← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 286

Sashe 154

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta tafi unguwa wai suna bukine yau kila saida yamma idan ta dawo ko kin iyane ki mun don Allah ta fada tana kallon fuskana. Murmushi nayi nace ban iya kitso sosai ba amma ina dan kamawa tace ko yayane dai don Allah ki mun don gobe kada in shiga mutane dakaina haka kinsan akwai bukin nan cikin gida da za ayi goben ko ba a fada maki bane ta dago tana tambayana. Wazai fada min Aisha kila sunga bukin bai shafeni bane yasa ba a fada min ba koma an fada kinsan Master baya gari ba lalai bane in tafi tunda bai nan. Kuma gaskiyane don nasan yaya yaji labari kin fita zuwa buki baina yana iya yin fada gashi ko banza ba shiri sukeyi da gidan ba don sun tsani kowa namu. Dijece make fada min dazun cewa abin ya samo asaline tun bayan rasuwan mijinta malam Ladan yan uwan nasa suka tsani yayanta din har muma abin ya shafemu. Balle suna muna kallon tallakawane a cikin su ko abu sukeyi basu faye saka mu ciki ba tunda mu bamu da irin tufafin yan gayu irin su. Ke Aisha ki godewa Allah kowa da abinda Allah ya bashi yake shiga yan uwa kin gani nan ban faye damuwa da irin abubuwan nan ba balle ko bamza ni ba buki nake zuwa ba dama. Gara dake ko banza ku yan gayune ba wanda zai maki wanan kallon amma ita innan mu bata damu da hakan ba haka take kokarin cunamu cikin su wai sune dai yan uwan nata. Ko wanan bukin kafin yaya ya tafi saida ta matsa mashi ya bata kudin da zata bayar na bukin a cikine naga ta sai wani atamfa ta dinka waishi zata goben muko kinga haka zamu shiga da tsofin kayan mu suna muna kallon banza. Mikewa nayi na shiga daki na dauko cumb da tsinken kitso ina fadin zauna nayi maki kafin innan su dawo ta samu kin shigo nan din. Wai ashe kema kinsan tana hanamu shigo wurin ki yanzu Dije tayi maganan hakan tace wai bata son wullakcine kada ki dauka don abinki muke binki nan. Aiko hakan ma nagode kisan kowa da nasa irin fahintar ai daga hakan naja bakina nayi shiru Allah ya taimaka mukai kitson har lokacin bata dawo har muka dora indomie a wuta mukaci tare a plate daya muna hira tana ban hiran zaman su Niger. Bamu dade da gama cin abincin ba sai mukaji shigowan su gidan ta tashi ta tafi lokacin nayi sallah na gyaro part dina na da muka dan bata. Na koma zaman kadaici don Aisha din ta dan debe min kewa da sato hanyar da takeyi din ta shigo wurina nakan ji dadin hakan sosai a raina. Don zaman kadaici baida dadi ga mutum ko ya yake kuwa gara kana dan magana da wani duk da bawai ina samun hakan bane ko wani lokaci kuma daman hakan ba damuna yayi ba. Amma kuma gashi uwar su yanzun tana skn sakani wani hali a rayuwana wanda bansan dalilin hakan ba a yanzu. A wanan zaman ne naji zancen wanan matar kawar inna data kira kanta da yar Giwa zancen tane tiryan tiryan yake dawo min a zuciyana. Naga laifin me nayiwa innan su Ahmed haka ta tsani sai naji ina son yin wanan zancen da wani ko zan samu mafita duk ban taba yin wani zancen ta da kowa ba ni kadai nake shanye abina a raina duk abinda akai min din na cin fuska. Saida ba zan iya wanan maganan da ummah ba don nasan itama tana can da nata tarin matsalolin datake fuskanta gidan wanda kullun bai karewa garesu. Hannatu ya kamata na kira zuciyana ya bani hakan duk da shekarun mu dayane ba wani shawaran zansamu da zai gamsheni ba amma ita din ya kamata na kira na fara jin me zata fada min kan hakan. Kiran dana danna mata sai gashi ya shiga ta dauka tana fadin yar halak yanzun nan nagama zancen kifa a raina wallahi tun shekaran jiya ba muyi waya dake ba. Wai kina inane yanzu ko kin samu tafiya sokoto din ne na tambayeta don mu katse zancen data dauko din a lokacin nasan tana iya bata muna lokaci da surutunta a hakan. Wallahi ina gusau dai ban tafi sokoton ba har yanzu don wanda zanbi din baizo weekend ba nace kai hanne akwaiki da son banza yanzun don dan kudin motan da zaki biya kike garin nan nan har yanzu ? Bayan kin sakawa gwaggo ran zuwan ki yanzu ki zauna kina jiran bati a nan tace ke an fada maki kowa irin kine da Master ya kamawa kina yadda kikaga dama. Humm wani master ni dama na kira najine idan kina gari akwai zancen da nake son muyine dake don abin ya daure min kai sosai wallahi. Da sauri naji yanayin muryanta yai kasa tana tambaya meke faruwa kuma zahra nace sai kinzo zakiji komeye but kada ki damu ba don ba komai bane mai yawa. Da haka muka kashe zancen da ita akan washe gari zata shigo wurina mukai sallama ta kashe wayan har lokacin ina faman sake sake a zuciyana nako in fada mata ko kuma nayi shiru kawai in bar zancen a ckkin raina. Saidai wanan zancen tafi karfin na barwa cikina shi don in dan tuntubi wani inji wani shawara zan samu na sake cusa kaina gun uwar mijin nawa da nake ganin hakan shjne mafita a lokacin. Sun fito daga lectures yana sauri ya koma masaukin su don azumin daya wuni dashi a bakin shi ga azumi ga kuma faduwan gaba da yake ji a ranan yana damun shi wanda hakan yasa shi kara zama shuru a lokacin. Ya iso gidan da suka kama suna zama shida abokin shi babu kowa haja yasa ya bude dakin ya shiga ya samu wuri ya kwanta don akwai sauran lokaci da zai dan gangara bakin titi ya dan sayo abinda zaiyi buda baki dashi lokacin. Barcine ya daukeshi a hakan ba tare da niyar hakan ba a lokacin can ya fara mafalki da ya bashi mamaki don mahaifin shine ya gani a gaban shi yana tsaye nisa dashi kadan . Sunawa juna kallon kallo kafin yaga ya miko mashi hannu alaman yazo gareshi sai yaga wata mace tazo da sauri ta shiga tsakanin su yana ganin hakan shi kuma juya ya bar wurin da sauri kafin mahaifin nasa ya farga da hakan . A daidai lokacin kuma ya mike zubur daga barcin nasa tare da wani irin zufa dake karyo mai duk da yabar kofan dakin nasu a bude amma zufa yakeyi har yana tsiyayo mashi ya jike sharkaf duk jikin shi. Zai iya cewa wanan ne karo na farko daya taba mafalki da mahaifin nasa irin haka sai abin ya fara bashi mamaki gashi shi kadai a dakin nasu lokacin. Macen nan fara da yaganine ta fado mashi a rai yake mamakin ita kuma wacece a garesu datazo ta shiga tsakanin su a lokacin da baisan abinda mahaifin nasa keda niyar fada mashi ba. Daba don yamma yayi a lokacin ba da zai koma barcin ko zaiyi sa,a yaci gaba da wanan mafalkin da baisan dalilin zuwan shiba gareshi a wanan lokacin. Haka yasha ruwa a dadare ranan bai samu tabukawa kanshi komai ba don ko dan karatun da yakayi bita a lokacin bai samuyi ba don yadda yake jin kanshi cikin damuwa a lokacin. Waya dai ya samu yayi da sahibarsa Zahra yaji lafiyanta dana mutanen gida a bakinta a nan take dan fada mai zancen bukin da za,ayi a cikin gidan nasu da suke kira da babban gida a wajensu. Take ya katse ta da zancen yana fadin Zahra kibarsu da bukin su don mutanen nan ba kaunata sukeyi ba zahra kinsan sani ba wanda cikinsu da yake nuna damuwan shi a kaina don haka kija nisa dasu kamar yadda nima nake nisa dasu a yanzu din. To amma Master kasan akwai hakkin zumuci tare da hakkin makwabtaka dasu ba zasu dauki hakan da laifinsu bane sai suga namu laifin ne a yanzu. Haka kuma Allah ba ruwan shi da wanan dalilan donshi ya sharada da ayi zumunci a tsakanin zumu kaga hakan sai, , , Zahra ki barsu idan lokacin yayi zamuyi zumuncin dasu amma ba yanzu da suke muna kallon fakirai ba a idanun su. To shike nan ta fada a sanyayye yadda tai maganan yasan zancen bai mata dadi ba a ranta amma gudun bacin ranshi yasa ta amsa mashi kamar yadda yake son ayi. Irin wanan halin nata yasa yake kara jinta a rashin don zahra ta daukeshi a na gaba da ita sosai yake jin sonta a ko yaushe yana kara shiga zuciyar yadda bata nuna cewa ita din mai gatace fiye dashi a zaman su na aurataya tana tsayawa a inda ya ajeta a rayuwan ta.
Chapter 154 · 0% Book details