Sashe 24
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zan iya cewa wanan lokacin na gane sauyin da gidan mu ke ciki a yadda ni na daukeshi ashe ba haka abin yake ba a dunkule a baiyanene nake ganin komai normal a gidan namu. Wata kila kuma watan hankalinane ya kama a lokacin har yakai ga na fahinci hakan a yanzu sabanin da da dauka daya nakewa iyayyen namu a zuciyana. Yanzu na gane kowa danshi ya sani kuma yake kokarin ganin ya zama wani abu a duniya ya kareshi daga duk wani sherin kada ya cin mai. Saidai wani abu da bai sauya ba shine yaran mama maza manya da suke daukan ummah da matsayi mai mutunci a idanun su basu fasa hakan ba don suna bugowa ummah waya kamar yadda suka saba a baya. Idan sunzo garin kuma zasu shigo su zauna a nan suyi hira duk da mama zatayi ta aikowa suzo tana neman su a wurin ta bai hana insun tafi su kara bullowa kafin dare kuma. Hakama alheri bai katsewa a tsakanin su da ummah din saidai nasan a boye sukeyin shi don yanzu sun fara aiki suna kuma kula da harkokin Abba haka yasa kudi ke shigo masu ta ko ina a yanzu. Saidai a garemu yanzu babu daman kwatanta hakan ga mama don bamuga fuskan yin hakan ba gareta a yanzu babu wani sakin fuska ko kara na jan mu jikinta kamar yadda ummah kewa nata diyan. Sai gaisuwa kawai koshi saida kyat take karba muna a tsatsaye dole mukaja jikin mu da ita ya kannena idan sun ganta jikinsu har rawa yakeyi. Wanan satin ma kamar kullun sunzo gida don suna garin na fito da shirina zan tafi school a waje na samu ya musa wanda yaci sunan kakan mu shine da nabiyu ga mama. Yana tsaye a farfajiyan gidan mu da kayan motsa jikin a jikin shi wurin shi na nufa ina gaidashi ya juyo fuska a sake yana fadin . Sai ina haka yan matan mama da safen nan haka school na bashi amsa kafin na karaso inda yake tsaye murmushi nayi tare da fadin ya musa ai yanzun mama ta daina sona kamar da. Ido ya kwalo waje yana fadin garin yaya haka ya faru keda maman ki dan shagwabewa nayi ina fadin nima ban sani ba ya musa na daiga ta daina sona ta daina kulani a yanzu na fada kamar zanyi kuka. Kai haba dai baki dai jida kyauba zarah har yaushe keda mamanki zata daina sonki kuma nace Allah ko ya musa nima bansan abinda nayi mata ba yanzu har haka ya faru. Wa zai kaiki school din ya tambaya ta hanyar kawar da zancen da mukeyi nace nike zuwa da kaina yaya da wani mota kuma yana raba ido ga motocin dake parke a haraban gidan. Nace cikin dan sakin fuska ga motata can ita nake ja yanzu ina nuna mai motan dayasani na Aisha da tayi accident da ita kamar ma ba zata gyaru ba lokacin. What ya fada yana kwalo ido waje tare da fadin wanan tsohowar motar dai yanzu har an saura shiganta gidan nan ashe ? Kai haba yaya garau take fa da ita nake fita kuwani duk inda zan tafi na bashi amsa ido ya kura min a zahiri zaki iya cewa ni yake kallo a lokacin. Kafin na katse mai tunane da fadin zan tafi yaya kada in makara amma dai aiba yau zaka tafi ba ko kada in dawo in samu ka wuce. Yau kuwa yan mata don Abba na jirana akwai inda zai turani kilama yau din nan nabar kasan nan insha Allahu. Allah sarki ashe da banganka yanzu ba saidai na dawo na samu ka wuce ke nan yace gaskiya kan zan bar maki sako hannun ummah idan kin dawo sai ki karba . Nagode yaya Allah ya saka da Alherin sa kai tun bakiga sako ba har kike min godiya haka aiko baka bayarba kayi niya kuma na gode Allah tsare hanya yace amin . Na juya zuwa wurin motar ya bini d kallo har lokacin dana bude na shiga na fice daga gidan ina masa horn ya daga min hannu mukai sallama dashi. Ajiyan zuciya ya sauke kafin ya tura hannu cikin aljihunshi ya ciro wayanshi lamban ya jafar ya kira suna gaisa ya fara fadin wallahi akwai matsala fa idan bamu fadawa mama gaskiya ba ka wanan abinda takeyi a gida nan. Meya faru ya jafar din ya tambayeshi yace yaya za,ace kowa zai shiga jami,a gidan nan ana sai mashi mota amma yanzu yazo kan zarah ace sai tsohuwar motar Aisha za a bawa zarah motan da har accident tayi da ita amma ita zarah ke shiga yanzu. Au kai sai yanzun kasan da wanan zancen ashe nina dade da sanin hakan da akayi na nuna bacin raina ga hakan da akayi nayi magana mama tace ina ruwana koni aka ba. Nayi shiru badon raina yaso hakan ba at,list ya kama tunda wanan shine karo na farko da za aiwa ummah haka ya kamata ace an kyautata mata itama tunda anyi muna tana gidan bata nuna hassadanta ba ita. I don't no why mama take haka na rasa dalilin sauyawan mama a wanan lokacin haka gaba daya ita da yaran nan yanzu sun tsani mutanen nan yanzu a gidan mu. Kaidai bari kawai wanan zuwan da nayi last bakaji irin fadan da mama tayi min bane kan naje wurin ummah na zauna saida na tattara na bar garin cikin bacin rai. Gaskiya nikan ba za yarda da hakan ba zan mata nasiha kada son kai yasa mama ta halaka kanta Allah ya tambayeta hakan gobe kiyama. Wanan matar ta barsu ga Allah kan duk abinda suke mata kuma hakan bai isa ba sai an hanasu harda walwala a cikin gida haba don Allah abin yayi yawa mana. Ya kashe wayan tare da daga kai ya kalli kayon gidan namu yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda ya fara takawa zuwa cikin gidan kai tsaye. Yanzu Amadi haka zaka zauna ba wani sana,an da kakeyi da zai taimakaqa rayuwanmu mu samu muci a ciki har mu tufatar da kanmu ga hakan. Da ka dauki wanan uwar garken ka kaita kasuwa ka sayar sai ka nemi sa,an da dan kudi zai dinga shigo ma yau wajen kwana biyar fa munacin ganye a gidan nan. Dije nima hakan yana damuna ina nan ina ta neman aikin da zanyi inda zamu rika samun abinci yana shigo muna hakan yana damuna sosai a raina. Nasani Amadi nasan da hakan kadai ki shawaranane daka jaraba hakan an gani zaifi ya nisa yana fadin Dije banaki bane akuyan nan ita kenan muna a rayuwa ina gudun akaita kasuwa azo a tayata wullakance. Kinga kuma hakan ba dadi ai gara dai a bari har Allah ya kaimu sallah saina fitar da ita a hurhura da wata karama a sake saura kudin saina fara juyawa. Ikon Allah yanzu dan nan sallah da sai nan da wata shidda ga mai yawancin rai ka dauka ka kai kawai Allah na nan tare damu in sha Allah kafin sallahn yazo aika tara na tarawa har ka mayar da kudinta kuma. Zan gwada hakan Dije ya yunkura yana fadi ya nufi hanyar dakin shi yaja ya tsaya ya kafawa uwar garke dake kwance tana gyangyadi a inda turken su yake. Ya dan jima tsaye kamar yana nazarin akuyan kafin ya shige dakin shi bai jima a ciki ba ya fito ya sauya kayan jikin nasa lokacin Dije ya ambata daga kofan dakinta daya tsaya din. Ta amsa mai daga ciki yake fadin ni zan dan fita naga ko zan samu mai sayen akuyan cikin unguwa tunda sun santa ai daga haka bai jira ta fito ba yasa kai ya fice daga gidan koda ta fito yariga ya tafi. Yana fita ya tsaya a kofan gidan yana bin gidajen dake wurin da kallo kafin ya nufi gidan makwabcin su mai irin wanan sana,an na dabbobi ya sallama mashi. Babban danshine yafito ya sanar maida mahaifinsu bayana nan ai ya tafi cin kasuwan kauye hakan yasa ya juya zuwa gidan wani can kasan layinsu. Shima haka yana kasuwa bai dawoba ya dawo kofan gidan malam Tanimu da ba kowa sai tarin gumaguman icce dake zube a kofa gidan da wanda aka faskara ya zauna shi kadai kamar yana jiran wani a wurin sai bin masu wucewa da kallo yakeyi. Yayi nisa a tunane yaji ana mashi sallama ya amsa yana dago kai ga maishi wani dattijone a tsaye ya rataya buhu a kafadan shi da ganin shi kamar mata fiyi bayan sun gaisane yake tambayanshi malam tanimu yace. Cikin ladabi nima ban san inda ya nufa ba baba zamana ke nan wurin nan yanzun nima ban wani dade ba sai mutumin yace kai gashi ko ina son ganin shi wallahi wai dama dabba nashigo saye yai min jagora. Yana fadi yana kaiwa zaune Amadi yace gashi ko da alama kamar yaje daji daukan icce ne don in yana gari bai faye zuwa wani wuri ba dai. Shiru dattijon tayi kamar yana nazari kafin Amadi ya mike tsaye yana fadin bari na shiga ciki a amsa maka ruwa da dan farafarau ka kora don alama ya nuna yanzu ka shigo. Yana fadin hakan ya mike bai jira jin tsohon ba ya shige cikin gidan malam Tanimu din bai dade ba ya fito da ruwan randa mai sanyi an surka da kunu anyi farau farau dashi a kofi mai marfi. Dattijon ya karba yana saka mashi albarka tare da mai fatan alheri yana fadin nagode nagode yadda ka tareni kaga tarbon arziki kaima a rayuwan ka har duniya ta nade. Shima godiya yayi yana fadin amin baba nagode nagode kwarai baba ya fada yana kaiwa kasa muryan dattijun ne ke fadin. Yaro kasan inda zan samu yar akuya ita nazo nema da yamman nan na dauka zan samu malam tanimu mu hada kafa muje tare. Kallon mamaki yaiwa dattijo saidai fuskan dattijon na kallon wani wuri a lokacin yayi karfin halin fadi a cikin mamaki aiko baba akwai akuya da akai niyar sayarwa dama barin shiga inwa maishi magana sai a fito dashi ka gani in zai maka. Ya mike zuwa gidan su bai jima ba sai gashi jaye