Sashe 208
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranan na kwana da mamakin inna a raina na rasa menayiwa wanan matar tsana ya shiga tsakani da ita ban gano komai ba sai a karshe da nayi nazarin zancen da naji suna fadin a kaina. Lokacin nagano cewa ba abinda nayi mata na rashin datacewa na farko dai jinin mu baizo daya bane dkn wani lokacin hakan yana faruwa kaji ka tsani mutum ba gaira ba dalili a banza. Sai na biyu kuma ni din ba zabinta bace don na fahinci akwai zabinta data so dan nata ya aura sai Allah yayi dani. Na uku hassada da bakin ciki yayiwa inna yawa akaina tana bakin ciki da gidan dana fito har yakai tana kiran uwana da mugun suna wai itace bora a gidan mu. Wanan kalman na inna da kawarta da suka kira mahaifiyata dashi ya matukan tsaya min a zuciyana gaba daya girmanta ya zube min a idona daga wanan ranan. Haka na kwana da zancen na tashi dashi da safe da wuri na shirya zuwa school kodana fita kamar in wuce bayan na rufo part dina amma wata zuciya tace min me Dije tayi maki ita ? Da inna na fara cin karo a bakin murhunsu tana hura wutan abinda zasu karya dashi na safe Aisha na tsaye tana kallon madubi ta fara shirin fita school ke nan a lokacin itama. Ina kwana kawai nace da ita cikin daure fuskana ba tare dana tsaya yadda na saba ina mata ladabin gaisuwa ranan sai bata samu hakan ba gareni don na wuce dakin dijene kai tsaye abina. Nan ta dago ta bini da kallon mamaki Aisha ma dake tsaye kallon tabini dashi kafin taci gaba da abinda takeyi cikin rashin damuwa don tasan ruwa baya tsami banza ai. Haka kuma na fito ban kalli kowa ba balle in kira suna cewa kawai nayi natafi sai na dawo duk suka bini da kallo don ban jira amsawan kowa ba a cikinsu. Haka na fita ta bini da kallo sai a lokacin ta fahinci cewa naji komai da suka fada a kaina ke nan tunda na fara nuna hakan a fili abinka da mara mutunci sai cewa tayi aikin banza don an fadi gaskiya kike wani fisge fisge ga iska. Inna anyi wani abin ne halan Aishan ta tambayi uwar cikin sonji daga gareta sai uwar tace in anyifa wa zata hurawa hanci tana wani busan iska wa mutane wai ita anzageta anzagi uwarta karya na fada ba yar bora gidansu bace ita. Kai haba haba inna haba zagin uwarta kuma ke ki rabani kada in hada dake amma ke sakariyace ashe ban sani ba Rashida. Har sakarcin naki yakai haka ashe ki zauna kina kishi da matar danki yar cikinki a cikin gidan nan ina ke ina zagin yar nan da ko kanta bata da lokaci balle na wani. Kai umma zaki soma ke nan baki san kan magana ba sai dijen ta kalleta a hasale tace ba kaiba har kafan zancen na sani ba yanzun kika fada da bakinki ba cewa kinbzageta kin zagi uwarta tayi abinda zatayi din. Zatako yi saidai ita da take yat halasne ta samu tarbiya daga iyeyyenta ba zata tankaki ba saidai ta nuna ranta ya baci kawai da wata yar banace aida yanzu kin raina kanki a gidan nan. Allah bata sa,a ranan nima tasan kalata da kyau sannan Umma zagi ke nan don nace kawai uwarta borace tazo tana daga muna kai sai zancen suwaiba dana fadawa inno shi taji dai take fushi ko ? Wai wata suwaiba kuma Asamau dake daki tana sauraren maganan su ta fito tana fada kedai inna baki iya fita zancen suwaiban nan wanan mai shegen kiba kamar tifa ita zaki kwasowa yayan mu wai. Nace a bar zancen nan watau baki fita zancen ba ke don ki nuna min kece kika haifi danki ko Dijen ta fada a hasale tana juyawa zuwa dakonta tabar inna din naci gaba da maganan. Koda na dawo ban bita kanta ba na dai shiga na gaidasu na gaida Dije na fito don ina son inyi girki saboda na kwana biyu ban girka abinci naba Dije ba gashi na kula girkina take ci sosai ita. Zancen kuma munyi shi da hannatu a school tabani shawara kan na kiyayi inna don so take ta bata min suna kada kuma in fasa kyautata mata tunda ina tare da danta. Wanan shawaran na hannatu na rike a raina yasa na dawo banwa kowa magana ba iyaka dai zan kara nisanta kaina da inna din don na fahinci dai bata kaunana kome zan mata kuwa. Ranan sati ban fita school don haka na shaki barcina har tara na safe kodana tashi na shiga cikin gidan nasamu inna din ta fita nagaida Dije da kwana na fito na gyara part dina na dora girki dama na sayo icce fish tun a school na gyara nayi miya dashi don zuwan kannena da ummah tace zata turo min su. Goma da yan mintoci na fito wanka na shirya ke nan naji sallaman su a gidan nayi masu oyoyo zuwan su ya dauke min hankali ga komai duk da rashin kirana da master baiyi a yanzu yana dan damuna nasan kuma fushi yakeyi dani kan zancen bada number wayanshi danayi ga mahaifinshi din. Muna tsaka da kallo da kannena a MBC 3 wayata ta dauki kara nakai hannu na karba daga hannun datti kanina shine a layin yake kira kiri kiri harya katse naki daukan wayan nima na kuma kashe wayan na jefa jakata. Mikewa nayi na shiga daki na kwasowa yaran kayan makulashe na zube a gabansu suka fara murna da ganin hakan na koma na debo na nufi cikin gida na samu su Aisha dukkan su tare da Dije a zaune saman tabarma na mika masu ledan suka karba suna godiya. Nan nake fada masu zuwan kannen nawa don sai lokacin suka san yaran na gidan a lokacin don part dinane na farko nasu yana ta daga ciki. Don haka shine yasa basu sanin wanda ya shigo wurin nawa gashi kuma wurin da katanga da kofa mai kauri dayayi kokari yasa lokacin auren mu. Nabada baya naji Asamau na fadin kai kamar kinsan abinda nake son zuwa saye ke nan yanzu sai Dije tace ato ga yarinya da kirkinta amma uwarku nasom bata ta da mugun halinta. Ita dai aka samu nikan babu uwar mijin da zata sakani a baki in kyaleta ban rama ba duk wadda tayi min ramawa zanyi ba ruwana da wata uwar miji. Jin hakan baisa na tsaya ba na koma part dina wurin yaran na sanesu suna fada wai datti ya kwashe sweet ya basu kadan nace su bari na kara masu wani. Na shiga na dauko zan fitone naji datti na fadin anty jiya anyi fada da mama da ummah har mama tace wai bamu samun komai saidai ummah tayi ta wahala damu yaranta sun gama kwashe komai. Shi yaron abinda yaji shiya fadi a cikin shirmenshi ni kuma ya barni da nazarin me mamake nufi da hakan data fada garemu duk da shirmesa na yara ya fada na fahinci wani abu. Watau tana ganin yarantane manya a gidan mu sun kwashe komai da Abban mu kedashi yanzu saidai ummah tayi tayin wahala akan mu ke nan. Inko hakane Allah yafita yafi sherinta don Allah yasan da duk bawansa dake duniya nan fadan Abba da hjy karima da naji su ummah na magana a waya kuma ya sake dawo min a rai nake tambayan kaina komeya kawo fada tsakanin su oho ? Wuni mukayi da yaran sai dare shehu yazo ya kwashesu zuwa gida naji kamar kada su wuce su barni a wanan gidan da nake zaman shi kamar na dole yanzu. Anyi haka da kwana biyu Allah ya dawo da master lafiya a cikin dare sosai ya iso don zuwa lokacin kafin iso din har hakkurin yan uwanshi ya soma karewa a lokacin . Don sun fara tambayan wai ina yajene haka har yake neman ya kwaahe wata baya nan itako inna cewa tayi cikin magana nidai Allah ya cece mu idan ba wani mugun wuri aka tura min shi ba don ya samu kudi ayi wadda akaso. Dijece ta bata amsa a lokacin da tambayanta waye zai turashi wani wajen don yai kudi dashi koshi Amadin har yanzu yarone kuma da za a turashi abu bai tashi yiba ? Tace nasani umma tunda bai cikin hankalinshi daidai sai abinda akace yayi yakeyi yanzu komai ma ai yana iya faruwa a hakan yanzu. Na daiga alaman nan gaba nice zaki kira da manya kan danki a gidan nan tunda yanzu idon ki ya bude uban kowa baki kunya ke yanzu don take takenki sarai naganeshi a gidan nan. Yanzu dai umma nagane zance ina yarongane baki son in saka baki daga yau na dai kada kuma a fadi abinda bance ba gashi naji an fara fadi yamzu. Sunyi hakan da kwana biyu cikin dare misalin shadayan dare sai gashi kamar anjefoshi daga sama mukaji sallaman shi nikan na rufe a lokacin saida Asmau ta kwankwas min kofa nace waye tace ki tashi ki bude yayane ya dawo. Asmau kinsan fa idan nayi barci banason a tasheni don Allah kada ki dameni sai naji muryanshi yana fadin bude min kofan mana na shigo. Jin hakan yasa na zabura da karfi na zo na bude kofan yana tsaye da suith baka daya balle aniniyar jikinta kina iya ganin farar riganshi dake ciki farinshi na asali ya fito fili sosai ya sake kamani a dan lokaci kankani da yayi batare damu ba ga kanshi yayi aski gashinshina fulani daya soma fitowa yayi kwace lup bakikirin a saman kan nasa gwanin ban sha,awa a lokacin.. Kallon shi nayi na dukar da kaina don nasan banda gaskiya na dance mai sannu da zuwa ya amsa min da yaiwa ki bude kofan can a shigo min da kaya ya fadawa Asamau din dake tsaye dauke da wani jakkar kayanshi a lokacin. Yasa hannu ya karba daga hannun sister nashi nakai hannu zan karba a hannunshi yace no bar wanan in shiga dashi ciki tukunna. Na jaye ya shige da shi zuwa uwar daka ni kuma na fita zuwa kitchen dina in duba ko akwai ruwan