Sashe 157
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
naji gidan shiru. Muna nan wallahi innace dai tun safe take can yanzun ma Asma,u ta dawo take fadin wai inna tace maza mu shirya mu zo za,a fara Dj . Dj kuma hannatu ta fadi hakan cikin mamaki koni naji wani iri yadda tai maganan nayi saurin fadin ba bukin gidan su akeyi ba keko taso ace nata sunje mana koni don Master baya garine aida tare zamu dasu. Nace don Allah ko iron dinki na kusa in dan goge tufafina kafin nepa su dauke wuta nace eh yana nan dama ke baki gogeba tun jiya bayan kinsan yau akwai buki ? Nifa ba wani damuwa da wanan bukin nayi ba dama mutanen da sukewa mutane kallon banza balle kaje sha,aninsu yaya ke nan kuma idan mun kai kanmu cikinsu. Haba dai keko har zaki yarda su raina maki ai shiga ta kamala zaki dinga yi idan zaki shiga wurin wanda kikasan akwai makiyan ki. Murmushi tayi tana fadin inna dai tayi ita don ta saje dasu amma mukan ai wanda suka san mu dashi zamu sa mu fito kinga kuwa dole su raina muna wayau. Ina zuwa na fada na shiga daki na barsu a nan ina ciki naji muryan Asma,u tana fadin kizo muci abincin mama Aisha. Ke haba mana keba kanwarta bace daba zaki kirata da Anty ba ko yaya ai an daina irin haka ku kuwa sai a daukeki bakauya ko wata bagidajiya can. Baki yarinyar ta turo tana shirin mata rashin kunya lokacin na fito daga dakin da kaya a hannuna naganta a tsaye daga kofa. A,a Asmau kema baki tafi bane eh ban tafi dazun dai na leka da Dije ta aikeni shine inna ta bani abincin in kawo muci kuma abincin ba yawa dan kadan ne tazo muci yunwa nake ji sosai tana ja min rai. A,a baga abinci a nan ba ku diba na dauka aikun tafine ba kowa a gidan shiga kitchen ki dibi mai isan ku kuci tayi dan jim kamar tana tunane sai kuma ta juya ta tafi . A nan na zube kayan dana dauko ina fadin Aisha ki duba wanda zai maki a cikin wanan sai kiba Asmau sauran kala bibiyu ne na zabo masu lokaci guda. Don ina da kaya birjit a dakin daba amfani nake dasu ba yanzu a cikine na debo masu wa yan nan din yanzu. Da sauri ta washe baki tana fadin wai da gaske matar yaya nace da gaske mana gwada ki gani ko zasuyi maki idan kun dawo saiki goge wanan din kada inna tayi fushi dake bakuzo wurin sha,anin da wuri ba. Takai hannunta saman kayan ta fara dubawa tana nuna farin cikin ta a fili tare da fadin ke Asmau taho kigani an bamu kayan da zamu saka mu fita. Saiga Asmau ta bude labulen kofa tana fadin kizo kiga abincin ko zai muna nikan bancin wancan da anka bamu don wanga mai dadine sosai harda ganyen salad cikinai hwa. Sai idon ta ya sauka akan kayan da yar uwan nata take duba tace kayan waye taho nice kigani matar yayane tabamu su mu saka. Da sauri ta sake labulen ta shigo tana fadin mu ankabasu walle har naji dadi kasan raina muma zamu hito kamar kowa a bukin nan ashe ? Ai dama daidai da kowa kuke idan kuna gyara Zahra kan bata da matsala in kuna hurda da ita fiye da hakan ma sai ku samu a wurin ta don wanan ba komai bane wurin zahra kowa yasani . Ai walle innata taka hanamu hurda da ita dama wai sai ta mayar damu bayinta Asmau ta fada tana bude kayan kafinta washe baki tana fadin wayyo ji irin dinkinga da nai maitanai a baya don Allah. Ke walle nika daukane bake ba wanga ina zai maki adaidai lokacin naji hanne tace bayi kuma don kana shiri da matan yayan ka shine wani abu kuma ? Ai shina gani daka zowa muna dan hira halan ta mayar dani boyantana to nidai haka niji inna tana hwadi ko wani lokaci. Yanzun dai ku shirya nayi maku kwalliya sai ku tafi hannatu ta fada sai sunci abinci aiko na fada daga inda na zauna. Abinci walle saina dawo nikan saina dawo nikacinai kedai aje muna har mu dawo daga wurin bukin Aisha ta fada a cikin zumudi sai hannatu tace ai gara kuci kada kuje can baku samu wani abincin ba. Hakan tayi masu kwalliyan tana jansu da hira nima ina dan saka baki wanda na kula da hakan yasa sun dan sake jiki sosai a wanan ranan dani har muna wasa da dari a fiye da kullun a cikin wata takwas din da nayi a gidan tare dasu. Wanda hakan ba karamin dadi nima naji ba don har akalma da jakka da gyale suka saka mukai masu rakiya hannatu nata zugasu Dijema saida ta fito don jin yawan hayaniyar mu da takeyi daga sashen su. Bayan tafiyan sune Hannatu ta gama yiwa Dije dan bayanin karya tana fadin ai kaka yan mata yanzu saida sa,oin su a gida suke gyaruwa amma a zauna ga zahra tare dasu muma na nisa muna cin muriyanta balle wa yanan dake zaman kannenta ai zaman lafiya yafi komai a rayuwa. To shina gani yar nan uwarsu taki gane hakan gashi yau yar nan da take rainawa itace tayi tsaye ta gyara mata diya haka tsab zasu shiga tsaran su don wanan sha,anin ba lamarin wasa bane don kowa na wurin a cikin danginsu kinga ko aga naka cikin shiga ta alfarma ai abin a yabane hakan. Tagama zuban ta ta dawo ta sameni ina gyaran part din ta kalleni tace to uwar tsabta koda zaki hakan ki dinga bari dai sai sun tafi don idan kina nuna wanan shagen tsabatan naki a gaban su haka zasu dauka kina kyaman tararyanki dasune. Banyi magana ba don nasan gaskiya ta fada min saidai ba zan iya ganin wuri haka komai a yamutse ba dole sai na gyara zanji dadi amma dai zan kiyayye din gaba. Mun dan taba hira ta wuce ina mata godiya na rakata zuwa waje a nan mukaga yadda jama,a suka cika unguwar don halartan wanan bukin mukai sallama ta tafi na dawo ciki nayi sallah na fito wurin Dije na zauna muna hira. A nan ta jefo min tambaya da fadin yaushene mijin ki zai dawo daga tafiyan shi dan murmushi nayi kafin nace ina ganin sai karshe wani mako kamar yadda yace. Saidai zuciya yana ban kamar zai dawo kafin lokacin yadda nake gani yar nan har ganin dawowan mijin naki kikeyi a yanzu sai nayi murmushi ina dan kame kame tare da fadin . A,ahaa kawai dai ina jin cewa zai dawo a yan kwanakin nan ne don haka jikina ke bani ta kara tuntsurewa da dariya irin na tsofi lokaci guda. Shigowan wasu mata wurinta ya dakatar muna da maganan suka tsaya gausawa da ita saidai ina zaune wurin har lokacin da suka fita bayan sun dan taba hira. Fitan su take fada min irin alakansu dasu akwai zumuci sosai a rsakani su na iyayye wanda a yanzu mutane basu daukan hakan da muhinmanci sosai shi tallaka yana gudun wulakancin da uwa mai kudi don wullakanci. Haka dan uwa mai kudi kuma yana gudun mamuwan dan uwa tallaka don bani bani don wasun su haka suke zubar da kiman su da roko a yadda Dijen ke min bayani kuma hakan gaskiyane a yanzu. Muka dauko hiran zaman mu da uwar mijina tana kara ban hakkuri kan halayen da take nuna min na dai nuna mata ai uwace a gareni don haka ba komai. Muna wurin misalin karfe biyar na yamma kawai Ahmed ya fado muna gidan kwatsam muka ganshi kamar an jefoshi a lokacin. Daga inda nake zaune ina hango bacin rai a fuskan shi ganin part din mu a rufe don ya dauka na tafi wurin bukin nasu daya hanani zuwa kenan tunda ga part din namu a rufe don yasan bana shiga cikin gida in zauna haka. Yana nufo part dinsu Dije din yai arba damu zaune tare da Dije din saman tabarma ya dan saki wani shu,umin murmushi a fuskan shi lokaci guda. Mukai mashi sannu da zuwa a nan ya zauna na mike karbi dan jakar nasa da yake rataye a kafadan shi na nufi part din mu dashi a nan naji Dije din na fadin. Allah ya horema mata mai halin kirki yarinyar akwaita da dattako da sanin yakama ka kara rike yar nan da hannu bibiyu don ba inda ta kasa da kai haka Yayi murmushi tare da fadin kai Dije ai nima ina da wanan halin irin nata kaidin shu,umine wani lokaci don wanda baisan kaba ya hauka katkace sai ya zame.