Sashe 40
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
data biyosu ranta bace. Duk yadda yaso ranan mu hadu bai samu hakan ba don bubuwa gaba daya sun rikemai a ranan saboda test din da suka shiga mai zafi kodaya fito ya samu motana baya wajen yasa shi komawa ciki. Zuciyar shi ta bashi shawaran ya nemi number na ya kirani haka kawai zaiyi ya samuyin magana dani yadda yake so son so yake yaja min kunnem yin hakan saidai yasan a fili ba zai iya yin hakan ba gareni don yana kallon narkankun idanuna yasan zasu rikitar dashine lokaci guda. Zai iya cewa yana hanin mata kyawawa da zarra irina mata amma bai taba haduwa da macen data rikitashi ba lokaci daya irin hakan. Yasan dai bai isa ya nuna so ko shakuwa a inda Allah bai kaishi ba haka kuma shi bai isa yakai ko matsayin drivern gidan su ba ko mai ban ruwa gidansu ba yadda yaji mutane suna fadan irin arzikin gidan mayana din a gari. Shawaran zuwa department din mu yayi ko zai ga abokan karatuna hakan yasa ya juya da sauri zuwa hanyar shiga building din suka hade da hannatu a kofan wace ke fitowa don zuwa gidan lokacin. Tana ganin shi ta fara sake murmushi a fuskanta lokaci guda tare da fara gaidashi tana fadin master kayi wuyan gani fa ashe ka shigo yau bamu sani ba gashi harsu zarah sun wuce gida tunda muka fito dazun tace yau suna da baki a gidansu don haka ta koma gida da wuri yau din. Don Allah ko kina da lambata ki kira min ita akwai sakon da zan batane eh to nima dai na dauki lambatane a wayan ta bata sani ba amma dai gashi tasa hannu tana ciro wayan nata daga cikin jakkarta na hannu ta fara duba wayan can ta miko mai tana fadin ga layin nata akwai kudi a ciki dazun ta saya min kati. Kai wanan ta faye surutun tsiya wallahi haka ya nasa a zuciyar shi yana karban wayan a hannunta sunan ZARAH MAYANA yagani da manyan harufa. Danna kira yayi sunan ya shiga saiga wayan na ringing a daidai lokacin ina kwashe kayan da mukaci abincin dashi da sauri na aje tarim plates din dana dauka zankai kitchen. Bakon number nagani na tsaya ina mamaki ciki tsoro nakai kunnena a lokacin naji muryan namiji yana kwada min sallama. Daga wayan nayi ina mamaki naji muryan hannatu na fadin zarah nice coursemate din ki master ke son magana dake na kiraki master na fada cikin mamaki sai naji sallaman namiji. Amsawa nayi yace OK dama naso ganjn ki yau ashe kin shigo har kin fita ban sani ba muna ciki munayin test bamu fito da wuri ba. Saisai dama akan wanan sakon da kika ban jiyane a cikin envelope naso muyi magana dake don ban san ko kudin meye haka kika bani ba ? No kayi amfani dashi kawai na bakane kawai nagode sai anjima zaiyi magana nace kaba hannatu na fada a karshe na hana dama yin magana a gaban hannutu din ko godiya. Hello Zarah kina lafiya kalau na fada a gajerce har yanzu kina school ke nan ashe tace yanzun nan fitowana daga class ke nan zantafi. Ok saida safe na fada na kashe wayan lokaci guda na mika hannuna na kwashi plates din abincin zuwa kitchen daga nan na koma dakina. Ba matsala ko Hannatu dake kallon shi ta tambayeshi ganin yadda yanayin fuskanshi ya sauya lokaci daya a wurin duk da bataji ko akan me mukai magana ba a lokacin. Hostel din maza ya nufa bayan sun rabu da Hannatu din don ya yawata ko kayan zasu shiga nan aka kewayeshi sai gashi kayan sun samu shiga har wasu basu samu ba a wurin. Haka yasa yai masu alkawarin zai kawo masu in sha Allah, kudin shi mina mina ya kirga sai bakin titi ya hau mashin zuwa kasuwa inda zai kara saro wasu ya kuma cika alkawarin daya dauka din wa mai kaya . Tun kan ya sauka mai kayan ya hangoshi ya fara washe baki don lokacin daya bashi ma bai karasa cika ba ya dawo suka gaisa dashi yace har sun shiga ke nan yace kaya sunyi kasuwa sosai wallahi. Nan ya mike ya jawo wanda ya boye mai da farko yana fadin kaga wasu yau aka kawosu sai ka hada dasu zasu shiga sosai wanan mata da maza duk zasuyi saya sosai idan sin gani. Zuciyar shice ta bashi shawara yayi amfani da wanan kudin kawai tunda nace na bashi su koda daga baya zai zauna dani muyi magana a kansu. A take ya biya kudin kayan gabaki daya yana gyaran kayan mutumin ke fadin daukan kayan nan yayima yawa da zaka daure ka samu tsohuwar mashin ka saya sai kaji dadin yawatawa da kayan nan zaifima sauki sosai. In,sha Allahu ina da niyar yin hakan nan gaba amma ba yanzu ba sai kudin sun kara kauri nan zuwa gaba dai sai nasa cigiya in saye don kayan sun fara min nauyi a kai haka. Ya baro kasuwa zuwa gida da kayansa niki niki yana hanyane ya tuna da alkawarin da tayi na sayowa dabbobin su abinci kaya kawai ya aje daga kofan yace mai mashi din ya koma dashi . Jin motsin shi da uwargarke tayine yasa ta mike ta fara kuka sosai lokaci guda kuna na tashin hankali har saida Dije dake daki ta fito hankali a tashe zuwa wurim garken nasu tana duban su. Kofan shigowa gidan uwar garke ke kallo tana kuka sosai sai hakan ya dagawa Dije hankali ta nufi hanyar fita wajen gidan sai kuma taci karo da kumshin kayan shi a ta cikim gidan . Mamakine ya kama Dijen lokaci guda ita daya take magana dama Amadi ya dawone ashe ko kuwa kayan a nan ya barsu ya tafi ? Lekawa tayi ba kowa wajen gidan sai yan mutanen dake gittaya jefi jefi a layin can ta hangoshi tafe ya sayowa dabbobin haki da dusa yana sauka saman mashin yana tambayanta ko lafiya ?