Sashe 198
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
din su iyayyenshi hakan baiyi daidai yanzu dai kija bakin ki kici gaba da addua Allah ya dawo manu dashi lafiya yasa tafiyan ya zamo mashi alheri damu gaba dayan mu na amsa da amin ummah hankali tashi tadai dan kwatar min da hankalina mukayi sallama. Yayi mamakin ganin abokan nashi Abuja saidai tunanen shi ya bashi akan matsalan shi da hjy yabi da take damun mutanen da tasan suna da muhinmanci a a wajenshi da kira shine ya kawo su a lokacin. Taro na muhinmanci sosai akai masu kafin su natsu su fara maganan daya kawosu din akan matsaloli biyun da suka tako zuwa Abuja don su gana dashi akai. Matsalan ita hjy yabi din suka fara gabatar mashi tare da bashi hakkuri a kai yana jinsu tare da kallon wanan bakon fuskan da baisani ba a cikin su lokaci lokaci yake dan dago kai ya sauke a kanshi din ya kuma kawar da idanun nasa. Saida ya gama sauraren su yace dasu ba mamaki don a yanzu kunzo da kanku har nan akan nayi hakkuri na sake zama da yabi a gida a matsayin iyalina. Saboda yawan damuwa da magiyan da take maku ko yaushe a waya ko ku kuma kuke ganin hakan bai dace da ita ba a yanzu don kuna ganin ita din matatace ko ? To kada ku manta da yabice silar lalacewan komai a gareni a baya har kun manta da rabani daku da tayi da irin cin fuska da zarfin data dinga yiwa duk wani na tare dani don kawai a barta dani su juyani yadda suke so ita da yan uwanta. To duk ba wanan ba sai irin yadda ta shiga ta fita harta fitar min da zuciyana ga yaron dana haifa a cikina saboda son kai irin nata kawai. Ta yaya kuke ganin zan iya sake zama da wanan matar yanzu a rayuwata bayan irin wanan cin amanan dayi mun haka a rayuwana wanda da badon Allah ya gyara ba da hakan wata,kila da zuciyana ya buga a wanan lokacin. Ba abinda ke cin zuciya kamar zancen yaron nan da bansan halinda yake ciki ba a yanzu shida uwarsa wanda nasan alhakinsa ba zai barni na zauna lafiya ba. Insha Allahu zaka zauna lafiya ai alhaki a kanta ita datayi asirin data rabaka da dan naka wanan bakon fuskan yayi magana na farko tun zaman su a falon bayan gaisawan da sukayi da juna. Ya cigaba da fadin ka godewa Allah dayasa warware maka matsalanka tunkan ka makara lokaci ya kurema zuwa lokacin da gane hakan baida amafani a gareka nan gaba. Amma Allah da ikonsa sai gashi ka kurto daga kaidinta da makarici a cikon lokacin da ake bukatan bawa ya koma ga Allah a lokacin zai dinga istigifari. Malam ai munayi don da taimakon hakan har aka samu na samu kaina daga sherinsu da bansan inda makircinsu zai kaini ba nan gaba. Kwarai kuwa Dan gaske kayi magana daidai gaba don wanan bawan Allah daka gan mu tare dashi a yanzu nasan kana mashi kallon rashin sani a fuska yanzu. Ya amsa da sauri da fadin kwarai kuwa dan tun zuwan ku nake masa kallon inda na sanshi abaya don fuskanshi yana min kama da wanda nasani abaya can amma kuma na manta da inda nasan shi. Ba lalai bane ka sanshi amma shi din yana daya daga cikin wanda ba zaka taba mantawa dashi ba idan kaji abinda muke tafe dashi game da wanan fuskan a yanzun. Zama ya gyara irin na manya yana fuskantarsu da kyau tare da fadin na,am cikin rashin gamsuwa da maganan da suke fadin. Alh jabbo yaci gaba da fadin a yan lokacin daya shude kadan a baya shi wanan bawan Allah ya hadu da wani yaro dayazo daga arewa maso yamma. Yazo da sunan neman mahaifinshi da baisan a ina zai sameshi ba jin hakan yasa bai yarda ya sake yaron hakana ba yayi mai masauki a gidanshi suna bincike a hankali. Da bai fahinci komai ba yaron ya tafi ya barshi da bincike bayan ya nema bai gane komai ba sai yayi amfani da sanin da Allah yayi mai ya gano wasu sirin abubuwan dake boye game da kai da iyalinka. Hakan baisa ya fito a lokacin yayi bayani ba sai daya zauna yayi aiki sosai a kan hakan har Allah ya taimaka ya cinwa makarin abin yakumayi aiki sosai akai ta hanyar yakar wanda ya aikata kulli a ruhinka. Wanda har hakan yayi nasaran kariyan komai dake kulle da ruhinka a wanan gabar kuma ya nememu a matsayin muna aminan ka na can baya don a san yadda za a tunkareka da wanan zancen. Zama ya gyara yana masu kallon ni za a aiwa wanan rainin wayau don sunga ina cikin damu har abin yakai yanzu suyi amfani da wanan daman a hada kai dasu a yaudareni ? Idonshi nakan Alh jabbo din dake bayani lokacin shiko yaci gaba da fadin a cikin hakane yaron ya sanar dashi cewa zaiyi aure shine lokacin da wanan malamin ya nemomu yake muna bayani komai . Kuma ya sanar damu komai daya sani a takaice dai in gajarce maka zancen munje buki a zamfara an daura aure mun tsaya mashi a matsayin iyayye a gareshi mun karba mashi aurensa. Wani kallon mamaki yakewa abokin nasa na kasan abinda kake fadi kuwa yace kwarai abindana fada dai atakaice danka Ahmed yana raye kuma mu munsa da hakan . Kawai dai munbar zancen ne a tsakanin mu tunda mun fahinci baya cikin zuciyar ka a lokacin fitowan shi ya baiyana a gareka hakan na iya haifar da wani matsala sabo .. Alh Jabbo ddana fa kake nufin cewa kunsan da inda yake har kunje kun tsaya mashi a matsayin iyayyensa ?