Sashe 124
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya musa ne a gaban Abba zaune matarshi tana gefe daya zaune bayan sun gaisa ya kalli Abban yana fadin yau zamubi jirgin sha biyu zuwa sokoto na buga waya a turo mota azo a daukemu. Kaidawa ke nan naga jafar ya tafi tun jiya dani da zahra zan mayar da ita gidane ya fada kai tsaye ba tare da jin komai ba. Abban ya kalli hjy karima din yana fadin har ta gama hutun ke nan zata koma kafin tayi magana ya Musa din yace eh zata koma don next monday zasu shiga school. Abba ya kara kallon hjy karima din sai cewa tayi amma ai naga bashi ya daukota ba ya kamata ko in san cewa zata koma in mata shirin da zan mata din a bangarena. No ku barshi ba sai kun mata wani shiri ba ai ya mike yana fada fuska daure tare da fadin yau din zan mayar da ita gida na fada mata ta shirya ko. Shiru sukayi ba wanda yai magana a cikin su saida ya fice take fadin abinda yaron kan nan ke mun bana son shi ina ruwanshi da zahra tunda ba wurin shi tazo ba. Amma ai kinsan halin musa tunda yace zai mayar da ita gida yau ba fashi ke nan ki kyalesu ya mayar da ita din tunda sun kitsa hakan a tsakanin su. Duk ina labe ina jin abinda suke fadi a lokacin hakan yasa na koma nayi kamar ban san da zancen tafiyan ba sai gata tashigo min dakin a fusace ta sameni nayi kwance ina karatun wani littafina. Ta turo kofan a fusace tana fadin Zahra wai me haka ke nufi ne nifa da alheri na daukoki ba don sheri ba amma naga ana son a munafunce ni kuma ? Na dan kalleta cikon mamaki ina fadin Mommy meya faru tace naji wai yau din nan zaki koma gida yayan ki na fadawa Abban ku nace yau mommy ? Kamar ban san da zancen ba ina dan dagowa ehmana yanzu yake fadawa Abban ku hakan nace gashi ban ko shirya ba ban hada kayana ba ai. Au kema baki san da zancen tafiyan bane ko me na girgiza kai tace shirmen banza toba inda zaki don naga shi a gadarance yake abinsa ni ba irin iyayyen sa bane don ya sani. Nace a a mommy ki bari in tafi tunda yace hakan ina jin tsoron ya musa sosao kada yai min fada kawai na tashi na fara hada kayana dake watse a cikon dakin da sauri . Ta tsaya tana min kallon mamaki kafinta juya ta fice a fusace kamar yadda ta shigo dakin da farko a hasale na kara hada kayana wanan ne silar barina abuja a ranan sai ganin mu kwatsam akayi mun dawo gusau baki a laikum. Ga ya musa yasa Abba ya bada kudin da za a sai mun tsaraba Abban ya bashi shi kuma ya miko min su duk da muka bar gidan ya biya dani wani tsore nayi sayayya sosai a store din. Ummah tayi mamakin ganina tunda na shigo ban zauna ba na nufi part din mama na gaida ita mun gaisa sama sama tayi min an dawo lafiya na fito. Nan ta fara sake magana cewa ai ido ta saka muna dagani har ummah ita zamuyiwa munafucin mu nuna muna tare da amarya don a hade mata kai aga bayanta a gari ko ? Kai haba mama yarinyar da Abba ya tilastawa da zuwa Abuja dole wai a can yanzu zata rika hutu don kawai an mata sherin cewa wani saurayi na zuwa wurin ta suma fa bada son ransu bane tatafi abujan hutu. Aiba sheri bane don nina fadawa Alh komai na sanar dashi kada yaji yace an munafuceshi daga baya don tana ganin yaron da zubin fulani take wani dagawa mutane kai don rainin wayau. Haba mama hakan ai bai dace ba tunda abinda takeso shi za a bata ta aura ai don baida kudi ai ita ta ganshi tace tana sonsa sai a barta da abinta ta aura. Nima saidana fada maki mama ki kyalesu suyi abinsu ba ruwanki ba ita zata sha wuyanta ba ita kadai ina ruwan wani ya musa din ya dan harari Aishan yace . Shi auren ne wuya ko auren wanda baida zarahi haramun ne akace ai shike nan taje ta aureshi din meya damu maimuna mama din ta fada sai ya jafar yace shine ai mama ki kyalesu please tunda tace shi take so. Bayan fitan diya mazan daga gidan suka zauna nan da Aisha suna magana suna dariya tace ai barsu na fisu iskanci zasu raina kansu daga ita har uwar nata. Ba mayana zai shigo wani sati ba ku fadawa masu neman ku cewa suzo suga Alh din nasan idan ya matsesu babu wani shi zasu fitar hakana din ai kinga ta fita zakka a cikin ku ke nan. Shina so ki gane tuntuni mama baki gane hakan ba ai wanan zaifi masu zafi da ciwo ace kowan mu ya auri abin kwarai ita ko ta buge ga wanan tallakan karshe. Kai Allah ya rabamu da kishiyar uwa mara imani macen da bata kaunan ganin diyan kishiyanta su karu da alheri ko wani iri amin. Nikan tunda na shiga dakina na fara gyara duk da baida wani datti a cikinsa na gama komai nayi wanka na dawo na kwanta ina tunanem irin makircin mommy da abubuwan da suka faru a tsakanin mu a tafiyana. Tare dashi akai sallah asuba don haka wasu suka sanda dawowan shi garin sai binshi mutane keyi da kallon mamaki har ya koma gida duk yana kule da hakan da mutane keyi mashi. Kwanciya yayi don yana tare da gajiya sosai lokacin barci ya dan fara diban shine yaji muryan malam Tanimu da labarin dawowanshi ya sama ya garzayo ya ji labarin komai daga bakin shi kafin wani ya bashi labarin yadda akayi. Sama sama ya dinga jiyo sallamanshi kafin yaji muryan Dije ta fito suna gaisawa dashi yaji yana fadin ace Amadi ya dawo shina niishigo taro nai. Badai lahiya ya iso ba ya yunkura a lokacin zai tashi yaji amsan da Dijen ta bashi yasa ya koma ya kwanta yana sauraren su dije din na fadin . Allah ya dawo dashi lahiya kasan dan yanzu da wayau shi yana wurin neman shi ana nan ana masa sheri da kazzalaha a cikin gari har wanda baka zata da zai maka sheri ba sai kaji mugun zance da mugun nufi a bakin shi. Hakane kan Dije kesan in abu yazo sai mutum ya dinga tunane har ya fita cikin lissafinai adaiyi hakkuri abinda ya wuce a barshi ya wuce a yafewa juna tunda ana tare wuri daya. Shikan amma abin ne da mamaki wai wanda ka dauka jigo shikama zagon kasa a boye yana hwadin maganan da bai dace ba a kanka dolena rai ya baci. Yanzu dai kiyi hakkuri ina shi Amadin yake shina zaka in gaisai in ya tashi ina hwada mashi ka shigo naji ya koma ya kwanta dazun don hakane malam tanimu din bai samu ganin Amadin ba wanda baiso hakan ba a lokacin. Sai bayan tafiyan shi an dan dade ya fito ya samu dije zaune bakin murhunta tana hasa wuta suka gaisa yake fadin yaji muryan malam tanimune ai. Bar munafukin banza da wofi watau yaji labarin dawowankana shina ya taho ya samu na karaswa aini malam Tanimu ya bani kunya a garin nan . Wai ace shi da kansa ke yawon bata muna suna yana aibanta maka sana ,anka da wani manufanai watau dama ashe dariyan hakori da jinine a tsakanin mu dashiya. Saida haka ya kasance na gane masoyan mu na gaskiya da wa yanda basu son mu da alheri a garin nan kai Amadi naga abu a cikin garin nan bayan tafiyan ka nan ta dan bashi labarin irin abubuwn da suka faru shidai murmushi yayi kawai bai samu abin fadi ba lokacin. Can ya mike ya shiga dakin dije din ya kwaso kayan daya shiga dashi jiya cikin dare nan ya dinga fitarwa yana mata bayanin komai a tsanake. Ya kwashe ya mayar daki Dije sai faman saka mai albarka da takeyi tana mashi adduan gamawa da duniya lafiya yana amsawa son shi kadai yasan abinda yake ji a zuciyarshi lokacin kan komai. Dakinshi ya nufa duk da ba wani kayan kirki a ciki hakaya gyara ya kakabe dan kuran dake ciki saida ya fitar da komai ya kakabe ya mayar ya koma gyaran gida ya gyara ko ina don duk gidan ya yamutse kamar ba wani mahalukin dake rayuwa a cikin gidan. Hakama dabbonin duk sun rame da alaman basu samun kiwon daya dace a bayanshi nan ma ya gyaro ya zuba masu dan abincin daya gani a wurin. Yana kule da kallon da uwar garke ke mashi tun safe amma addua ni a zuciyan shi sam bai nuna ya gane hakan ba gareta saima nunawan da yayi bai damu da itaba.. Baiyi aune ba yaji takai mai irin tunkudan data taba mai a baya a mambilla hakan yasashi juyowa gareta yana dan tsura mata ido na dan lokaci kafin ya mika mata sauran abincin daya rage a hannun shi din. Daga haka ya juya ya bar wurun bai sake juyowa inda dabbobin suke ba ruwa ya diba ya watsa a jikin shi ya fito ya shige dakin shi ya shirya lokacin ya nufi dakin Dije don ya karya. Bayan ya zauna ya fara cin abincin ne ya dago yace mata kinji labarin Rashida dacewa mahaifiyarshi don haka yake kiranta da sunanta. Mamaki Dije taji jin ya tambayeta mahaifiyar nasa da bai damu da yin hakan ba garesu tace dashi ta bugo waya tana tafe don an kirata an sheda mata batan ka . Wai mijin natane maciji ya taba ashe muka jisu kwana biyun nan shiru amma tace da sauki yanzu zata zo nan bada dadewa ba idan ta samu sararin hakan. Allah ya kyauta yace da ita yaci gaba da cin abincin shi yana nazari kafin ya sake dago kai yana fadin lokacin da ta rabu da mahaifina ina da shekara nawa ne Dije ? Kai Dije ta dago tana mashi kallon mamaki kafin tace dashi missa ka faye