← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 263 OF 286

Sashe 263

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bamu samu shigo Nigeria ba a takaice sai da muka share shekara biyar acan a cikin na shidda ya shirya muna zuwa gida koshi zuwan da dalili. Don Abbana da baida lafiya sosai a lokacin yasa muka shirya a gagauce zuwa gida saidai zamu sauka a karo na farkone a gidan mahaifinshi yadda ya bukata. Lokacin yarana biyu ina dauke da cikin na ukku a jikina saukan dare mukayi don haka a part din da aka shirya muna muka sauka mun samu an hada muna abincin taro da komai a ciki. Saidai kafin mu shiga na kula master baiyi gagawan shiga ciki ba a bakin get yasa driver ya tsaya ya fito mun dan dade tsaye a wurin kafin yaba driver umurnin shiga damu cikin haraban gida shiko ya tako da kafa zuwa cikin haraban gidan. Tun lokacin nasan shima hatsabibin kanshine ashe gidane mai kyau wanda ban taba tsamani ba gaskiya ashe Abban ya tambayeni waye ubana a lokacin dana fara ganin shi. Da gajiya a jikin mu sosai abincin ma shida kansa yaba yaran sukaci shida Dije wanka na shiga na fito na nemi abincina fresh milk na kinkima nasha tare da dan cake na kwanta. Koda matar gidan ta shigo ta samu na kwanta a lokacin don haka bamu samu ganin juna da ita ba saida safe shidai kan ba zance yayi barci ba a ranan. Don zaune ya kwana yana lazumi bandai san abinda yakewa ba amma naga hakan gareshi don duk falkowa nayi zan gashi a tsaye yana sallah ko zaune ya daga hannayenshi sama yana rokon Allah. Saidai ni din ma dana samu barci mafalkaiya nake faman yi a lokacin da na samu barci zan gani a cikin iccen tumfafiya masu yawa wani lokaci suyi min haske wani lokaci kuma kore shar nake ganin su. Idan kuma fitsari ya tayar dani don maganin da nake sha yana yawan sakani fitsari sosai haka kuma banda abinci sai abu mai dan ruwa zansha ya zauna a ciki idan na yashi na kewaya na dawo na kwanta zaci gaba da irin mafalki gudane na wanan iccen na tumfafiyar masu yawa a wuri. Sai a karshene gabanin asubahi na ganmu dukkan mu har yaran zaune saman wani dadduma mai kyau a cikin zugun tumfafiyan wani mutum daya bamu baya yana fadin ai na fada maku zaku shigo ku zauna kamar kowa. Danan da can a yanzu kun wuce kaidin kowa a cikinsu hankalinku da natsuwanku da rike Allah da kukaiyine ya kaiku ga nasara a yanzu din don haka. Babu wani mahalukin daya isa ya taba lafiyan ku face wanan abinda yai maku kwatankwancin shi bai sameshi ba kudai kada kuyiwa kowa sheri a rayuwan ku shine cikar imanin bawa sai dai idan ku kuka canza rayuwan ku nan gaba zakuga akasin hakan. Master yace dashi bamu fatan mu canza akullun muna kawo Allah a gaban komai da zamuyi don haka ubangiji ba zai yarda mu halaka ba insha Allah kai waye wai da kazo muna nan yanzu Mutumin yace ni nine mahadin kaddaranku na asalin don nine sanadiyar haduwan ruhin ku a nan baki daya. Da mutumin ya juyo sai naga tsohone kuma na taba ganin fuskashi a baya na nunashi da yatsa ina fadin dama baba kaine ashe yayi min murmushi yace nice diyana . Na bishi da kallon mamaki naga ya juya ba tare daya kara magana ba ya shige cikin duhun wanan itatuwan na tumfafiyan yana saye da dogon jallabiya fara da dan buhunshi saman kafadanshi yana dogara sandan shi kamar ranan dana fara haduwa dashi a hanyar makarantarmu. Na bude baki zanyi magana lokacin ya kusa lumewa nace baba din Allah ka dawo ka karbi sadaka yau ban baka ba ka wuce daga inda yake ya tsaya ya miko min hannunshi. Abin mamaki sai naga hannun sun kawo har inda muke zaune duk da dan nisan dake tsakanin mu dashi a lokacin na bude jakkata na debe kudi na basa yadda yai min addua a ranan irinsa ya maimaita mun a lokacin na dago kai ince amin sai naga ya bace bangasa ba na fara fadin innalillahi da hakan na farka ina ambata innalillahi a bakina. Naga master ya kalloni daga inda yake zaune ya bude Alkur,ani yana karatu yace ke zahra lafiya meke faruwa dakene haka tun dazun kike suraitai fa. Bin dakin nayi da kallo na tuna a inda nake zaune nakai ina fadin mafalki kila nakeyi na bashi amsa da hakan kafin na mike na shiga bandaki. Washegari bayan munyi wanka mun shirya gaba dayan mu muka dunguma zuwa falo inda mutanen gidan suke jiran mu muci abinci. Shine gaba yana dauke da dansa Amir mai sunan Abbanshi Abubakar ke nan ya riko Bananh da dayan hannun shi nida Dije muna daga bayansu. Yayin da yan gidan gaba dayansu suke zaune saman kujera sun zubo muna idanu tun lokacin da sukaji sallamanmu din suka dago suna kallon mu inka debe salima dake duke da kai tana dakilan wayanta a yangance a lokacin. Muka shigo wurin Abba din muka nufa inda yake zaune muka zube kasa har Dije da sauri Abban ke fadin haba haba mama kizo ki zauna ga wuri nan a tanada maku ku tashi ku zauna ga kujera nan. Shiya mike ya gyarawa Dije wurin ta zauna ya dawo kasan inda yake yana gaida mahaifinshi a cikin ladabi ya amsa yana mika hannu ya dauki takwaranshi yaron yaki zuwa ya kara makewa a jikin ubanshi. Yace mai sunan ne kuwa dakin takwaransa a cikin hausansu irin ta fulani da yakeyi a harshenshi kafin yace idan shi bai zuwa ke mata kizo yana mikawa yarinyar hannu ta sone kai a jikin babanta. Abban yayi dariya yace watau baku san kowa ba sai iyayyen ku ko kaina duk yana duke a lokacin kafin na dago ina fadin Abba ina kwana ya amsa da fadin . Zahra kunzo lafiya ya hanya da zaman jirgi jikin naki da sauki dai ko na amsa da fadin Alhamdullahi Abba mun sameku lafiya ? Kana na sake dagowa nace mommy ina kwana ya gida mun sameku lafiya ta amsa a sake cikin sakin fuska da nuna jin dadin ganin mu. Kana nayiwa sauran jam,i da fadin kuna lafiya ya muka sameku dacewan yaran dake wurin da suka zuba muna ido suna kallon mu for the first time a cikinsu a lokacin. Na daiji an amsa ba zance ga wa yanda suka amsa min ba a lokacin saidai ina tunanen cewa amma badai wanan matar bace ta haifesu duka amma zamu sani gaba ai. Duk abin nan master bai dago kansa ba don jin yaran ba wanda ya iya gaida dije a lokacin inka debe hjyn data gaishe ta hanyar fadin mama sannun ku da gajiya ya hanya ya kuma zaman can ku dai sha turai sun baki wahala. Shine ya dago yana gaisheta sai kuma wasu yan mata mutum biyu da suka fito daga ciki tun kan su zauna suke fadin a,a sannunku da zuwa yaya hanya anty sannu da zuwa . A cikin fara,a suma suka gaida dije din dayan harda ba,a tana fadin tsohuwa kinsha hanya sannu da kokari ai naso ku iso idon mu biyu sai gashi kunzo munyi barci lokacin. Hjyn tace idan idonki biyu me zaki mata tana dariya tace wai na kamata ta fito mota mummy kinsan tsufa to baku daiga fitowan nata ba ai. No yaya ya daukota ko anty mungani ai a cikin mafalkin mu daga can daya daga cikin wa yanda muka fara sama a wurin naji muryan daya na fadin nifa na daukota zuwa mota amma yanzun zata rama wahalan daukota da nayi don abinci zata ban a baki naci . Aka kwashe da dariya yaci gaba da fadin yau ai har goyon nan na kaka saitayi min shi a gidan nan nima tunda Bros kawai kike goyawa shi kadai mu kin barmu nan ya fada yana tasowa zuwa inda take ya duka tare da riko hannun dije din ya dora akansa yana fadin ki fara saka min albarka kafin mu gaisa. Dan murmushi yake master yayi yace kai daka daukota a bayanka tun jiya aita gama saka mata albarka a wurin nan dai sukai ta jan dijen da firan jika da kaka kafin ya dago zuwa wurin dan uwan nasa ya zauna a gefenshi yace. Bros ya hanya ya aiki kuma da mutanen can yana mika masa hannu a cikin fara,a dan uwan nasa da har lokacin fuskanshi a daure yake falon yace yasir ya kake ya aiki kuma ? Wallahi lafiya kalau Bros yau Allah ya nufa zamu hadu kwanan nima na dawo bai one week ba ina gani kana ya dago yana dan leko kai yace madam ya kike ya yara kuma ? Na dago na amsa mai a lokacin Abba ke fadin Alh dai jiki ya kiya nacewa mijin ki ya kaishi indiya in yaga jikin har yanzu sai a shirya a fita dashi zaifi. Nagode Abba na fada cikin girmamawa a gareshi so sorry Dad dinkine baida lafiya shine dalilin zuwan mu kasan Master ya bashi amsa ayyah sorry ko a cikin kulawa. Cikin dakewan murya yace hjy fa ko tayi tafiyane hjy ko kana nufin mummy din mu yace eh bata nan ne banganta bane ai tun jiya din shiru yasir din yayi kafin karamin yace wai daddy ya koreta a gidan nan saboda , , , Musty ka faye surutu kai aka tambaya ta dago tana fadawa yaron haka a cikin harara yace mum fa ya tambaya sister shine ka rufa min bakinka a nan ta fada da dan tsawa. Yaron ya soke kanshi cikin wani murya mai kaushi muryan Abba ya ambaci sunanta yace ke Salima bakiga babban yayanku bane da matarsa da suka shigo falon nan ? Daddy na gansu mana ta fada a tsiwace tana mayar da air piecer a cikin kunnuwanta yayin da jikinta yake saye da wani dan riga fari mara hannu mai aniniyaiya zuwa kasa karshen hannun rigan an takwasheshi daga can ta hammatanshi. Sai dan wando pink wanda ya tsaya mata iya sharaban kafa shima wandon kuma an masa anini a karshe ya matse kafan wanda hakan ya kara fito mata da yan gajerarun kafaduwanta farare a waje. Don gajerace mazan
Chapter 263 · 0% Book details