← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 286

Sashe 60

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

yaran nan angode Allah kara arziki da nisan kwana Allah ya kade shedan da raban rayuwanku a kullun sai mun ga abin sallah kuma in Allah yakai rayuwan mu lafiya ba matsala kaka tunda kinga wanan ai kishi yana tafe in sha Allah hanne ta fada. Har lokacin jna rakube a bayan shi cikin tsoro da tashin hankali ganin na kasa wuce yasa ya dan juyo idona yana rufe shige man ku tafi zarah ke take jira ku tafi. Kamar wace ta farfado na dan zabura ban tsaya mata ko sai anjima ba na bi bayan zarah muka fita har ina hadawa da dan gudu kadan don sauri. Muryan shine a bayan mu yake fadin kiyi hakkuri zarah akuyan na bata komai haka take idan taga mutane don son mutane ne da takeyi aina fada mata haka akuya take idan ta saba da mutane. Munkai bakin motan lokacin yaran suka fito daga gidan da sauri suna fadi mun daure ta hanne tace a, a kudai dan abinda mukace zamu baku kuka biyo dai ga hamsin ku tafi jin haka yasa na bude baki da kyar nace. Wani irin hamshin kuma ku jira nazo zan sallameku na bude motana na zaro kudi daga cikin jakkata dan dubu daya sabo kar na mika masu nace mungode kunji. Kai amma zarah kan dan wanan abin zaki basu har dubu daya nace haba dai ai sunyi kokari sosai hjy mungode Allah ya kara arziki da wadata na amsa da amin. Yana tsaye yana kallo mu kafin yace kin daiki jin maganata zarah wanan dawainiyan haka ga kuma uwargarke data tsorata ki haka kuma. Inbanda ke wa yake tsoron akuya zarah a lokacin na zauna da kyau a cikin motar na dago kai na kalleshi nace ban taba zuwa inda ake kiwon su bane kuma bana son kukan nan nata ina jinshi wani iri sosai har cikin raina. Yayi murmushi yace kardai tsoro gareki haka kai mata ke nan meke a cikin akuya kike tsoranta haka sai anjima na fada ina tayar da motan nawa. Yana tsaye har muka bar wajen muka fice daga unguwar nasu ya juya ya shiga gidan ya samu Dije na bude kayan tana ganin ya shigo ta fara washe baki tana fadin sun tafi ko ? Eh sun tafi ya samu wuri yana kaiwa zaune tare da kallon abinda tsohuwar keyi tana fadin in Allah yaso ka da arziki tsuntuwa yake baka. Haba Dije bai kamata kina nuna hakan ba a gaban su gaskiya yarinyar nan Allah ne ya hadani da ita kawai jinin mi yazo daya daga taimako abin ya koma muna zumunci a tsakanin . Amma don kinga sun kawo wanan kika kasa boye zumudin ki kan wanan abin don Allah me kuma nayi yanzu akan hakan na zubar da mutunci Amadi ? Kudine ta jawo a cikin ledan yasa ta juyo tana masa kallon tambaya a cikin mamaki yar nan da abin arziki take har da wani kudi ta dora a kai bayan wanan wahalan. Kudi kuma ya tambaya yana kallonta tace gasu kana gani kuwa nan ta shiga kirga kudin tana gamawa tace a, a a dubu ashirin cif ikon Allah wanan yarinya lalai tumfafiyace ita raban ta alheri ne a garemu gidan nan. Ashe uwargarke taga abinda tagani take mata wanan godiyan haka har muna hanata hakan taga abinda ta gani ashe a jiki yarinyar ke nan ? Mikewa yayi ya ciro yar nokia din shi tsohuwa data sha dauri ya danna kira na sauke hanna ke nan naga kiranshi ya shigo min a wayan na dauka. Bai jira mu gaisaba ya fara fadin zarah don me zaki min hakan tun farko ina munyi wanan maganan dake ba wanan a tsakanin zaman mu dake ko ? Wanan sai mutane su dauka saboda irin hakan yasa nake tare dake dama sai su mace mutumcin da ke tsakani na dake a dauka abin hannun ki yasa nake mutunci dake ashe ? Amma kasan bakai na kawowa kaya nan ba ko kuma ba gidan ku kawai na bawa ba don Allah ka daina min irin haka idan nayiwa kaka Alheri.
Chapter 60 · 0% Book details