Sashe 98
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
zahra Allah ba zan fadawa kowa ba tundama har kinsan inda yake ai dama hankalinane ya tashi da zancen batan da akace yayi wai an masa kurciya ya bar gari. Don Allah dai na rokeki hanne kada ki kuskura ki furta wani abu har ace nina fadi kinsan Abban mu zaiji zan kuma shiga cikin matsala ke kin sani. Tace wallahi na fada maki banyin zancen nan da kowa idan Allah ya dawo dashi ai zai nemi wanda ya bata mashi sunan aji ta fada. Nikan muna gama waya da hanne din nayi ta tirayin din layin shi baya shiga amma hakan bai dameni ba daga nan na fita zuwa kitchen na samu mutane mukayi ta hira har ma na manta da zancen. Don ban dauki zancen da ma,ana ba a zuciyana haka yasa banji komai ba a lokacin kan zancen har zuwa lokacin dana daidaici cewa mutanen gidan sun kusa dawowa na shige daki daga sunan sallah ban sake fitowa ba nayi wanka na fito nayi sallah na sake komawa na kwanta. Sai shida na fito gaida mommy don nasan ta dawo gida a lokacin saidai ashe shigowan ta ke nan gidan wai ta biya wurin tellan data bawa dinkunan buki ta karbo. Tana zaune a falo sai gani na fito da fara,a a fuskanta ta na karasa wurinta ina mata sannu da zuwa tace come come my daughter yanzun nake zancen in tura a kiraki. Kizo ki gwada kayan nan ko zasuyi sizes din ki don kwatancen ki kawai nayi mashi ya dinka maki duk da naso yazo ya ganeki ko kije amma yace aiki yayi masu yawa sosai. Na karasa zama ta miko min leda da kaya a ciki na dadu dasu sunsha guga na karba ina fadin thanks mom haba dai gwada mu gani ko zasuyi maki idan ba matsala ga dinkin. Karba nayi na fara budewa tace yawa kinga wanan shine za a saka ranan kamu namu ankone na gidan ango wanan din. Abu na farko dana fara dubawa shine dinkin bujen don ban saka bujen daya matseni sosai don haka Allah yayini ni bana son kaya su matseni tam a jikina sai in koma ban walwala ko sakewa karshe ma saidai in kyautar da kayan. Naji dadin ganin akwai space a dinkin tellan koda ya matse zan iya budeshi haka nayi ta dagasu har kala biyar tana min bayanin kayan da ranan da za a sakasu din. Bayan na gama ganine na hada a wuri daya na mike daga inda nake zaune na durkusa a gabanta ina fadin mommy na gode tare da dan fadawa saman jikinta ta dafa min baya tana fadin haba haba dai ki bari don Allah zahra . Kkme nayi maki kin cancanci hakan gareni tunda kun yaba dani har kuma kun yarda da zamana a cikin ku ba tare da nuna min hassada ba ko kishi don me nima zan gaza daku yanzu. Shigowan Abba yasa na mike da kayan a hannuna bayan na gaidashi na shige ciki ina tunanen irin hakin mommy dana kasa fassara manufabta a kaina yanzu. Daki na shiga na fara gwada kayan a jikina gaskiya kayan ba laifi ba dinkin ba ba kayan da akaiwa design din ba duk ko wani abin a yabane. Tunane yazo min bayan na gama ganin kayan shin me wanan matar take nufi dani hakane abinda ban yarda dashi ba shine dole akwai manufa ga zuciyan wanan matar a kaina. Saidai ban gane me take nufi ba take min hakan dole dai nasan akwaishi amma zan bita a hankaki har in gano hakan inda na godewa Allah shine banda rawan kai da zai hanani gane hakan da take min din. Gashi ga lissafina saura kwana biyu mu wuce zuwa kano kamar yadda ta fada min a baya dole gobe in bayar da kayan da zantafi dasu a kara wanke min a goge hakan yasa na lalubo wayana na kira ummah ina fada mata komai daya faru. Ki dai kula da kyau kuma ki natsu ki kula da kanki banda rawan kai Allah ya tsare tunda ba yadda zamuyi don Alh ya tsaya mata nan kuma suna ganin kamar wani munafuncine na kulla ga yin hakan. A sanyayyena amsa da toh ummah in sha Allah zanyi yadda kikace min din muka dauko hiran kanne da ita har ta basu wayan na gaisa dasu din . Saidai na yanke a raina muna dawowa zan koma gida don nagaji da zaman Abujan ba yan uwana da mahaifiyan mu a kusa saboda hakane nake zama a takure gashi ba wani sabawa nayi da mommy din ba sosai kamar yadda na saba da mama a baya.