← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 286

Sashe 100

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Makewayin ba laifi don an shafeshi da siminti gashi da gani yana samun kula wajen tsabtaceshi ko uaushe haka kuma baka ma dauka gidan marasa karfine kake. Tufafin jikin shi ya fara cirewa kafin ya watsa ruwa ya dade yana cuda jikin shi ya kuma ji dadin ruwan sosai ya kwara ya fito take yaji wani iska mai sanyi yana dukan jikin shi. Da dan sauri ya karasa wanan sakin da Shattu ta nuna mai ya shiga bai sauya kayan ba gadon da ya gani a dakin yakai zaune a kai. Sai lokacin natsuwa ya fara zuwa mai ya fara bin ko ina na dakin da kallo babu wasu kayan jin dadi a dakin sai wanan gadon da wani mattacen kujera mai zaman mutum biyu kawai a dakin. A hankali yakai kwance saman gadon sai lokacin ya gane cewa saman gadon kara yake zaune ashe saidai yadda yasha gyara ba zaka gane cewa gadon karane hakaba. Tunane ya fara yi kota ina zai farayin abinda ya kawoshi wanan kasan don yadda yaga garuruwan yana da wuya a iya gano mai mahaifinshi haka kai tsaye. Dan dama saukin da yaji shine cewan da tsohon yayi zaibi masu irin sana,an mahaifin nasa a baya ya bincika masa. Yana cikin wanan yanayin na tunane har barci mai nauyi ya daukeshi a wurin na tsawon lokaci yana kwance yana barcin gajiya don akwai gajiya sosai a jikinshi gaskiya. Karfe biyu ya falka koshi ba don yaso ba sai don lokacin sallah dake ratsa jinin mai kula dashi da duk lokacin yayi zai tashi kome yakeyi yayita a cikin lokaci wanan ne ya falkar dashi daga barcin nasa a lokacin. Shatu kawai ya gani a tsakar gidan tana yan aikace aikacen ta a lokacin ya nufi ban daki ya kewaya ya fito ya fara alwala don sallah. Yana dakin zaune har akai la,asar ya fito waje ya samu itama Shattun tana daki lokacin hakan yasashi fita wajen gidan don dama maza ba a san su da zaman gida ba su sai mata. Sannu a hankali yake takowa daga inda yake tsaye kofan gidan bayan ya gama bin unguwar da kallo yana nazarin wurin can ya tako zuwa inda dabbobin gidan suke killace kamar yadda ya hango a sauran gidajen unguwar suma sunyi. Nan ya tsaya yana karewa dabbobon kallo yana mamakin irin kiwon da suka samu suka cika haka sukai kyau da dadin gani kafin idon shi can ya sauka kan wata akuya dake kiwo a cikin awakan dake cikin garken. Uwargarke sak yagani a idonshi saida abin ya firgitashi lokaci guda ga kuma akuyan na kallon shi ta tsura mai ido kamar yadda uwargarke kan kafa shi idanu tana kallon shi din wani lokaci. Kasa boye mamakinshi yayi don saida ya furta a fili yana nunata yace uwargarke ke nake gani ko gizo idona keyine ? Yarona ka samu tashi ashe yaji an fada daga bayanshi jin haka yasashi juyowa yana fadin eh baba ashe barci na samu nayi tun fitowana daga wanka. Ai hakan yana da kyau sosai gara dai daka dan samu ka runtsa din zaka samu ka dan walwale kadan gashi yanzu har kazo duban dabbobin mu. Eh baba kiwon sun samu kula sosai gasu sun banje suyi kyau sosai gwanin ban sha,awa tubarkallah masha Allah. Kazalika dana ai kiwo kula sukeso indai ana kula dasu ana basu abinci yadda ya dace sai kaga Allah ya tarfawa abin albarka kasan kuma mu filani ba a rabamu da kiwo ko da na kazane kuwa. Ya dan murmusa har lokacin idon shi na kan wanan akuyan yana kallonta cike da mamakin haka a zuciyarshi. Baba dama akuya sukanyi kama da junane ya tambayi tsohon alokacin da bai shirya hakan ba yaji tambayan ya fito a bakin shi lokaci daya ya furta hakan ga tsohon. Murmushi mai sauti tsohon ya sake ya dora da fadin yaro mutane ma anyi su da kama balle dabbobi da halittansu duk iri dayane . Sai kuma ya kawar da zancen ta hanyan fadin yanzu daga wurin abokina nake na soma tambayan shi labarin mahaifinka ko Allah zaisa a dace amma hakan bai samu ba don ya nuna min bai san wani wanda ya taba zama a wanan nahiyan na sokoto ba gaskiya . Saidai zai saka bincike a kai shima ta hanyan tambayan mutanen su don shima wani tsohon mafataucine daya jima yana wanan harkan na sayar da dabbobi a kudu. Sosai Ahmed din yaji dadin jin bayanin da tsohon ke mashi a lokacin nan dai ya kara kwantarwa yaron da hankali tare da bashi tabbacin cewa ya kwantar da hankalinshi muddin mahaifin shi dan kasan mambilane za a gano mashi shi in sha Allahu. Suna wajen suna hira har akai kiran magariba abinda yasa su dagawa ke nan shi Ahmed din ya shiga gida ya debo masu ruwan alwala ya kawo masu. Tare dasu akai sallah jam,i a masallacin unguwar suna cikin wa yanda suka dakata har a idar da sallah a lokacin bayan sun idar din suka nufo gida kai tsaye tsohon na gaba shi Ahmed din yana bayan shi. Ya dade a zaune yana maimaita kallon photo don shi kanshi yasan yayi kama da wanan guy din sosai sadai kamar wanan din zai dan darashi da fari da kuma tsawo haka kuma ya dan fi shi yasir din dan budawa kadan. A ina fattu ta sami wanan photon kuma wayeshi din na cikin photon da har yake da kama dashi haka kama ba kuma na wasa ba ? Da badon yasan cewa shine dan fari ga iyayyen shi ba da yace shima wanan din jinin sune don kamarsu har ya baci sosai. To a cikin dangi shi din dan waye da har bai sanshi ba bai taba jin wani yayi maganan shi ba kuma ko ta kamanin su duk da dai shi ba wani sanin yan uwama yayi sosai ba. Well zai kira Fattu din yaji waye wanan guy din kila a wurinta zai samu karin bayanin da yake son sani amma tabbas itama Fattu din taga kamar sune dashi yasa ta turo mai wanan photon da aka rubutawa Master namu. Master ? Master din me ya tambayi kanshi kafin yaja tsuki yana aje wayan a gefen shi ya dauko littafin shi yana dubawa. Naji dadin zama a dakin tsohuwar don kuryan ba hayaniya ko gittaiyan mutane kamar wancan dakin dana baro na farko da muka sauka sai nan din yafi mun can dadin zama. Saidai da alaman abokiyar zamanta a dakin itama tana ji da kanta don tun shigowan ta lokacin banyi barci ba muna waya da ummah ta shigo muka gaisa bata kara bi ta kaina ba sai harkokin gaban ta takeyi na shirin kwanciya ta fita batuna nima haka. Washe gari ma hakane mun daiyi gaisuwan safe da ita bayan mun sallame sallah daga haka kuma bamu kara yin wani magana ba karshema na saka earpiece a kunnena ina sauraren kira,a nayi barci don haka ban sam me akeyi a gidan ba kuma. Sai wajajen karfe goma naji ana tayar dani daga barcin na bude idona tsohuwan dakin ne mahaifiyar su mommy a kaina. Da sauri na kai hannu na cire abinda ke kunnena na dan yunkura ina gaida ita da kwana duk dana lekata da asuba nagaida ita tana fadin kina barci haka baki karya ba har wanan lokacin yar nan ? Zan karya na fada a sanyaye ina dan murmushi a fuskana toki tashi ga abin karyawan ki nan uwarki ta aje maki a falo tun dazun su sun fitane zuwa Na,ibawa gidan wan mahaifinsu. Na amsa mata da to ina kokatin mikewa zaune tana fita take kara fadin idan zakiyi wanka sai in saka a kawo maki ruwan dumi kiyi hakan yasa na gane ba zan samu ruwa a bayin ba ke nan lokacin. Nace wanka zan fara saina karya tace barin zo ta fita zuwa can saiga wata matashiyar mata ta shigo da ruwan wankan tana gaidani na amsa tace ga ruwan hjy tace a shigo maki dashi nan din. Nayi mata godiya tazo zata fita na kirata na mika mata dubu daya nan take ta washe baki tana min godiya ta karba ta fita tana murna ni kuma na mike zuwa ban dakin nayi wanka tare da brush na fito. Kamar yadda na saba idan ba makaranta zan fita ba ko wani waje nakan tsaya in bata lokacina a daidai wanan lokacin nayi sallah nafila na rokawa kaina saukin rayuwa da dacewa ga rahaman ubangiji da nemawa iyayyena gafara. Nan ma din hakan nayi don nayo alawala na fito nayi raka,a biyu na zauna ina addua a daidai lokacin wanan yarinyar da muka kwana saman gado daya tashigo dakin . Kallona tayi ta dauke kanta gefe taci gaba da abinda takeyi har zuwa shiga ban dakinta don ta kewaya sai gata tafito kuma a lokaci guda tana fadin. Don Allah a ina kika samu ruwan wanka ne nace wata mata ta kawo min nayi daga haka ta fice daga falo can naji muryanta tana fadin. Nima a saka a kawo min ruwan mana zanyi wankan yanzu kifita min a ido yar nan ko ita wanan bata da lafiyane kuma bakuwace ita kinga dole nu kula da yar mutane ko. Bandai san ya sukayi ba naga wanan ta dauko ruwan da kanta tashige bayi tana wanka har na gama shirina na nufi falon tsohuwar bata fito ba. Ruwan shayi na dansha koshi ban iya shanyewa duka ba nabar saura na mike na koma cikin dakin na haye gado wanan din na sama tana shiri kallo daya tayi min ta kawar da kanta gefe har tagama ta fice ta barni. Ina nan ni kaidai a dakin tunda ba sanin kowa nayi ba zuwa can rana sosai na fara jin muryan mommy sun dawo sunawa mahaifiyar su bayani. Zuwa can mommy din ta leko tana fadin daughter na tafi na barki ke kadai sai ta sameni a shirye na saka wani atamfa blue da adon farin filawa a jikina sai dan kwalin shi da gyale fari mai kyau a gefena ajiye koda fita zai kamani. To kinyi wanka ko nace eh hjy tasa an bani ruwan wanka nayi OK kin karya dai ko ta tambayeni eh na bata amsa cikin
Chapter 100 · 0% Book details