Sashe 204
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
tazo ta dauka har lokacin suna tsakar gida tsatsaye Aisha na basu labarin abinda idonta ya gano mata a wajen. Ta dauka ta fito dashi zuwa waje inna tabi da kallo don ba wanda yasan saitin kayan jug din kaf gidan nan na fito na samu Dije tana godiya ga Allah na wanan ranan tare da fadin. Dama malam yana fadin wata rana zai dawo zai dawo nan ko son dansa mu daiyi hakkuri lokaci na zuwa yauko ga zancen nasa ya fito don ko gashi da kafanshi yazo don dansa. Butocina Aisha ta shiga ta dayko ta cicika da ruwa ta fita dasu nikan nabi jikin bango na lafe ina kallon re action din kowa a gidan mu samman inna data kasa zaune ta kasa tsaye kan zuwan nasu. Ganin tsayuwan ba zai mun ba yasa koma part dina ina tunane ta hanyan hayewa kujera na na kwanta ba abinda nake tunane sai hiran da master yai min kan mahaifin nasa duk da nashi hakkuri akan baisan uzurinsa nayin hakan gareshi ba. Amma nasan hakan baisa ya sauke kudirinshi a kanshi don bana jin kalami mai taushi akan tsohon a bakin shi ko yaushe zance irin haka abinda yake fadi dayane shine baison suma hadu dashi ga baki daya. Idan nace ya daina fadan haka don Allah mahaifi mahaifine sai tace bari zahra baki san komai ba ke don Allah kawai dai mu tafi a hakan dashi shike nan. Yau kuma sai gashi Allah ya kado munashi garin saidai master din bayanan a wanan lokacin gabana ya fadin don tunowa da nayi da cewa idan mun boyewa su Dije inda yaje yanzu ai ba zan boyewa mahaifin inda yake ba. Haka na zauna inata tsara mezan fada masu da zaiyi kama da maganan farko Aishace ta fado dakin tana fadin Dije tace kibada wuri a saka masu fura da aka sayo masu gidan mai dawo. Nan na mike muka shiga kitchen tare muma nemo waje muka juye furan aka dora saman wani ture din golden ta fita masu dashi inna ko ban kara ganin giccen taba duk lokaci tana daki she waya takeyi . Can naga ana shigowa da tsaraba irin kayan hanyar abuja sak don mahaifinmu ya saba sayowa muna gani da subutan baki nace gasu kamar sun fito Abuja mana ? Wani Abuja suda suka fito can nisa akace kusa da fita Najeriya zaki wani ce Abuja kuma Asmau ta tareni da fadin hakan a lokacin ne mukaji sallaman mutane zasu shigo a zaton muma sune zasu shigo sai mukaga. Yan uwan mahaifin su innane sune suka shigo lokacin duk da dattije nai amma idon su akaina hakan yasa na tsargu duk da shigana lokacin ba laifi ina cikin suturana mai rufe jiki. Gaishesu mukayi suka nufi wurin Dije nikan a lokacin na shige part dina na rufo kofana don ban ma son naji kome zasu tatauna a lokacin sai gasu Aisha sun biyoni ciki suma. Nan muka zauna dasu Asmau na fadin ji munafukai basu zo gidan nan ba saida gulma ya samu sunji ance manyan mutane sunzo sunzo su samu canjin kashewa shegun matan su. Kai Asmau halin nan naki baida kyau wallahi iyayyen naki kewa wanan kazafin na fada a cikin daure fuska gareta . Tace barsu anface sune suka kashe auren inna da mutumin nan da badon suba da yanzu muma shine mahaifin mu ai suka kwafsa muna. Kallon takaici muka watsa mata lokaci guda don jin abinda ta fada din game da tsofin na takaici nice nace baki san wani baya haihuwan dan wanu ba dama haka Allah ya tsara abinsa.[6/19, 8:05 AM] Mmn Bibo: 🌱TUMFAFIYA UWAR KWANKWANMAI ,,,,,,,,,, 🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,, 🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH ,,,,,,,,,, ZAINAB IDRIS MAKAWA 7️⃣5️⃣ ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA AMIN,,,,,,,