyi hakuri dashi anty...you need to hear irin zagin da tayiwa late mother Dina....gaskiya anty na hakura..." Ta fada hawaye na fita daga idanuwanta, salima shuru tayi not knowing what to say Don har ha Allah batason tayi statement da zaiyi kaman Tana sukan uwar gidanta, Anty tace na lalata mata da...tace bani da zuciya wai suhail ya kawo matar aure amma ban rabu dashi ba...anty Wallahi inason suhail..amma bani da uwa kuma bazan iya kasance da Wanda mom dinshi bata kauna ta ba..." Ta fada still crying, ahankali Salima ta Dora kanta kan shoulder dinta Sannan tace "Kiyi hakuri...nasan suhail na sonki...duk hukuncin da zaki yanke ki dinga tunawa da halin da zai shiga..." Salima ta fada Tana Shafa kanta "Wallahi banason ya Kara Shan wahala kaman yanda yasha kanki amma kuma bana baki shawarar auren Wanda uwarshi batason ki...uwa dabance..." Salima, Ta fada mata, Kai Maryam ta Dora kan kafarta Tana lumshe idanuwa Sannan ta tunani "Anty I think kawai zan samu wani in aura...bazan iya auren Salman ba..,attitude dinshi is something else..." Ta fadawa Salima, "Hmmm Ni daman banason Salman...ni Wallahi in da saki yarda Dana hada ki da wani kanina...yana da kirki sosai...kuma daman matar aure yake néma..." Salima ta fada mata, shuru Maryam tayi without saying a word, "Ko baki so?.." Salima ta tambayeta, ahankali tace "Anty I don't really know,,,Wallahi kawai dad Dina né ya matsa min amma ni ko nan da shekara goma ban sa niyyar aure...yace in ban Fiddo Wanda zan aura ba da kanshi zai zaba min ...ni kuma Wallahi nasan za'a samu matsala in har aka bani wani Wanda ban sani ba...anty zan iya kashe Kaina". Ta fada cike da bakin ciki, kanta Salima ta Shafa Tana cewa "Dear sai hakuri...irin wannan auren ma ya fi dadi...zakiyi ta yanda kikeso har Allah yasa ki fara sonshi..." Salima ta fada Tana dariya, da sauri Maryam ta daga Kai Tana cewa "Over my dead body...anty ni fa I can't let the man I hate touch my fingers balle hannuna har yazo ga jikina...gaskiya anty ba Iyawa...I just can't,.." Ta fada atakaice, dariya salima tayi Tana cewa "Kin bani dariya...irin ku né da anyi aure ko wata ba'a yi sai ciki...duk cikin kiyayyar zaki bashi had in Kai...ke dai sai indai babu rabo tsananin ka da mutum amma Wallahi in da rabo komin kiyayyar dake tsakanin ku sai kun jone...." Salima ta fada mata sounding frank, "Kam...Ina...nidai anty ki tayani adua Allah ya bani wani Mai Hali da kyau kaman suhail...Yanzu saura wata shida Inyi aure..." Dariya Salima ta sake yi Tana cewa "Har kin San nan da six months zakiyi aure?.." Ta fada mata, "Eh mana anty...daddyna yace Ina cika shekara ashirin zanyi aure...kuma Wallahi he doesn't go back on his words...nasan dole yayi min aure..." Kallon mamaki Salima ta dingayi mata Don tunda suke bata taba yin personal hira daita ba balle tasa ko ita wacece, kawai dai alhaji ya bata amana kuma Ta amsa batare da ta nemi Jin ko yar wacece ko daga Ina take ba, "Wai Dan Allah kiyi hakuri zanyi maki wata tambaya...wai Ina babanki yake?.." Ta tambayeta, Dan murmushi Maryam ta saki da swollen eyes dinta Sannan tace "Yana USA" Ta amsa mata Don she don't feel like hiding anything from her anymore, tasan she won't do anything to jeopardize her security, "Kasar waje babanki yake?.." Salima ta tambayeta sounding so surprised, "Eh mana...Nima chan na tashi..." Da sauri Salima tace "Haba,,ai biri yayi Kama da mutum...Ashe shiyasa kike wasu abubuwan...haba sai Yanzu na gane...Allah sarki...mom dinki fa?" Ta tambayeta, "Mamana ta rasu...tun Ina yar yarinya...wajen babana nashi...he's my mentor and everything..." "Allah sarki...Allah ya jikanta...aiki babanki yake a chan?.." T tambayeta "Eh...babana alhaji Mahmoud shugaba..." Da sauri Salima ta mike Ta tsaye Tana cewa "Kina nufin kece yar shi daya da ake cewa ya mallaka?...ya ma sunanta?.." Salima ta fada sounding so out of words, "Maryama..." Maryam ta fada mata, "Eh Maryam...Ashe saboda ke ya biya mana hajji da umrah....ya ilahi..." Salima ta fada idanuwanta duk waje daga inda take tsaye Tana kallon Maryam kaman she's just seeing her for the very first time, "Anty Dan Allah ki dawo ki zauna...you're making me feel uncomfortable..." Ta fada Don batason yanda Salima ta saki baki Tana kallon ta kaman mirror, "Ina zan zauna Ina zaune da manyan kasa ban sani ba!!! Ya zaayi in zauna?.. Dan Allah tunda kike na Taba munana maki?.." Salima ta tambayeta sounding so confused, Dan dariya Maryam ta saki Sannan ta mike ta kamata suka koma suka zauna Tana cewa "Anty baki taba yi min komai na bacin rai ba...kin kula Dani tamkar kinsan koni wacece...anty kece first adult woman da nake hira daita da nake Jin dadi da kuma take bani shawara...kuma pls kar ki bar bani shawara..Ina Jin dadinsu..." Maryam ta fada, Salima kallon ta kawai take bakinta bude "Amma anty baban gidan nan is a nice person...yasan darajan amana da alkawari...Ina mamakin yanda akayi bai fadawa kowa ko ni wacece ba...har ke da kike his amarya...gaskiya ya cika Muslim na gaske Wanda ake alfahari dasu..." Idanuwa Salima ta lumshe tare da sakin ajiyan zuciya tace "Ai in dai amana aka bashi kuma ya cika Muslim bazai Taba ci ba...ai ance cin amana da karya alkawari alamomine na munafuki...kuma ko min kankantar amana sai ta Hana mutum sukuni ranar gobe kiyama...gaskiya nidai da hankalina bazan ci amana ba...ba a haifi Wanda zaisa inci amana ba...shiyasa in naga kina wasu abubuwan yana damuna saboda ke amana ce wajena...duk abinda kikayi sai ya shafeni tunda naji na dauka.." "Anty ai naji dadin zama dake...gaskiya anty kinyi..kina da Hali masu kyau...kina shiga damuwa in ni na shiga damuwa dukda bakisan ni ba...gaskiya anty masu halinki babu yawa...nagode..." Bata karasa ba Salima ta rufe mata baki. "Dan Allah ki bar barin inajinn kunya...wane kin gode....ke da muke rawa da bazarki?.. Dan Allah kiyi hakuri ranar nan da kika bini Kofar dakina na Kulle na bar ki wajen kina kuka".." Dariya Maryam ta saki Tana cewa Anty kin iya bada dariya..." Ta fada mata Tana kama hannunta, "Hmmm ba zaki gane bane..zuciya ta har bugawa take da karfi...Allah duk jikina yana rawa...ba kullum kake sanin cewa kana tare da Maryama shugaba ba..." Ta fada idanuwanta duk waje, dariya Maryam ta saki Tana massaging hannun Salima ahankali, ,"pls in sake tamabayan ki?" Inji salima "Komai ma..." "Ina dangin mom dinki suke..." "Suna maiduguri...su kuma dangin dad Dina suna sokoto..." Ta amsa mata, "Ya akayi baki zauna da su ba?.." Dan ajiyan zuciya Maryam ta saki Sannan tace "Family din dad Dina are not nice to us...they hate him for Allah knows why...da akwai lokacin da muka zo da dad ..wani wanshi yace he will take me out...muna fita ya sayo Nono da yawa ya saka sugar Sannan muka je wani joint ya sayi fish pepper soup yace inci..." Bata karasa ba Salima ta zaro idanuwa tare dacewa "Nono da kifi?.. Yanason kasheki kenan..." Ta fada sounding so tensed, "Hmm. Anty Ni ban San it's a poison ba..kawai Allah né ya kaddara da akwai sauran numfashina but I suffered...da dad ya tambayeshi sai yace ai bai San it's a poison ba...shi kawai yasan mu tashin turai da akwai mu da cin dadi..." "Kam ya Raina maku hankali...gaskiyar bai kyuatawa kanshi ba...ai na gaba yayi gaba na baya sai labari...su kuma dangin mom dinki fa?.. Suma haka suke?.." Da sauri Maryam ta girgiza Kai Tana cewa "Suna sona over...kawai dad na Jin haushin wai zasu sangartani...that's why bai son Ina zuwa Sannan yace bai son family dinshi su san Ina Nigeria...that's why yayi choosing baban nan gidan in zauna dashi..." Ta fada ahankali, Idanuwa Salima ta lumshe taking in all what she have said, "Amma gaskiya nayi bakinciki halin da Maman suhail take nuna maki...ke tamkar allurace cikin teku..Mai rabo zai aureki...gashi suhail yaci saa ya samu zuciyarki amma mahaifiyarshi taja mashi...Kai Sam banji dadi ba..." Salima ta fada cikin sanyinmurya, "Anty maganar gaskiya Ina Kaunar suhail...da farko babu Wanda na tsana