← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 276 OF 286

Sashe 276

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sosai na kuma yi masa addua Allah ya kawo masa dauki cikin lamarinsa yace amin mukayi sallama dashi yace sai ya kara zagayowa nace ya jirani na shiga daki nafito da kudi a hannuna na mika mai yace . Zahra bansan me zance maki ba kinga wanan dan zaman da kika ban lokacin ki mukayi yafi min komai dadi a yanzu don yafi min wanan kudin da kika bani don babu wanda ke zama dani muyi magana ta fahinta sai ummah saiko ke yanzu da muka zauna dake kika fahinceni. Hawayene ya taru a idona nace yaya kowama yana fahitar ka kawai dai don baka dashi yanzu Abba kuma dake baka shima baidashi a yanzu yasa suke maka daukan mahaukaci. Tare da taimakon ka kuma yaya don wanan shaye shayen shine ya kara sa mutane suna maka daukan mahaukaci ba girman ka bane da darajanka ace wai kana sha a yanzu. Shekarun ku yakai ace kun fara aje mata a yanzu dakai da yaya jafar gurin su mama ke nan yanzu a kanku suga kun fara aje iyali a tare daku. Dariya yayi yana fadin kai zahra waye zaisoni a haka ki dai tayani rokon Allah na samu abinyi na gina gidan kaina inda zan aje mata. Muka kwashi lokaci tsaye muna magana ya sallameni ya tafi nima na koma ciki na zauna ina tunanen duniya gaskiya mutum ya godewa Allah idan Allah ya tsarkake masa zuciyan shi ga komai. Yau yayan mamace ke wanan gararanban rayuwa haka rayuwa bashi da tabbas ga dan Adam don in kaine yau bakaine gobe ba na tuna yadda mama da yaranta suke kamar wani gwanati ga iko ga izza da takama da isa ga kowa sai tayima kallon banzan nan nata a wullakance zata kalli mutum. Sai gashi a yanzu yadda naga su mama har yaranta mata da take mutuwan so duk sun koma abin tausayi don komai ya kare a yanzu din dama ashe da abin hannun Abba suke komai. Amma a lokacin mama cewa takeyi ni ban dogara da abin Alh ba kun sani kodashi ko bashi sai inyi yadda nake so a rayuwata Allah ke nan yanzu tun a duniya yake jarabtan bawansa. Wai yau mamace ke fadin sun rasa motan shiga a gidan mu ta manta lokacin data karbe min mota kuma ba ai komai ba haka maganan ya zauna motar ta karbu ke nan kuwa. Don duk zaman auren da nayi gidan Abba banda mota shima baida shi dama kuma hakan akeson aga rayuwan mu ciki sai gashi da taimakon Allah abubuwa sun juya a yanzu. Tau gamu dai mun zo naji muryan Asmau dake shigowa gidan tana fadi hakan ya katse min tunanena na gidan mu a lokacin na koma kallon Asmau dasuka shigo da kawayen ta gidan. Mamaki naji yadda akayi suka san gidan na taresu da haba haba ina masu sannu da zuwa nasa aka kawo masu abinci da abinsha da sauran abin motsa baki. Aisha ta fito tana masu sannu da zuwa suka amsa nan Asmau ta fara sake magana a fakaice dana fahinci dani sukeyi na mike ina fadin jummai idan bakin sun fita ki gyara wurin ni zan kwantane na kallesu a wullakance nace sai anjiman ku ko . Na hada kan yarana dake wasa muka shige ciki abina na dasu na rufo kofa na barsu a falon zaune sai ta muzanta a wurin kawayen nata a lokacin irin yadda nayi masu din don haka basu dade bama sukace zasu tafi. Tana zuwa gida take ba inna labari tace inna yau naga duniya naje gidan yaya da tambaya da komai saida nagano gidan wallahi can fa New GRA gidan yake cikin manyan mutane inna. Hummm kinga Zahra yadda take mulki lallai Zahra ta gama maki da da wallahi saidai hakkuri bayama gari ashe Aisha ke fada muna dije ko har muka fito gidan bata fito mun gaisa da ita ba. Yau inna naga abu ke wallahi inna wani abin ma na gidan ban taba ganin sa nidai Zahra wai harda cewa a wanke kayan da mukaci abincin dashi idan mun gama yaran nason zuwa wurin mu ta hana. Halan daga gidan ubanta tazo dasu ko taki ko taso dai dole ace daku kanen ubansune kuma ciki daya kuka kwanta da ubansu. Abinda nake hangowa ke nan tun farko naso tun lokacin ya kara aure don gudun irin hakan dama nasan tunda ba raggo baneshi yana samu hakace zata kasance dashi sai yadda suka juyashi. Yanzu gashi sun mallakeshi komai suke tsara mai yadda zaiyi bai daukemu a bakin komai ba ga umma ta mallake masa zuciya kamar itace ta haifoshi duniya. Dije kan ji take kamar itace uwarsu don a yanzu nunawa take kamar itace uwarshi dole inna sai kinyiwa abin tufka gaba dayansu ke seta masu hankalinsu harshi kansa din ki nuna masu kece uwarshi dai. Gobe sammako zan masu a gidan wai nan suga yan birni sun barmu a rubaben gida sun koma sabo na gani na fada nida wahalan ciki na haifi da suda jin dadinshi a yanzu. Lalai dai kan inna sai kin nuna masu cewa kema da sauranki zasu shiga hankalinsu dake don wallahi inkince zaki zuba ido ana abubuwa haka za a shaki a banza bagas. Don da gangan Dije keyi hakan don bata son ki ni na taba ganin ace wai kaka ta shige gaban uwa ta kicicine komai ta hana gaba ta hana baya duk ta tare kofa babu wuri duk wanda yazo ba zai shiga ba. Ai kilama asiri ta hadashi dashi da bai ganin kowa da mutunci sai ita don komai Dije zata iya akanshi inba haka yaya zai rika barin ki ya kama dije sai matarshi. Uwar tace ba asiri bane kafazucin juna sukeyi ita dashi don tun lokacin dana haifeshi a hannunta yake har yau din nan kiga kuwa yafi saninta dani. Nima yanzun nake jin haushin hakan yadda na barshi kamar ba dana bane nasan harda abubuwan da babanku yai ta masa a lokacin ya hada yake jin haushina yanzu a kansa. Ni kuma Allah ya gani lokacin dana san babanku zai tafi ya barmu ne dana kamashi sosai wallahi amma a lokacin sai nake tsoron kada in matsawa son dana baban naku ya sakoni kan hakan a fara kirga min dakin aure yasa na biyewa hauka irin nasa nakin agola a gidansa. Atoh ki daiyi wani abu ake kika haifesa ba dije ba don me yanzu dije zata dinga jin dadinsa ita kadai ke a wareki a gefe dole kan sai kinyi wani abu zasu tuna da hakan. Sallama aka kwada suka amsa wani daga kofa yace masu ginane sukazo duban wuri muna son a bamu izini mu shigo mu duba gidan don Allah ? Kallon juna sukayi kafin ita Asmau tace anya malam nane kuwa akace kazo ka duba yace kwarai banan bane gidansu Master tsoho wanda ke auren zahra yar gidan Ali custom yanzu ? Asmau ce ta mike ta fita don taga ko suwaye ta samu mutum hudu a tsaye waje kallo ta bisu dashi tana fadin master ne ya turomu muzo mu duba gidan nan za ai masa aikine a ciki. Wani murguda baki tayi tana fadin mu ai bai fada muna cewa zakuzo ba don haka bamu san da zancen ba mu sai ku koma ku fada mashi bamu da labarin wani aiki a gidan nan.
Chapter 276 · 0% Book details