← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 246 OF 286

Sashe 246

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

a zatonsu ci zanyi kada kiyi gangancin cinsa fa matar Amadi dije ta fada shakawa zanyi na bata amsa ina kaiwa a hancina sosai na shaka naji wani irin abu ya doki kaina lokaci guda. Amma yana kaiwa kamar minti biyu na fara jin kasala a jikina yana rufeni lokacin inna ta miko min maganin nasha na karba kada kisha idan ta baki kalman daya fado min a raina ke nan ajewa nayi gefena tace ki sha mana nace zan wanke bakinane na mike zuwa bandaki. Allah ya taimaka koda na fito sun koma bandaki nayi saurin daukan cup din maganin zuwa bandaki na watsar na zuba ruwa na dawo da kofin na zauna a bakin gadona kamar nasha. Aisha ta leko take fadin ashe kin fito zubur inna ta mike tana fadin dauki maganin kisha tun baiyi sanyi ba Aisha tace ai tasha ta shanye tace eh ta shigo tace aiko abu yayi tunda tana shan maganin. Ai kinsan saukin kaine da ita bata gudun magani ita dije ta fada ga mijinki Aisha ta fada ta miko min wayan na karba muryan shi cikin damuwa yake magana tambayana yake ya jikin nace da sauki yace ance ciwon ya matsa ummah zatazo kuje asibiti nace toh yanzu ina kike ji nace kaina da kirjina ke min suya. Barin karanto maki Al jinn don dashi Annabi sulaiman ya yaki shedanun lokacinsa a hankali ya fara karanto min a hankali kuma barci ke daukana ban kara sanin a inda nake ba kuma tun wanan lokacin. Ina tashi naganni a gadon asibiti kwance gasu ummah da yan gidansu Ahmed a kaina sannu suka fara yi min ina amsawa da kyat daga bayan su nurse ke fadin na fada maku tun dazun ku rage a dakin nan. Likitane ya shigo tare da nurse biyu mata zai dubani yasa suka rage a dakin aka bar Tani da ummah sai wata tsohuwa dake zaune itama yar tanice don na santa dama. Sunzo da itane wai zata zauna dani a dakina saigashi kuma ankaiga bani gado na kwanta asibitin su suka rage a dakin lokacin tare dani . Likita ya farawa ummah bayanin zasu fara min magani don inji sauki in samu barci za a kuma daura min ruwa a lokacin kai na fara girgizawa a hankali kafin nace a,a , a,a ummah. Don Allah ku mayar dani gida kada ki bari suyi min komai idan ba magani zasu ban ba nasha idan suyi min zan mutune ummah. An fada min kuma naga komai zasu halakanine ummah ke don Allah kiyi shiru kin taba ganin wanda aka halaka a asibiti ne ummah ta fada a hasale. Wallahi ummah ba karya nakeyi ba ki yarda dani komai dana gani a cikin mafalkin yana faruwa daya bayan daya don haka ku barini indai kuna kaunata. Likita ka bar yarinyar nan tunda ta fadi haka kada kuyi mata wani abu a samu matsala wanan tsohuwar da zata zauna dani ta fada daga inda take zaune. Shiko likitan bai kulamu ba sai zukam alluran da yake shirin min yakeyi yana murmushi ya gama yayo kaina yana fadin kada ki damu babu zafi ai wanan murmushin nan naga halittanshi ya juye min ya zama wani kamar dodo a lokacin. Basu ankara ba sai wani irin hankade likitan nayi tare da tsale na sauka a saman gadon nayi waje hakan danayi sai hankali ya tashi dani. Su a ganinsu na zautune yasa hakan nan suka biyoni hankali tashe na karbi hijjab a hannun dije na saka nake fada masu banson allura na fada gashi kuma wallahi nagani likitan nan yana rikida ba mutum bane shi. Hakan dana fada a karshe shiya kara daga masu hankali kai hjy kubar yarinyar nan tunda har an gane cewa ba ciwon asibitine ke damunta kada azo ai mata wani abu tunda sun fada sun kuma nuna alaman basa so to in kunbi ta nawa ku barta aci gaba da mata nagida a gani. Wanan tsohuwar take fadin hakan hankali tashe ga ummah kallonta ummah din tayi tace to iyan jummai haka zamu kyaleta tana wahala ai ba zamu dakatanata ba ko ? Zafin ciwone kawai ke damunta ba wani abu ba zaki aikata kuskure babba kuwa hjy don wallahi na taba ganin hakan a unguwar mu akaki yarda ya zama sanadinta. Jikin ummah din ne yayi sanyi haka dai suka rarasheni na koma dakin kowa na fadin na bakinsa saida aka rage ina lafe nayi shiru naji suna maganan lokacin na fara fada masu abinda naji a mafalkin da kuma komai daya faru har maganin da inna ta kawo min da aka hana insha. Washe gari dai aka ban sallama tunda safe muka kwaso muka dawo gida hakana amma ina yawan shaka kwalon tumfafiyan nan da Dije ke wahalan tsunko min a kai akai. Na fara jin sauki har ina dan iya cin abinci amma abu mai ruwa ruwa nake samu ya zauna min a cikina wanan tsohuwar dai ita ta fara magana dagani sai ita a daki sai kuma ummah tana shigowa ranan ta gane hakan. Tace anya iyar jummai wanan kawar taki ita kadaine kuwa don gaskiya akwai sauyi sosai a jikinta wata kawar ummah dince tazo har gida ta aunani ciki wata hudu yake batun shiga lokacin. Sunyi mamakin hakan sosai ummah da kanta take fadawa Ahmed din sun dade suna magana sai lokacin hankalinshi ya kwanta a karshe da sukai waya da mahaifinshi yake sanar dashi halin da nake ciki. Mahaifin nasa yace tunda na gama karatu a lokacin me zai hana in bishi kawai mu je can a dubani yadda ya dace don zaman nan ai baida alfanu a yanzu gareni tunda shima hankalinshi ba zai kwanta da hakan ba shima. Tafiya ya kama da Dije hakan ya dan kawo tsaiko ga tafiyan mu din inna ko hankalinta ya tashi sosai da jin hakan duk dauriyan ta sai data nuna a fili bata son hakan yakai mahaifin Ahmed din ya kira a waya yayi mata magana da murya mai kaushi a gareta. Gidan mu kuma basu sani ba sai ana saura kwana uku zamu wuce abujan naje na sallamesu nake fadawa mama nace mama nazo inyi maku sallamane ranan Tuesday zamu tafi. Ina ta tambaya cikin mamaki nace zan sameshi a can ne mahaifinshi yace mu sameshi na haihu a can ikon Allah yanzu shine ba a fada min ba sai yanzu Allah ya kaiku lafiya yasa a sauke lafiya nace amin na daga na fito daga part din zuwa namu. Tafiyan mu gari ya dauki zance kamar an fasa bom lokaci guda maganan ya yadu a cikin gari kowa da abinda yake fada a kan mu. Kwanan mu biyu a abuja muka daga zuwa US nida dije da sauran abokan tafiya da muka hadu a filin jirgi ban sha wahala ba don nasan yadda ake fita don haka ban wahala bani. Saidai Dije da abin take gani kamar a mafarki itace ta dan ban wahala kadan koshi ba sosai ba a lokacin kuma fada sosai mama tayi da ummah wai an munafunce ta an dauketa muguwa ko me ?
Chapter 246 · 0% Book details