← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 286

Sashe 83

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

son nayi barci da wuri jiya din. Allah ya tsare ta fada ba tare data dago kai ta kalli inda nake ba na kara dago kai na kalli su Aisha nace to ni zan tafi sai nadawo ke nan ba wace ta juyo ta kalli inda nake. Na fice ina komawa part din mu wanka na shiga ashe fitana part din mama din ta fara fada tana fadin munafucin banza da wofi ansan munafuncin da aka kula da zai kaini can din wurin su Abba din. Mama saude ce tace anya ba da wani manufa yarinyar nan zata Abujan nan ba nifa tun farko shiyasa nace a barta da zancen yaron nan data nacewa. Amma kin nace sai kin kula mata wanan sherin son kamal yanzu ga kamal din shima ba ganin shi kikeyi ba akai akai. Anty tunda kamal ya yarda yana sonta ai gara in hadata dashi shegiya inga bayanta har uwarta don dole su zauna a karkashina innuwana sai yadda nayi dasu har kamal din. Kina ganin ubanta ko uwarta zasu yarda da wanan zabin naki kuwa idan sun gano kudurin ki akan yarsu mama din ta tare da fadin ta yama zasu gane cewa ina hada wanan plan din. Idan hakan ya faru aishi kamal yafi kowa cin riban harkan dan iska zai samu zukekiyar yarinya irin haka a bagas. Murmushin gefen fuska mama ta sauke don tasan irin mugunta data shirya min wanda ba lalai bane ta fada a fili sai gurinta ya gama cika za a san manufarta akai. Mun iso Abuja lafiya wani sabon driver ya turo ya daukeni airport muka isa gidan babu kowa a gidan lokacin wai suna wurin aiki dukkansu lokacin. Sai yan aiki ke sintiri a cikin gidan falon gidan da yanzu ya sauya sosai nabi da kallo ina jin wani abu na taso min a kasan raina. Dakin da yake mallakin ummahna a da yana kulle shina kalla na lumshe idanuna ina jin wani zafi a zuciyana yana kuna min rai. Wanan dakin da ada muke sauke baki a cikin shi naga an bude min waina shiga shine masaukina banyi kasa a gwiwa ba nace. Wanan ba shine dakina ba ai don ina da daki a gidan nan dama shi Abba ya sani wai waye ne me take fadane wai wata murya dake fitowa ta fada a bayana. Dan juyowa nayi ina kallon inda nake jin muryan wata mace ce da ba zan iya fadin ajin da take ba ko budurwace ko bazawara waye ita me take fadane wai ? A,a bakuwar da Alh ya tura na dauko airport ne dama shine take fadin wai ba zata shiga wanan dakin ba dama tana da daki a gidan nan. A,a to ta fada taba ashe zakisha zama a nan to inane ma dakin naki a cikin gidan nan dama shiru nayi ban kalleta ba ta juya tana tsuki ta tafice gidan tana fadin kaga ka barta a nan harsu dawo idan ba zata shiga ba. Komawa nayi saman kujera na zauna ganin hakan ya fice daga falon sai yan aikin dake sintiri suke gaidani jefi jefi ina amsawa har barci ya daukeni a wurin. Ban falka ba sai da la,asar tashi nayi ina son inyi sallah kitchen na nufa wurin yan aikin nasan komai nagidan namu don haka mike nufin baya naso shiga bandakin dake baya din amma yana rufe shima a nan wurin su nayi alwala nadawo falon nayi sallah. Bandaga ba daga wurin hjy karima din ta shigo tana fadin ina daughter na din take sai ta hangoni a zaune ina addua ga akwatina a gefena aje . Ya haka naga kayan ki a nan bayan na fada masu dakin da zasu saukeki a ciki idan sun iso saida na shafa nake ce mata sannu da dawowa mummy ta amsa min ta sake fadin wai basu kaiki dakin danace bane ? Dakin baki suka kaini nikuma nace masu bashine dakina ba don haka ban shiga wanan din na fada kai tsaye a daidai lokacin da Abba shima ya shigo falon ke nan. Kallon mu yakeyi tunkan ya karaso lafiya bata shiga daki ba ya fada nace Abba ba dakina aka kaini ba ni kuma ban iya kwana ko wani daki gidan nan idan ba nawa ba kasani. Mama meke damun kine da zuwan ki ko wani daki aka kaiki yanzu ai shine naki tunda ba ummah ki bace a gidan nan yanzu. Ba zan iya kwana ba Abba na fada cikin rashin damuwa zaiyi magana tace kaga Alh dama wanine dakin nata wacan dayan da kike zama shine nata dayan kuma na uwarta sai wancan dasu hafsat ke ciki yanzu kannenta ke zaune a ciki dayan na mai aikinsuce. Bari a sauketa a nata din tunda ban faye shigan shi ba dama ta fada kai tsaye ta kira yar aikinsu Tabitha tazo tace takai mun kaya a dakin tana fadin dama tun da kika iso kina nan falo zaune ? Mummu ban iya zama ko wani daki sai wancan din na fada ina mikewa nabi bayan yarinyar da taja min kauyan zuwa ciki komai nawa an kwashe a dakin saina mummy din akwai gado da mirro da kujera. Na aje jakar hannuna a kujeran dakin na shiga bandaki wanka nayi na fito na bude jakata na dauko riga na saka na shafa mai ina shirin naji an turo kofa mummy dince ta shigo dakin. Yanzun hankalin ki ya kwanta ko ni har kin tayar min da hankali wallahi kan hakan zakiki shiga daki ki zauna a falo yanzu tunda naga kinyi wanka taso muje falo kici abinci. Mommy banjin yunwa na fada tace me kikaci nace nasha cock da snack da muka iso sokoto dama haka kike wasa da abinci daughter a, a nace tace taso muje ki danci wani abu. Banyi musu ba na mike nabi bayanta muka fito falon zuwa lokacin itama ta sauya kayan jikinta zuwa rigan shan iska. Baya na dan tsankwara ne na koma daki ban sake fitowa ba don haka a ranan ban tantace iya mazauna gidan ba a lokacin har na kwanta wayana ya dauki kara na duba Ahmed ne ke kirana na dauka muka gaisa. Yayi min ya hanya na bashi amsa da lafiya kalau nace yasu kaka Dije tana nan kalau sai nace aff wai kasan naga akuyarka kuwa a cikin mamaki yace a ina ? A cikin mafalkina wallahi na bashi amsa nan na kwashe yadda mukayi na fada mai komai shiru naji yayi kafin yace ke nan uwargarke tana raye a wani wajen ?
Chapter 83 · 0% Book details