← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 286

Sashe 45

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fita part din mu suka hade da Aisha wace ta kara biyo sawun su kabir ne yace waitin you come do here amebo ? Stop calling me that yeye name i tell you say i no want that name amebo you na de call me with it! Nobe amebo you come do ? why you de follow us like small kids any where we go har suka shiga part din mama suna fada haka dashi. Mama wace bata son ran diyanta ya baci ta kasa boye bacin ranta a zuciyarta ta hau Aisha da fada haka yaja ran hjy Rafat baci don tasan halin mama irin wanan wajen don bata kaunan ran yaranta ya baci sam. Saidai duk abinda sukai maka kayi hakkuri amma idan kace zaka rama a gabanta zaku samu matsala da ita duk yadda kuke kuwa da ita. Don mama irin matan nan ne masu ririta diyan cikin su fiye da komai a duniya kema uban wa yace ki bisune bayan kinsan halin kabir sarai ba kyaleki zaiyi ba. Hjy Rafat tace kabir kasan uwarsu bata son a taba mata yara don gudun irin hakane fa banso ka biyomu ba kanace sai kazo arewa kaima ka gani. Gashi ance kunje part dincan kun tare har kuna cin abinci tare da zarah a plate daya da ita kallon Rukkaiya yayi yace mama shiyasa nace yaran nan naku munafukaine wallahi. Ni sun sani sun san halina idan yarinya ta kawo min raini yanzun za ajimu da ita ba ruwana da wai maman jafar bata son ayi masu mussu yanzu zanwa yarinya one below seven die. Ganin abin zai iya kawo masu matsala don tasan halin kabir sosai baida kunya ko tsoro irin roget din lagos dinan ne shi don ko kallon shi kayi zaka fahinci koshi waye don kanshi ya tara wani irin suma hakama kayan jikin shi irin na shegun Lagos ne yake sakawa. Sabanin dan uwanshi da ba ruwan shi shiru shiru yake shi ko halin irin na yayan farine ke binshi oho mama din ne tace mai ai ina ganin kaikan kabir wurin damben kokuwa zamu kaika kawai turai mu huta da haka suka wasance wanan zancen. Da suka kebe da uwar tasuce take kara masu fada take fadin kai Dele ka cire ranka ga yarsu don komai ya kara rikicewa yanzu gidan nan ga baki daya don dukkan ku nan kunsan halin mami jafar ta tsani wa yan nan mutane sosai. Ba zata taba yarda a hada ka da zarah ba yanzu ma kokarin hadaka da yarta Aisha naga tanayi bayan ta sani sarai zarah din kakeso ba Aisha ba. Duban uwar yayi ya nuna kanshi yace wani mama na auri wanan yaran da basu da tarbiya ko kadan nerve kada ki soma wanan zancen dani don ni zarah nace ina so tun tana karamar ta. Ba zaka auri zarah ba na fadama kada ka bata min zumuncina da kawata kan wanan bukatab naka don haka ka duba tsakanin Aisha da Rukkaiya ka zabi daya. Ohh really mum da baki kinki ke fada min haka yau baya kinsan iri son da nakewa yarinyar nan zarah a raina ? So so suma zaka so su ai idan ka zabi daya daga cikin su OK ya fada ya mike ya fito daga dakin kai tsaye haraban gidan namu ya nufa tsaye yayi wuri daya idanun shi a rufe kafin yaji motsi ya bude idanun nasa. Nice a duke wurin motana ina daukan abu sai kanwata karama dake gefena tsaye tana surutu kusan kamarmu daya da yarinyar na dago ina rufe motar tare da riko hannun yarinyar muna shirin barin wurin da takardun dana dauko a hannuna daga cikin motar. Takowa yayi zuwa inda naken ganin shi ya dan sani kaduwa lokaci guda zan iya cewa wanan ne ganin murmushi a fuskanshivtun zuwan su gusau din na da sukayi. Hannun yarinyar ya riko yana fadin meye sunanta kafin in fadi ta amsa mai da yusurah ya dan rage tsawo yana fadin sunan ki nada dadi sosai. Kafin ya dago yana kallona tare da fadin nice name naso su yarda muyi aure amma saboda maman jafar hakan ba zai samu ba a tsakanin mu. They are telling me now wai na zabi Aisha ko Rukkaiya na aure mamadin ke ni kuma zuciyana ke yake so zarah ba suba don su din ba zabina bane zabin su mami ne hakan. Gobe zan koma da safe in sha Allahu ina son ki dauki layina a wayan ki don ina son muyi zumuci a tsakanin mu har yayan mu nidake saboda kada alakanmu dake ya yanke. Duk wani abinda ya sameki don Allah zarah na rokeki kirani zarah muddin ina raye ba zan taba barin ki wahala ba yadda suke nufi a duniyan. Idan sun hanani auren ki ba zasu hani zumunci dake ba na sani don ba zasu taba sanin ina taimakoki ba wanan alkwari haka nayi maki zarah. Ki natsu kimaida hankali ga karatun ki don ki zama wani abu a cikin rayuwan ki yadda zaki taimaki mahaifiyar ki da yan uwanki nan gaba ina maki fatan alheri a rayuwan ki don sun rabani dake yanzu. Ki mi alkawarin zaki cika min burina na taimakonki a kaina nan gaba don ba karamin shiri akewa rayuwan ki ba zarah shine dalilin da basu son kasancewana tare dake a yanzu na gama fahintar komai daga garesu. Saidai basu san cewa kedin kinci sunan ki na Zarah ba kin daga sama fiye da diyan da suke son su dago din na barki lafiya sai in Allah ya kaddari haduwan mu ya miko min katin wayan shi da address din shi na dago ido da hawayen daya fara sauko min a idona ina kallon shi. Suka zubo lokaci daya dan murmushin yake da baikai ciki ba ya sauke a fuskanshi yana fadin don't worry take care kada ki bari su san muna tare ina taimakon ki. Daga haka ya sake hannun yusura yana fadin bye ya tafi na bishi da kallon mamaki har ya shige inda dakunan samarin gidan suke inda a can ne aka saukesu suma. Cikin wani irin yanayi na shiga gida Allah ya taimaka ummah bata falo na samu daman shigewa ciki na fada saman gado ina sake hawaye masu yawa. Ban taba soba ban kuma fara ba saidai kalama brother Dele din sun tsaya min a raina sosai don na kasa raba dayan biyun kan abinda yake kokarin son in fahinta daga zancen shi din . Washegari hargowan su mamane ya tayat damu daga barci wai Dele ya bace tun asubahi an nemeshi a rasa kuma ya tafi da kayan shi bai fadawa kowa inda zai tafi ba. Dole ba shiri suka shirya tafiya suma a ranan da cewa zasubi bayanshi don me yuyuwa ya koma lagosne ya barsu nan su zaman me zata zauna yi a garin mutane bata san halinda dan yake ciki ba . Dole muka fito wajen nasu da zasu tafi ita da drivern su da danta kabir mama sai waya take faman yi da Abba tana sanar mashi halinda ake ciki. Abbah din a karshe yace su tafi da mama suzo nan sokoto subi jirgi zuwa lagos inyaso sai driver ya koma da motarsu shi a nan mama ke zage zage tana fadin akan wata yarinyar banza can yaro yana neman halaka kanshi. Duk wanda ke wajen zai fahinci a fakaice mama ke sake magana da wani a wurin duk da bata fito fili ta ambaci sunan wanda takeyi dashi ba wurin amma kowa ya gane hakan. Kara lafewa nayi jikin motan danake tsaye kusa da ummah da itama ido ta zubawa mama dake faman sakin magana a cikin habaici irin na kwararu iya habaici. Cikin gida suka kwasa suka koma suka barmu a tsaye waje yayin da yaranta ma suka mara mata baya lokacin guda kabir ne daga inda yake tsaye yana magana da drivern su ya tako zuwa inda nake tsaye ina rike da hannun yusura. Baby kema kin damune don nasan ya fada maki komai jiya ai don na fito na biyo bayan shi na sameku tare saina koma ciki. Amma kada ki damu fa ban fadawa kowa hakan ba do kada na jefaki cikin matsala irin nasu maman jafar gaskiya zan fada maki matan nan bata son ki keda maman ki. Ta sani sarai brother Dele ke yakeso kamar yayi hauka amma yanzu munzo kan zancen ku ta dauko zancen hadi da yarta ta kawo mashi shine dalilin da yayi fushi ya tafi ya barmu nan. Amma kinsa da ace nine yau da sun gane basu da wayau a garin nan amma shi yana da sanyin hali sosai kinga ya tafi ya barmu a na ita mami tasan halinshi idan yai zuciya zai iya barin kasa nan ga baki daya yanzu haka shiyasa kikaga sun tayar da hankalinsu haka. Ummah ce ta juyo inda nake tana fadin dauki Yusura mu koma ciki ta kalli kabir tana fadin Allah ya kaisu lafiya ya amsa da amin nima kallonshi nayi ya rigani fadin ban layinki sai mu djnga gaisawa. Na karanto mai number na yayi serving mukayi sai watarana na juya na shiga vida don ummah har ta shige ko a lokacin ita. A falo na samu ummah zaune ranta a bace sai hankalina ya tashi sosai ganin yanayin ta kallona tayi tana fadin maamah zoki zauna kuma ki fada min gaskiya don banson karya kin sani. Wallahi umma zan fada idan abinda na sanine zaki tambayeni a kanshi tace dakyau me kika sani game da tafiyan yaron nan kuma meye hadin ki dasu ? Ummah ni babu komai a tsakanin mu ku ban san komai a kantafiyan shi ba sai jiya daine yake ce min na kawo duk yadda mukayi dasu tundaga farko har wanan maganan da kabir ya fada min a waje na fada mata komai. Oh wanan dama take kullawa naso in fahinci hakan amma sai na dauka kawai hakan shakuwane a tsakanin ku amma ai ita hjy mama din tayi kuskure tunda ta mata da Allah ke komai ga bawanshi. Idan shi Dele din ya kasance mijinki ita bata isa ta hana hakan ba sai anyi balle ban fatan hakan a gareki a samu abin fadi cewa kin
Chapter 45 · 0% Book details