← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 236 OF 286

Sashe 236

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakin yayi tsit baka jin motsin kowa a lokacin don ko haraban asibitin yayi tsit sosai a lokacin Abbane ya kallo inda mama take zaune yace. Mamakin zancen wanan yaron ya hanani barci don indai dan gaske dana sani wanan mai arzikin mutumin dake da motoci da gidajen haya a Abuja shine mahaifin yaron nan da gaske abin nasu akwai daure kai ke nan a cikinsa. Abinda nake nazari daya tsaya min a raina maimuna shine ke nan ita salma da yarta sunsan da hakan suka boye muna kome hakan yake nufi yanzu ? Sai lokacin mama tayi magana tace Alh makircin Salmane kuma baka sani ba wanan matar mai tsaban jinin makirci kaga har yar nata ta koyawa wanan halin ke nan zurfin ciki da iya shiri ga salma kamar matan farko take a wurin iya tako. Kai anya ban tsanmani sunsan da hakan suma gaskiya don da salman ta fada min kota fadawasu musa a lokacin suma dai ina tsammanin daga bayane suka sanda hakan kila. Au baka yarda ba ke nan da shirin salma ko ai salma zata iya aikata fiyema da hakan nidai ina tunanen bandan cikinsa bane kila dan wani dan uwasa daine na kusa yake son yayi amfani da sunansa yanzu din. Wanan mutumin yadda naji kana kwatantawa ina zai auri mace irin wanan don da gani arzikin nasa kamar na gadone don haka inama zai hadu da wanan matar anan ya aura. Abba din bai kara magana ba bayan hakan daya fada yaci gaba da nazarin da yakeyi a cikin zuciyarshi na shi kadai don yana son ya natsu yayi tunane a kai alokacin. Mama bata iya barci ba a ranan don wanan maganan da taji yazo mata a bazata sai sakawa take tana walwala da kullawa a kasan zuciyarta a daren ranan gashi a asibiti suke tayi data sanin kwanan da tayi asibitin a ranan . Garina wayewa tace gida zata tafi gashi duk iya kokarin ta na son ta boye bacin ranta takasa hakan saida aka fahinci halinda take ciki lokacin. Har Abba ke fadin ke kuma meya faru dake haka naga kin fita cikin hankalinki ko kwanan asibitin ne ya taba maki zuciyarki kika koma hakan. Tsuki taja tana fadin wanan wuri aiba wurin da mutum zai zauna bane har ya saki jikinsa gida zan koma nadan yi wanka in huta kafin rana in fito da haka tabar asibitin ranta na mata suya tun a cikin mota ta fara kiran yaranta da su hadu gida gata hanyan gida din yanzu itama. Tambaya suke hankali tashe don sanin mahaifinsu na asibiti kwance a lokacin sun dauka wani abune ya sameshi don kiran safe yana nunawa mutum ba lafiyaba a lokacin saboda mafiyan kiran safe tashin hankaline. Karfe daya saura ya dawo gida tun daga bakin layin nasu babu kowa a lokacin don dare ya soma rabawa a lokacin kowa ya samu wuri ya natsu sai me lalura irin nsa daya hadu dasu mutum biyu bai kara haduwa da kowa ba kuma. Saidai abin mamaki yana tura kofan gidan su ya shiga yayi tozali da uwargarke a kwance kofan mu kamar tana gadin wurin duk da yadda yake jin zuciyan shi ba dadi hakan bai hana ya fadi cikin mamaki ikon Allah uwar garke kece nan kin tsukene yau kika dawo nan kina gadin mu kuma. Kamar taji meya fada sai kai ta dago ta kalleshi ta mayar ta kwanta shi kuma yana kokarin rufe kofan gidan dake bude kodaya gama ya juyo sai ya samu ta daga daga wajen ta nufi hanyar bandakin da ake dauresu. Hakan bai bashi mamaki ba ya dai shige ciki ya rufo namu part din don yasan babu inda zata koda ba a daure taba a cikin daren nan tunda gidan rufe yake. Ya samu na rufe kofan amma turawa kawai nayi don ban zaci zai kai wanan lokacin haka a can ba bai dawo ba don haka na kwanta sai gajiya yasa barci ya daukeni a nan falo inda nake dakon dawowanshi. Baya ya rufe kofan ya shige ciki ya gama abinda zaiyi sannan ya dawo falon ya tayar dani muka shiga ciki kowa nada gajiya don haka bai matsawa kansa da nemana ba a ranan. Washe tunda safe na dora girkin da zai tafi dashi asibitin karfe takwasa na safe duk na gama ya dauka ya nufi asibitin don ya kai masu. Bai samu kowa a wurin Abban namu ba a lokacin don hamzan da mama ta barshi dashi ya dan fita waje ya busa taba yabar Abba din a dakin shi kadai a lokacin Ahmed din ya shigo. Suka gaisa ya tambayi lafiyan jikin yace yaji sauki sosai don ya samu barci a daren jiya sosai ba kamar kwanakin da suka shude ba. Nan ya zuba masa shayi yana sha suna dan hira jefi jefi dashi a zuciyarshi kuma yana mamaki mutum kamar Abba za a bari shi kadai a dakin asibiti ina iyalinsa suke don yasan ya bar mama asibitin dare jiya kafin ya tafi. Aka turo kofa ummah ce da yaran data hana zuwa school ranan don su samu zuwa gaida Abba din nan suka shiga gaisawa da juna tanawa Ahmed din ba,a da fadin. Kai wanan matar taka da rawan kai take wai ita har ta gamawa Abban naku abin kari ta rigamu kawo masa ke nan ato su sukasan zafina fiye daku bagashi har yazo dubana ba ku kuna gida. Wallahi bansan hjy maimuna ta koma gida ba ai ni duk daukana ai tana nan ga masu nacin dana tsaya shiryawa nan su sai sunzo sungaida Abbansu tana nuna yaran dake gaban Abban suna magana. Malam Ahmed ina kuma zuwa Abba ya tambayi Ahmed din dake shirin fita daga dakin nan ya juyo cikin ladabi yace ruwa zan karbo nan bakin get na dawo Abba. Kagani ko an manta da ruwan yana nan nasa Tani ta fito dashi tun jiya da dare da muka koma har safen nan ina zuci zuci na fito dashi fili na manta wurin sauri. Ahmed din ya fice yaja kanina babba suka fita tare ruwan ya sayo ya wurin bag biyar ya rabawa sauran dakunan shi kuma ya nufo dakin da Abban yake kwance dana goran swan ya kawo masu. A yadda ya samu Abban da ummah zaune ya tabbatar mashi suna wani muhinmin maganan daya shafi rayuwansune a lokacin don yanayinsu kawai ya kalla ya gane hakan zanje gida na daukota ya fada. Yauma ba zata shiga school din bane tunda jikin Abban naku da sauki sai ya danyi kasa da kai yana dan murzan hannayeshi yace damawai tazo din dai ta dubashi hankalinta zaifi kwanciya. Kai amma Ahmed kana da wani zance don me zaka biyewa shirmenta bayan tana shirin zana jerabawa nan da yan kwanaki masu zuwa idan Allah ya kaimu. Kinga kyalesu yakawota daga nan sai ta wuce ai sunsan abinda sukeyi amma kafin ka tafi idan ba matsala ka dubo likitan yazo ya dubani. Don naji sauki ina son sallama yau nagaji da zaman asibitin nan to barin duba Abba ya fada ya samu likitan bai karaso ba don haka ya dawo ya fada masu lokacin hankalin ummah yana gun yaranta don haka bata bi ta kansu ba kuma. Har ya fita yana tunanen rayuwan irin na gidan mu a yadda yadan kulla a dan zaman asibitin nan ba karamin kokari Abba keyi da iyalishin ba aje iyali irin wanan sai mai dauriya dayasan kan duniya. Ba zai iya jure zama a tsakanin su ba don haka ya mike ya fita dan dama dama Abba din ya kan iya dan sakewa dashi a wanan zaman asibitinne kuma har dan fara ganin sakewan fuska ga Abba din. Falon ta fado hankali tashe sukai ido biyu da uwar dake zaune ita kadai tana dan dukan kafanta a kasa tare da bubuga hannunta saman kujeran da take zaune a kai. Babu ko sallam tana shigowa sukai arba da mahaifiyarsu din ta fara fadin mama lafiya ni wallahi har kin ban tsoro na dauka Abbane wani abu ya sama ai tana maganan tana kokarin cire gyalen dake kafadanta a lokacin. Amma ai jiya kan ku tafi ya samu sauki aiko ni dan Allah zauna ki tayani tinane ko zancen nan danaji gaskiyane da sauri Aishan ta kallo uwar a cikkn son tasan meya faru lokacin yar uwan nata Rukkaiya ta shigo da yarta gida. Mama wallahi har gabana ya fadi saida nazo banga kowa a kofan gidaba hankalina ya kwanta na dauka Abbane yayi margaye wallahi. Ke sakarece Abban naku kike son ya mutu to mama akwai wanda ba zai mutu bane duniyan nan kowa ai tunda yazo saiya koma don babu mai tsayawa gadin ta. Ni dan Allah ki zauna kun isheni da shirme wai ashe mijin zahra dan wani babban maikudine a Abuja mutanen nan dasu suka munafuncemu suka rufe zancen. Dan me kudi kuma ta ina mama kodai dan dangin mai kudin kinfasan mutane da karya mama sai a shirya karya yanzu ki dauka gaskiyace. Akwai kamshin gaskiya a cikin zancen nan don haka nake ganin ba karya bace wai shine dan farin mutumin ke yanzu hakafa waje zasu koma da zama wai ashe saboda zahran ya zauna nan har lokacin nan. Mama ke ina kikaji wanan zancen don Allah kuma har in gaskiyane mu meye ruwan mu cikin zancen su suka sani da wanan ai bamuba. Wallahi A bakin Shafa shafa makirace tasan komai amma ta iya rufe muna haka kuma salma da kanta ta fada da Alh ke mamaki ya tsure yaron shine yake fada mai gaskiya. Kasan Niger ko, ko mali don suma kasan wajene ai, ji sauniya ana maki zancen US yana aiki under UNICEF nefa ashe kingako dole hankalina ya tashi ai don ko yannan ku maza basu iya samun wurin nan balle mazajen ku da basuyi wani karatun kirki ba. Jikin Aishace ya fara sanyu don ta fahinci me uwar ke nufi itako Rukkaiya cewa tayi ko ma me yake ai baikai mazan namu wayewa ba tunda har yanzu a babur yake yawo a gari. Rukkaiya kin kuwa san me mama ta hango a nan dan kwanaki kadan zakiji cewa zahra da mijin ta sun faso gari wata kilama har yafi kowa. In ma
Chapter 236 · 0% Book details