Sashe 37
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya zaba tare da rokan mai kayan ya aje mai zuwa safe ko yamma zai dawo ya saye sauran ga baki daya . Mutumin yai shiru na dan lokaci kafin ya duba sabo da kwazon yaron yace amma idan bakai bane banayin haka gaskiya tunda inada masaya. Ida har bakazo ba zuwa biyar zan sayar dasu duka gaskiya yana magana yana hada sauran kayan a wuri daya don ya adana mashi kada wani yazo ya dauka bai sani ba. Ya bashi kudin tare da godiya kan karancin da yayi mai saboda sabo da juna da sukayi ya dauko kayan shi zuwa inda zai samu abin hawa da zai kaishi unguwarsu. Da kayan shi niki niki ya shigo bai tsaya ba sai kofan dakin Dije data riga ta tayar da sallah magariba a lokaci shima buta ya dauka ya fara alwala kada ya rasa jam,i. Bai dawo gidan ba sai yamma lis ya dawo duk a gajiye yake sosai a lokacin hakan bai hana shi zuwa wurin uwar garke dake kwance ba ita da yayan ta.. Duban abin abincin su yayi babu komai a cikin kwanon haka yasa ya fita gidan ba tare da sanin Dije ba yaje gidan da ake sayar da abincin dabbobi unguwar don ya sayo masu. Dije wace taji shigowan shi gidan saidai bata karajin motsin shi ba a zatonta yana dakin shi yana hada kaya ta fito tana magana taji shiru. Yau ga ja,iri kafita ne koka kewaya ban dakine wai ita kadai take maganan a tsakar gida sai gashi ya bullo a cikin duhu har saida ta dan kadu dan ganin shi a lokacin. Tambaya yayi lafiya kike nan a tsaye cikin duhu wai kai na fito nema naji motsin ka kuma nazo naji shiru ashema kana waje. Naje nan gidan malu ce na karbowa dabbobin nan abinci don naga basu da abinci saidai dusan gwaunatice na samu na gargajiyan ya kare tace. Dadina dakai Amadi akwai kula duk da wanan gajiyan daka kwaso bai hana ka tuna da bayin Allah nan ba a ranka Dije dole mu kula dasu tunda mun turkesu a wuri daya idan bamu basu abinci ba sai Allah ya tambayemu hakkin su akan mu. Yana bata amsa ya duka yana zubawa dabbobin abinci kafin yakai hannu ga uwar garke yana fadin uwar garke tashi kiyi kiwo kada ki kwana da yunwa kinji kuci sai na sayo maku haki gobe insha Allahu. Zakace da mutane yake wanan maganan yadda dabbobin suka mike suka fara kiwo lokaci guda abin shan ruwan su ya dauka ya daure guntun jarkan da aka yanke ana zuba masu ruwan sha a ciki yaje har randan ruwan su ya debo ruwa lokacin ya farga da basu sa ruwa a gidan ashe. Yana gamawa da dabbobin ruwa ya fara diban masu yana cika kayan zuba ruwan Dije duk ya samu ya cika don ya samu ba mutane sosai wurin ruwan. Sai goma da wani abu ya samu kanshi ya sauya kayan jikinshi ya nufo dakin Dije wace ke shirin kwanciya hannu dauke da takardan da yarinyar nan da sunan gidan su ya sani na MAYANA. Zama yayi yana bude takardan don ganin meke ciki kudine suka zobo daga cikin takardan zuwa jikin shi sabi dasu kar saida ya dan kadu da ganin hakan. Kai din da yace yasa Dije juyowa inda yake tana kalloshi idonta ya sauka saman kudin da yake tattarawa a jikinshi. Amadi ina kafito da wanan kudin sabbi haka kar dasu tana tambaya take tsureshi da ido a cikin tsaro da son jin ina ya fito da wa yan nan kudin masu yawa. Bai dago kaiba don tsayawa da yayi kidaya kudin dubu darine cif din su a mike dinsu suna daukan ido tambaya ta jefo mai da ina kafito da wanan kudin Amadi ? Wallahi Dije ina wanan yarinyar da matar nan tazo gidan nan karbawa magani wurin malam tanimu ranan to itace dazun ta bani shi tace don Allah na karba kada in bude sai nazo gida. Nina dauka ma wani takardan wani abune a ciki ai ashe kudine ta saka haka a cikin takardan nan ta bani har tana fadim nayi hakkuri dashi don Allah. Amadi kudi lafiya mace ce zata baka kudi haka kuma yarinya karama kadafa ta jawo muna matsala muna zaune kalau a yanzu ?