Sashe 187
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
fice take fadin salima tace kana kirana ? Banda wanan time a yanzu ya fada yasa kai ya fita taja tsoki itama ta fice daga falon zuwa part din ta har ta zauna wani zuciya ya debeta ta mike zuwa part din da bakin nasu suke. Zaune suke dukkansu a falo suna hira saigata ji sukayi kawai an fado dakin ba sallama hakan bai hana dayan tace a, a hjy Yabi ce yanzun muke maganan ko kun tashi muje mu gaisheki ai. Hannu ta daga alaman tayi mata shiru a lokacin kafin ta bisu da kallo daya bayan daya ta sauke idonta akan hjy Murja din tana fadin murja meya kawoki gidana a wanan lokacin? Hjy murjan ta dago ta kalleta tayi dan murmushi kafin tace amma dai musulmai kika samu a dakin akala kyayi sallama ko zamu san damu kike zancen a yanzu ? Murja watau har kin dauka wuyan ki ya isa yanka a gidan don dan wanan asirin naki da ayanzu kike ganin yana aiki akan Alh ke nan to barin fada maki kiji kuma ki rike idan kina tafiya da rana tsaye ni yabi dare da ranan duk a tsaye nake indai akan gidanane kece kika fara yanzu. Lalai kuma kinyi sa,a malamin ki ya iya aiki harda ya iya karya dokana yasaka Alh ya dauko ki daga kauye zuwa wanan gidan a yanzu saidai kinyi kuskure babba na yin hakan . Don in kishigone ta gaba ta birkice zaki koma wata kilama wanan karon ba inda kika fito zaki koma ba sai wani bakon waien. Kowa na dakin sai binta sukeyi da kallon mamaki daga can inda yan matasan yan matan ke zaune da sauri dayan ta kunna waya tana daukan komai dake faruwa a dakin lokacin saboda yarinta. Hjy yabi ke nan ban kara tabbatar da cewa ke din jahila bace sai yau din nan da kike wanan ikirarin haka a gaba saidai ki sani . Ni murja ba yar matsafa band ba kuma jikansu bace a gidanmu musan Allah da Annabinsa tsagwaron su haka kuma da shi na dogara a rayuwana don shine boka da malam din gidan mu kinga tunda har Allah ya amsa min addua na akanki saina kara gode mashi. Karya kikeyi munafukan Allah duk inda kike zuwa ai munsani don abin duniya ba boye yake a kasan nan indai indai bera bai daina yawon dare ba wata rana su hade da mage wurin yawon ai. Ta jiya a fusace ta bar dakin cikin kunan rai tare da mamakin canzawan hjy murjan don bata taba tsamanin irin haka ba gareta wanan abin ya bata mamaki matuka. Abin mamaki baya karewa sai ga hjy yabi din na fadawa Alh wai yayiwa hjy murja iyaka da ita don ta nuna ba zaman lafiya tazo yiba a nan don tana ganin kamar ka daure mata yanzu. Har tana nema taci min a mutunci a gaban yan uwanta har tana fadin zataga iyakanta yanzu a gidan ke nan dama da wani manufa tazo nan ke nan. Ya juyo ya bar abinda yakeyi din gaban mirror dinshi yana fuskantar ta abinda ya dade bai faru tsakaninsu ba ya dan murmusa yace. Cikin kada kai Yabi kada ki manta da cewa ni din nan ni na aje kowan ku a gidan nan haka kuma nasan halin ko wacen ku. Don haka ke me kikaje nema a part din ta don naga ni kaina na nemi kizo nan kika bata min lokaci ki kaki zuwa don ki nuna mata koni ban isa dake a gidan nan. Don haka kina tsanmanin yanzu zaki samu wani girma a wurin murjan ke nan a gabanta fa kika nuna banda daraja ko kima har a idon yayan ki ?