← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 239 OF 286

Sashe 239

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dije waya daure wanan akuyan jiyane data banye Ahmed dake tsaye rike da abincin dabbobin yake tambayan kakar tasa banyewa kuma yaushe ta banye don koda safe da zan shiga bandaki ai a daure take banga alaman ta banye ba. Kallon mamaki yakewa kakar tasa ganin haka yasa tace dashi amma barin tambayi uwarku inji ko itace ta daureta ko kuma wata daga cikin yan uwan naka ta daure. Kai ban tsamani don naga kamar ai ba ruwansu da dabbobinsu barshi kawai kila dai na mantane ya fada ya nufi hanyar shiga wurin dabbobin dauke da abincin nasu. Yana isa itace ta farkon tasowa da farko ya dauka cewa saboda abincin data gani a hannunshi yasa ta nufo shi amma sai yaga sabanin hakan don jikinshi takebi da sunsuna tana dona kanta saman jikinshi. Baya jin komai game da akuyan don haka ya dauki hannunshi ya dora a kanta ya fara sosa mata saman kan nata a hankali yana shafan bayan ta har zuwa tsawon wani lokaci. Kafin shima ya sauke ajiyan zuciya yana fadin uwar garke bari naba yan uwaki abinci kada muyi laifi a wurinsu kuma daga haka ya duka ya fara kokarin bude ledan abincin nasu ya fito da harawa ya zuba masu nan suka rufe daci shi kuma ya fara gyara masu wurin da yai kwana biyu ba a gyara masu ba. Kamar ance ya dogo kai ya kallo iccen tumfafiyan sai yaga alaman wasu ganye suna ja a jikinshi shi a zatonshi iccen ne keson mutuwa a lokacin don haka ya nufi wurin da zuma ya kai hannu ya duba. Aikuwa daga can wanan akuyan ta soma wani irin kukan nan nata mai nuna inkiya ga mutum lokacin da wani abu zai faru da mutum din a lokacin da sauri ya cire hannun shi daga iccen yana kallon akuyan dake kuka tana tuma tana nuna alaman kada ya taba icen sai kuma ya koma kallon iccen ya dan kurawa icen ido kananan tuho yagani a jikin iccen sun tartso a jikinsa ya sauke ajiyan zuciya tare da dukawa ya dan fara tsuntar busasshen ganyen icen daya fado kasa yana tarawa don yana da bukatanshi. Kafin ya fara kawar da kayan da aka watsar da shara a gindin itaciyar ya share wurin tas har ko ina yana Allah waddai da hali irin na kannesa dako shara basa iya yi suna mata dasu . Har sai yar tsohuwan dake fama da kanta wani lokacin ta duka ta gyara wurin da kanta haka kuma ba kunya zasu kara bata wurin saboda basu da kwabo. Har lokacin wanan akuyar uwargarke tana tsaye ta kafa mai idanu saida taga ya kauce daga wajen lokacin tayi kamar ajiyan zuciya irin na mutane ta soke kai ta fara sunsunan abincin daya aje masu din. Ya gama dasu shine ya dawo falo ya zauna yaci abinci lokacin ne ya bugawa mahaifinshi waya don haka kawai yaji yana kewan mahaifin nasa yana son yajishi yaji yaya muryan mahaifin nasa take ya dauki waya ya danna masa sako don yasan zai kira idan yaga sakon nasa saidai bai dauka haka da wuri mahaifin nasa zai kirasa ba. Sai gashi nan take yana ganin sakon ya dauki wayan ya kirashi shi kuma yaki dauka ya fito daga daukoni ya ajeni asibiti wurin Abba zai dawo gidane ya tsaya wani shigo yayi sayayya don inna ta fada mai kayan miyarsu ya kare. Ita kuma a zatonta yana asibiti yana dawainiya da yan gidan mu shine ya fita batunsu har kayan abinci ya kare bai sayo masu ba don haka ta sameshi a part din mu tayi mashi tas tana fadin cewa ya kama dangin mace ya fita batunsu su. Shine dalilin tsayawanshi ya sawo masu abinda tace din ya kare masu lokacin saiga mahaifin nasa ya kirashi da wani number sai ya dauka ba tare da sanin shibane a lokacin don da bai daga wayan tasa ba ya nasa a zuciyar shi. Sai gashi kuma ranan ya kasa barci don tunda na dawo naga canji a fuskanshi saidai bansan abinda ya sameshi ba bai kuma fada min ba don haka na dauka ko dashi da inna ce a lokacin. Washe gari aka sallamo Abba da safe don haka ban samu zuwa ba sai weekend na shirya zuwa gidan namu da sunan idan naje a can zan wuni saida yamma zan dawo gida. Sauri nake ina ta dan aikin da zanyi lokacin ne na dago jakkarshi da yai tafiya da ita zuwa bambarake tsuki naja don sam na manta da jakar a wurin tun lokacin daya dawo din. Na dauko jakkar a cikin sauri ina kokarin cire kayan dake cikin jakkar naga kullin maganin daya dawo dasu kamshin maganin kawai naji saida kaina yayi wani irin sarawa lokaci guda a saman gado na dora mashi su naci gaba da aikin da nake ga warin maganin yana shiga min hanci ba dadi a lokacin. Ya dawo daga sayen kosai ya shigo dakin tun daga kofa yaji kamshin maganin ya fara dan waige waige yana duban ko ina na falon kafin yace zahra na amsa mai daga ciki ina fitowa daga bandakin dana gama wankowa a lokacin. Na fito muka hade a kofan falon yake fadin naji kamshin wani abu a dakin nan mai daga hankali nima yanzu na dauko wani leda a cikin jakar da kadowa tafiya dashi ga yacan saman gado na ajema na fada mai ina kokarin fita don kaina dake sara min a lokacin. Waje na koma na zauna jina shiru ban shigo dakin ba yasa ya leko wajen yana fadin wai aiki kikeyine kizo mu karya zaune ya hangoni nayi tagumi da hannu daya ina sakin hawaye a fuskana. Subbanallahi zahra meya faru ko Abbane shiru zahra ya kara maimaita sunan yana kiran sunana tare da dan girgizani idona yana kafe wuri daya banko kyaftawa. Innalillahi ya fara nanatawa a bakinshi kafin ya juya zuwa dakin da sauri ya dauko wanan maganin da aka bashi ya bani yana zuwa ya turmuza min a hanci kafin ya fita da sauri zuwa wurin su inna ya debo garwashi a murhu saida ya kamo hanya ya fara kwalawa Dije kira yana fadin Dije dije dije da sauri bai tsaya ba ya nufo part din mu kuma. Bai tsaya rufa min komai ba ya zuba hayakin hakana ya tara a fuskana yana dan hura hayakin dake tashi da hannunshi zuwa jikina kuka sosai na fara cak ya mike ya daukeni zuwa kuryan dakin mu kafin ya fito zuwa dauko bin hayakin ya shigo dashi. Amadi lafiya kuwa muryan dije ke tambayanshi daga kofan ga kuma wanan bakar akuyan nasu ita da tan uwanta sun dauki ihu lokaci daya daga can ciki yake ba dije amsa da shigo dije zahrace wallahibta rikice min yanzun nan fa. Subbahanallahi meya faru meya jawo hakan ta fada cike da kulawa tana karasowa cikin dakin idonta ya sauka a kaina ta fara fadim aashaa dama tana dasu ke nan dai eh tana dasu saidai ban tsamanin suna tashi haka dama. Ko yanzu wani maganine dana zo dashi shine sanadin tashin nasu yanzu din don maganin yana da karfi sosai gaskiya wallahi ban ma san lokacin data dauko maganin ba na dawo daga sayen kosai na samu ra fito dashi a jakata yana magana yana kokarin maida hankalinshi a kaina ya fara karanta min addua kafin ya koma kira,a suratul sulaimana. Har akaci aka sude wai inna basuji duk abinda ke faruwa a wurin mu ba sukace don sun koma daki sun rufe suna barcin safe a lokacin hakan ya hana masu jin abindake faruwa a lokacin. Barci na samu nayi sosai sai sha biyu na mike ina salati tare da kallon lokaci ina kokarin son in tuna abinda ya faru dani amma na kasa hakan saidai jin jikina da nakeyi kamar andokeni konayi wani aikin wahala. Kin tashi ke nan ya fada na amsa mashi da eh kawai ina kwance zakici wani abune yanzu naje na sayo maki ya tambayeni cikin kulawa nace bana jin cin komai. To dan daka ni kazo ka fita min da wanan mashin din daya tare muna hanya mutum yana cikin daki da mace tun safe ya kasa fita ko ina dan sana,anma da kakeyi yanzu nema kake ka daina in an kyale ka duk saboda mace. Innace tsaye a kofan falon mu take fadin wanan maganan cikin daga muryanta wai zata fita da kaya mashin dinsa ya tare mata hanyan da zata fita tace. Baiyi magana ba naga kawai ya mike ya fita zuwa wajen can naji muryan shi yana fadin haba inna na dauka ai ko kare na kawo gidan nan da sunan nawane zaki kula min dashi balle matata zahra inna. Nina rasa me yarinyar nan ta tare maki kullun kike hattaranta haka inna har da laluran ciwo ya kama yarinyar nan amma baki leko kin mata ya jiki ba sai kizo kuma yanzu kina fadin wanan maganan don Allah. Yarinyar nan fa da ace itama mai halin yan zamanin nan ne bata samu tarbiya irin hakaba ba za ayi abu mai kyawo a tsakani n kubafa don ko waye baida lafiya baka dubashi ba kuma ka kama fadin magana mara didi a kanshi lokacin dole yaji zafi gaskiya. Don ni banga inda ta kasa daku ba a gidan nan duk yadda ake son a samu mace mai hakkuri nasan zahra tana hakkuri da kowan mu gidan nan don bata taba nuna abinda kike mata yana sosa ranta ba. Ikon Allah dan Dije duk akan matarka don na hanaku kwanciyan lalaci ka fito kana fada min magana haka son ranka don raini dake tsakaninmu ko ? In babu raini zaka fito don nayima fada ka jaye mashin tun safe ya tarewa mutane wuri kana cikjn daki kwance shine jin haushin ka dani har zaka nemi mayar min da magana kan wata mata taka can. Koma dai meye inna ni nasan darajan mata ta don ba zaman banza nakeyi da ita ba a gidan nan aure mukeyi don kuma naga ai bake ba kosu Aisha ke ciwo gidan nan ta fara zariya ke nan tana dubansu amma ke baki leko ba suma hakan. Fisabilillahi anyi adalci ke nan inna ga hakan yanzun kuma kinzo kina fadin maganan
Chapter 239 · 0% Book details