Sashe 89
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
fita bai dade ba ya sake shigowa yace wai ance ina yaje dan nan ina zan sani ina nan zaune ta fada da alaman fada. Ta zata zai dawo a lokacin saidai shiru bataji dawowan yaron gidan ba kuma sai yamma ta fito kayan data gani a jingine cikin buhu ajeyine ta tsaya tana kallo a cikin mamaki. Kafin tace yanzu meye wanan Amadi ya aje min nan kuma ta nufi wurin kayan tana duba cikin mamaki takai hannunta taushi taji hakan yasa tayi zaton kayan gwajon shine ya aje a wurin ya manta kafin ya fita. Abinda zataci ta fita nema a waje ta sayo tuwo da miyan taushe irin na sayarwa da ake samu a layi ta sayo don taci don ba zata girka komai ba don Amadin baya gari. La,asarne lis lokacin amma ina kwance na kifa ciki ina tunane a dakin ni kadai naji wayana ya dauki kara lokaci guda ban dago ba don naso na share kiran a lokacin. Hannu na mika na dauko wayan na duba lamban kasan waje nagani yana kirana lokacin mamaki ya kamani tare da tsoron waye wanan din ke kirana. Kodai ya Jafar ne dake can na fada a raina nakai hannuna da sauri na dauki wayan muryan namijin bature ne naji yana fadin hey na amsa da hello. Yace young lady kina magana da Jerry daga Paris ko zaki tuna da mutumin da kika taba kira da wanan number shekara daya daya wuce akan wani wallet da kuka tsunta a cikin gwanjo. Cikin mamaki nace da wanan layin kuwa yace kwarai kuwa kun kirani kuna a Nigeria kun sayi kaya kuka samu wallet dina da kudi da katina nan dai ya tuno min da duk yadda mukayi dashi a ranan. Ohh i remember na fada yace don Allah idan son samune ko zan duba bayan wanan katin na fado mai wasu number dake rubuce a jikin takardan number guda ashirin ne. Kayi hakkuri na fada ka dan bani lokaci don yanzun katin baya tare dani don nayi tafiya amma zanyi kokari naga na turoma da number insha Allah. Koda na kashe wayan sai mamaki ya kamani don lokacin da muka gama magana da Baturen a ranan yace zamu iya amfani da kudin sai ya watsar da takardun na duka na tattarosu na na watsa jakkata ina ganin su kuma ban zubat ba. Haka kawai nake jin takardan zasuyi amfani wata rana son haka banyi gigin zubarwa na aje sai gashi yau wajen shekara daya da rabi ke nan saiga kiran shi ya shigo min a wayana da wata bukata kuma. Tambayan kaina nakeyi da yanzu na watsar da wa yanan tarkacen nasa yaya zanyi anya kuwama wanan dan katin yana nan kuwa a hannuna . Kallo lokaci nayi na mike da sauri zuwa bandaki na dauro alwala na fito nayi sallah a nan inda na sallame sallah na dauko wayana na kira ummah nace taba kanina waya muyi magana dashi. Ya amsa a hannun ummah din nan na fara masa bayanin abinda zai mun har dakina yaje da kyar na samu ya gano jakkar da nake nufi ya dauko yace min yaga katin a ciki naji wani irin dadi a lokacin. Nan nasashi ya katanto min number da mutumin ke nema a jikin katin ya turo min da komai yai mi kuma photo n katin ya turo duk a wayan ummah. Ba bata lokaci na turawa mutumin sako ban kira ba duk ni kadai a dakin nake bidirina nagama bayan nayi sallah na kwanta ban fito ba sai safe kodana fito babu kowa a gidan duk sun fita. Allah ya gani nikan ba zance naji dadin zuwa wanan hutun da nayi zuwa gidan Abba don irin sabin rayuwan da nake gani a gidan yanzu kuma Abbane mai yarda da hakan wai. Gudu sosai motan keyi don haka karfe shidda na safe suna kano suna karyawa inda daga nan zaiyi furfuren mota da zai shiga motan zuwa yola daga kano