← Book details Wulakanci Dodone complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 190

Sashe 81

Wulakanci Dodone complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kasaita ta taka zuwa part dinshi, duk inda tabi kamshin perfume dinta kawai ke tashi, bata ko Shafa powder ba amma Her face is glowing, Tana zuwa ta bude Kofar without knocking, suhail dake kwance kan kujera a falo bai saga Kai ba Don he can smell her from distance, daure face tayi tare da rufe Kofar da karfi amma still bai bude idanuwa ba, tsayawa tayi Tana kallon face dinshi sai taga kaman ya Kara rame wa, suhail najin shurun yayi yawa ya Dan bude idanuwa sai suka hade Ido, daure face yayi tamau itama ta daure nata, rasa abinda zata ce mashi tayi, "Dazun Kai ka dauki laptop Dina?.." Ta dada kaman an fixgo maganar daga bakinta, a I irin irritating look ya watsa mata Sannan ya juya without saying a word, kallon daure mata Kai yayi Don she doesn't understand why yake yi mata irin wannan kallon ba Don tamkar yaga kashi yakeyi, tsoki taja Sannan tace "From today don't touch anything I didn't ask you to touch...kar ka sake taba min Kaya balle kayi invading privacy Dina...am warning you, " Ta fada cikin matsanacin fad'a, sake juyowa suhail yayi ya sake watsa mata kallon tsana from head to toe Sannan ya ya dauke kanshi, nufo shi tayi Tana cewa "Wane irin kallo né wannan...kana kallo na kaman kaga what class Dinka...am not your type so don't look at me as if I am..." Ta fada Tana nuna shi sa yatsa, murmushin takaici suhail ya saki Sannan yace "Daman you are not my type..and you will never be...am 29 and will be 30 in next few months but am intact..." Ya fada sounding proud, word dinshi yasa Maryam yin shuru because she have heard such word daga wajen mr i love you, na he's 29 and will be 30, Sannan word dinshi na intact got her thinking, "Meye maanar hakan?.." Ta tambayeshi Tana kallon yanda yake cika yana btsewa, banza yaji daita, "I said what is the meaning of your last statement?." Ta fada kaman sabon shigar mahaukaciya, mikewa yayi ya saka takalmin shi yana cewa "Oho....ki shafa kiji..." Ya fada Sannan ya juya ya barta nan tsaye, afusace tace "Don't you dare walk out of me...come back right now..." Tayi commanding dinshi, kaman hungry lion ya juyo ya fixgota har turban dake kanta ya fadi kasa, kamar wata kaza ya jata bakin Kofar ya sa free hand dinshi ya bude Kofar Sannan ya wurgar da ita waje, Sauran kadan ta fad'i kasa, da sauri ta gyara tsayuwarta tare da juyawa to make sure no body is watching sannan ta sake bude Kofar da sauri ta shiga, already suhail ya shige bedroom, da sauri ta bi bayanshi Tana cewa "Nan gidan ubanka né da zakayi pushing Dina out?... Ni da gidan ubana and you pushed me out?.." Ta fada cikin tsananin harshness, suhail dake kwance kan kujera ya kalleta Sannan yace "Now I know why baki Jin shakkan fadawa mutum magana anyhow...Sannan ai ba daga bola na zo nan ba....am also a prince in my own house...if I annoy you so much then tell you zillionaire father to take me back..." "not until am done with you..." Ta fada cikin Ihu, Kara mikewa suhail yayi ya sake fixgota ya kaita bakin kofa, "Don't touch me with your stinking hands..." Ta fada Tana duka shi da free hand dinta, kaman feather ya bude kofar ya turata waje Sannan yace "Stay out of my way...in ba haka ba ko ubanki bai Hana abinda zanyi maki...sai dai a mutu duka...a word is enough for the wise..." Ya fada sannan yayi banging Kofar tare da kulle wa. Idanuwa Maryam ta zaro not believing what she just witnessed, yanda yayi mata magana tasan da gaske yake Don babu zance wasa in his statement, why is he so harsh, da sauri ta buga Kofar da karfi Tana cewa "How dare you...wallahi sai nayi magani ka...ni da gidana and you're pushing me out with your filthy hands....you will regret this.." Ta fada sounding so angry, juyawa tayi Tana tafiya kaman zata tashi sama, Tana zuwa falo ta tarda dad dinta, kallo daya yayi mata ya gane she's disturbed, "What's wrong with you my princess?.." Ya tambayeta amma bata amsa ba ta wuce upstairs da gudu, Tana shiga dakinta ta zauna bakin gado Tana sauke ajiyan zuciya, wani irin haushi take ji Wanda batasan na meye ba, she feels like strangling him to death, "I hate you " Ta fada da karfi kaman yana dakin, Tana cikin sauke ajiyan zuciya sai ta fashe da kukan da batasan dalili, "I hate a billion times..." Ta sake fada cikin kuka, Tana nan zaune har lokacin sallah, mikewa tayi ta shiga bathroom ta fito da alwallah tayi sallah Sannan ta kwanta. Shima suhail yana kwance bayan sallah magrub aka shigo aka shaida mashi dinner at 7pm, banza yayi da baturiya sai da ta fita Sannan yace "Sai dai kuci kanku...." Ya fada yana juya kwanciyar shi, alhaji Mahmoud da Maryam sun fito dinner amma Banda suhail Wanda hakan yasa alhaji Mahmoud tambayan Maryam why itama tace bata sani ba Sannan ta Kara dacewa "Duk yau bai ci komai ba..." Ta fada mashi Tana cin abincintq, kallon mamaki alhaji yayi mata tare dacewa "What's wrong with him..." "Nima ban sani ba..,.may be he's not hungry..." "Ban gane maybe he's not hungry ba..,me kika bashi ya ci.."Maryam Kurba lemo tayi Sannan tace "Ai dad har lunch nasa a Kai mashi but bai ci ba...haka aka maidoshi..." Ta fada sounding carefree, "Shine baki damu ki tambayeshi abinda ke damunshi ba?.." Inji alhaji Mahmoud, daga Kai yayi ya Kira wani saurayîn dake tsaye gefe daya da alaman bodyguard dinshi né, saurayîn na zuwa ya shaida mashi yaje ya Kira suhail. Lokacin suhail na kwance babu abinda yake tunawa sai pictures da yagani, kawai yana tunanin how she will be on be, da kuma yanda zata dinga acting during sex, ji yayi kaman ya hadiye zuciya ya mutu saboda bakin ciki, yana cikin wannan tunanin yaji Ana cewa alhaji Mahmoud yana kiran shi, kaman baiso ya mike ya saka shoes ya fita, duk jikinshi look so weak, amma he's ace looks strong and stunning. Yana zuwa part din ya tarda Maryam da dad dinta zaune kan dining "Son why bakayi joining din mu a dinner ba?... " Alhaji Mahmoud ya tambayeshi sounding so concerned, Dan murmushi suhail ya saki Sannan yace "Bana Jin yunwa né..." Ya fada with respect, kallon Maryam alhaji yayi Sannan ya kalli suhail before saying "But tace duk yau bakaci komai ba..." Ya fada mashi, Dan murmushi suhail ya sake saki Sannan yace "Bani da apetite ne...." "am sorry...ko dai bakason abincin né..." Inji alhaji Mahmoud, da sauri suhail ya girgiza Kai tare dacewa "No sir...kawai..." Bai idaba alhaji Mahmoud ya kalli guy dayasa ya Kira suhail yace mashi "Bring one of the car keys and take him out...take him to nice restaurant around..." Da sauri Maryam ta daga Kai ta kalleshi Sannan ta kalli dad dinta, "Daddy cewa yayi he's not hungry..." Kallon ta alhaji Mahmoud yayi tare dacewa "Kin taba ganin inda mutum bai ci komb a kuma he's not hungry?.." Ya tambayeshi, suhail na tsaye kanshi kasa sai murmushi kawai yake dukda yasan ko ya fita ba zai iya cin komai ba because he's mad to the core, Maryam sake kallon suhail tayi ta watsa mashi kallon haushi sannan ta kalli dad dinta tare dacewa "Ai dad yace he's not hungry...maybe he has been eating something without my..." Bata idaba alhaji Mahmoud yace "Turanci kike kou?.." Da sauri Maryam tace "Aa..." Suhail kallon ta yayi "Daddy kilan yana cin abinci..." "Yana cin abinci kuma kikace duk yau bai ci komai ba?... Ai ke kikace duk yau bai ci komai ba..." Inji alhaji, suhail kallon ta yayi yana mamakin statement din alhaji Mahmoud, wata ita ta damu da rashin cin abinci shi, ita kuma Maryam ji tayi kunya ya kamata saboda abinda dad dinta ya fada, bataso ya fadi hakan ba, guy din né ya dawo da keys, "And pls get him a phone.." Alhaji Mahmoud ya fada yana mika mashi credit card, Maryam ji tayi kaman ta mutu saboda takaici "Thanks sir..." Inji suhail, da sauri alhaji Mahmoud ya daga mashi hannu yana cewa "Babu godiya tsakanina da Kai..babanka ya kula da my daughter so Nima ya zama dole in kula da Kai...so have fun...and gobe zan sa a ajiye maka keys In Case kana son fita..." Bai idaba Maryam ta tashi fuuuu kaman zata tashi sama ta bar dining room din, bayanta suhail yabi da kallo tare da tabe bak, alhaji Mahmoud kallon ta yayi ya kalli suhail tare dacewa "I don't know what's wrong with her this days...she acting weird...," Inji alhaji Mahmoud, murmushi kawai suhail ya saki tare dacewa "Should I talk to her?..." Ya tambayeshi calmly, gira daya alhaji Mahmoud ya daga Sannan yace "Ai kaman she talks to you more than she talk to me this days..." "No way..." Suhail ya fada cikin ranshi Sannan yace "I will be back.." Ya fada tare da bin bayan, suhail yana mamakin halin alhaji Mahmoud, zama da shi for just a day ya ko ya mashi abubuwa da dama, yasan cewa ba kudi ke sa wasu jiji da kansu ba sai Don a jininsu yake, he remembered he's own attitude and yasan cewa abunda yakeyi a baya bai dace da shi ba, ko ba komai he have Maryam to Thank for opening his eyes, yasan he can't wait ya koma gida Don ya bawa mutane da yakewa Wulakanci hakuri...he has learnt his lesson duk da daima jininshi yake amma he will control himself, yana zuwa ya bude dakinta sai yaga bata cikin, bedroom ya shiga yaga still bata nan' face Dinshi daure ya Kama hanyar bathroom ya kanga kunne yaji shuru, fita yayi har sai sauka sai kuma ya koma ya fara bin dakuna, sai Yanzu ya gane they all belong to her sai dai ko wanne da irin design din Kayan ciki' yana daf da zuwa da biyar yaji kukanta, kofa ya bude ya shiga tayi saurin daga Kai, "Kai kana da nerves,...after everything da kayi min still ka zo gidana kana
Chapter 81 · 0% Book details