Sashe 94
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baka jin komai a motar sai kidan gurmi da irin wasu dirobobin nan kan saka a mota idan wanan ya kare wani kalan zai dauka su ukune a cikin motan daga driver sai tsohon nan guda sai ko kayan daya dauko a bayan motan nasa. Don haka motan yayi shiru sai kida ke tashi a ciki kawai yayin da Amadi ke faman sauraron fatawan malam daurawa ta hanyar saka earpiece dinshi a kunne a yar karaman wayan shi a lokacin . Idan malam din yaba da wani adduan da bai gane ba zaiyi ta faman nanata adduan yana bi a haka har barci ya dan daukeshi na dan lokaci. Mafalki yayi da har ya manta da cewa a mota yake lokacin ba a gida ba komai yake mafalki a kai ba sai farin cikin rayuwan shi watau zahra. Zahra din ya gani zaune a cikin damuwa ya karaso inda take zaune yana tambayanta ko lafiya ya ganta haka a cikin damuwa. Kai ta dago ta kalleshi da fararen idanunta ta dan yi murmushin yake gareshi tana fadin sun sakani a gaba brother sai kace ni kadaine diya a gidan mu. Why zasuce saini ni kadai why da suke min hakan zasu rabani dakai su waye zahra ya tambaya bakin shi na rawa ta dago kai cikin yanayin kuka ga hawaye ya bata mata fuska ta ko ina ta nuna tana fadin sune sune suke son ganin bayan mu. Juyawan da yayi yaga inda take nuna mashi din ne ya falka ya ganshi a cikin mota ana faman sharara gudu sai tsohon nan abokin tafiyan shi daga gefen shi zaune sai daya mutumin dake tare da driver a gaba. Dan gyara zama yayi yana fadin sannu baba jin haka yasa tsohon dan dagowa yana amsawa tare da fadin amma yaro kai daga nahiyan sokoto kake ko naji hausan ka ta mutanen wajajencan na sokoto. Eh baba amma ni daga zamfara nake ba sokoto ba zani neman mahaifina ne a nan garin ysohon ya amsa da na,am anan Manbila yake da zama yace eh to bandai sani ba amma yace shi mutumin mambila ne saidai kuma in anzo mambila din anfi sanin su da chedawa. Chedawa tsohon ya maimaita sunan yace anya kuwa a nan cikin mambilan zaka sameshi tunda naji kace chedawa sai wajajen tasanma su gurojje. Jin hakan yasa Amadin jin gaban shi ya fadi sai ya kasa daurewa yace baba ina ne hakan kuma ? Duk a cikin bangaren mambilawa yake saidai ba gari daya bane don akwai dan tafiya tsakanin shi da garin mambila din. Au bakone a wanan nan nahiyar namu ke nan drivern ya fadi daga gaban motan tsohon yace bakone bai taba zuwa wanan kasan ba. Yace wai ya fito yawon neman mahaifin shine daga zamfara dattijon ya fada jin hakan yasa drivern dan juyowa yana fadin daga zamfara fa kace kake yaro ? Wallahi daga can nake ya kara fadi yace kace kasha hanya da tafiya mai nisa ke nan, amma kayi kokori sosai wurin wanan tafiyan haka ? Drivern ya fada yana mamakin yaron kafin ya kara fadin da fatan kasan inda zaka sameshi dai ya tambayi Amadin ? Idan bai sani ba ai baya zuwa har nan da sunan neman shi duk yadda akayi yana da kwatancen inda zai sameshi dayan mutumin dake zaune tare da drivern gaban mota ya fada. Murmushi Ahmed ya sauke a fuskan shi yana girgiza kai cikin bacin rai yace ko sanin sa ban taba yi ba asalima dai tun ina goye ya tafi ya barni nida mahaifiyata. Na daizo ne ko Allah zaisa na gano inda zan sameshi amma bansan sunan garin da zan sameshi ba din a yanzu yaji drivern motan yana fadin. Kai mutanen mu akwai daukarwa kai nauyi zaka tafi kabar danka daka haifa da zufan ka babu ko waiwaye wanan ai yiwa kai zaluncine don duk abinda ya shafi jinin ka ya shafeka. Drivern motan nasu ke fadin haka yaci gaba da fadin kayi dabara yaro don haka shine gatan ka da cikar kimar ka a idon mutane don duk da mutane sunsan ta hanyar sunna akai haifeka wanan ba zai hana su soke dashi ba. Ai wasu mutanen suna yin abu a cikin duhun kai da jahilci ta yaya kasan kana da da a wani wajen zaka gudo ka barsu tsawon wanan shekarun mutumin dake zaune gaban mota tare da driver yake fadin haka. Wani lokaci kadara da nisan wuri ke jawo hakan saidai wasu suna irin haka da son ransune Allah ya kyauta tsohon dake tare dake tare da Ahmed din a bayan mota zaune ya fada. Duk Ahmed din yana jin zafin maganganun nasu a zuciyan shi saidai baida zabin hakan don bai sani ba ko ta sanadiyan hakan zai samu mafita ga tafiyan nasa. Haka sukai ta zancen su daya shafi irin matsalan nan yana sauraren duk abinda suke fadi duk yana jin zafin hakan amma bai saka masu baki a zancen ba. Kasancewa tafiyan nasu yayi yamma da yawa don haka duhun dare ya riskesu sosai a hanyan baida wani zabi sai wasiwasin yadda zaiyi idan sun sauka wani gari. Wayan drivern ne yayi kara ya dauka hakan ya saka motan yin shiru lokaci guda da alaman tambayan shi ake ko yana ina a lokacin don cewa yayi munashiga taraba yanzu. Nan Ahmed din yasan inda suke ya gyara zamanshi yana bin hanyar da kallo ba tare da ya furta komai nan zaka gane irin misikilancin shi na rashin son yin magana sosai da baiyi. Ina zaune falo tare da mommy data dawo tasa Tabitha ta kirani a dakina tana tambayana abinda ke damuna nace ba komai kaina kawaine yake dan min ciwo nasha magani kuma ya daina yanzu. Idan bai daina ba muje asibiti zaifi su duba idan wani abune yake damun ki na danyi murmushi ina fadin ba komai mommy naji sauki. Fada min dai idan kewa hjy kika farayi tun yanzu na sani nace a a mommy ba gaki ba tace nasani amma tun zuwan ki nima nasan ban samu lokacin zama dake ba gidan nan daughter. Kiyi hakkuri wallahi aiyukane sukai min yawa ga zancen bukin auren autan hamisu ga kuma aiki daya taso muna a office wanan duk ya dauke min hankalina. Wallahi har fita nake sonyi dake muje ki dan zabo wasu abubuwan bukatan ki a nan don kada ki takura don naga bakizo da wasu kaya masu yawa ba don kada ki dade ko ? Murmushi nayi ina fadin lah mommy wallahi ba hakana bane naga dai ba inda zanine yasa ban dauko kaya masu yawa ba dama ban fada maki har kano zamu tafi buki tare dake ba. Za,ayi bukin autan mu namiji zaiyi aure kinsan maman mu mu bakwai ta haifa mu uku mata da wanan da kika ga dayan maman mu daya da ita itace yar wanda zaiyi auren a yanzu ita kuma dayan yar kanwar maman muce ita. Dukkan su a wurina suke tuntasowan su danayi auren farko nake zaune tare dasu mijina na farko mun rabune dashi yarana suna can hannun shi biyu maza sai mace daya. Saidai nan gidan ku kuma idan na samu indada karawa ta fada tana dariya nace Allah yasa mommy muma mu samu kani ko kanwa don Affarace karama har yanzu su ummah da mama basu kara bamu baby ba kuma . Da alama taji dadin zancen nawa don yadda naga ta lumshe idanun ta tace watau zahra kin gane wanan halin naku yasa nake son ku keda mahaifiyar ku. Don idan kuna zama da mutum da zuciya daya kuke zama da kowa ba tare da wata manufa ba kinsan maman ku maimuna ido da ido ta kalleni tace dani ba daina haihu da daddyn ku ba saidai na saka a masai ? Wanan yasa nake son haihuwa yanzu sosai zahra ko don in nuna mata iyakarta ta gane ba aiwa Allah shishigi ga lamarin shi da sam banda ra,ayin kara haihuwa a rayuwata . Amma yanzu naji ina son na haihu a gidan ku nima na saka nawa irin a cikin ku naga yadda zatayi damu din a gidan lokaci daya duk muka juya don jin kamshin turaren Abba da mukayi alama ya shigo gidan ke nan ya dawo lokacin. Fuskan Abba a kanta yake fadin wai zama kikayi da yarki haka kuna hira kamar kin samu wata babba sa,arki kuna hira. Daddy ke nan idan uwa bata zauna da yarta tayi hiraba a yanzu dawa zaka zauna hirana da zahra naji dadinshi sosai don yarinyace mai hangen nisa sosai. Ni ki tashi da wana shirmen naki ki bani abinci Abba ya fada kamar wani yaro mai jin yunwa ita kuma tana kokarin janshi da wasa har dai ta mike ta wuce zuwa kitchen wurin masu aiki. Lokacin Abba ya kalleni yace maamah ya labarin karatun kine da fatan kina mayar da hankali sosai dai kuma ina fatan kin fita zancen wanan yaron mara asali ? Gabana ya fadi amma haka na daure nace Abba lafiya kalau Alhamdullahi bana wasa da karatu in sha Allahu shine amsan dana iya ba Abba din lokacin. Zanji dadi idan hakan ya kasance gareki don ina da hope maikyau a gareki don hakane bana son ki tsaya yin wasa ko kulawasu can idan kinyi hakan zamu shirya dake. A zuciya na bashi amsa da sabanin hakan matsalane ke nan ko amma fili cewa nayi ban wasa Abba kuma ban kula kowa yanzu duk ina da labarin komai Abba ya ban amsa. Shiru nayi na dan lokaci kaina yana duke kasa kafin naji fitowan mommy daga kitchen hakan yasa na daga daga wurin na nufi dakina don kada in tsaya idona ya gane min irin soyayyan da sukeyi kamar yara ko a gaban kowa. Daki na nufa zuciyana cike da maganganu kan zancen mu da Abba dana mommy din da mukayi watau dai Abba har yanzu ya dauki zancen Ahmed da zafi a ranshi ? Ni banga wani illa dake ga Ahmed din ba da ko yaushe Abba ke kiranshi da kaskantance kawai dai rashin fahinta ne wani tambaya ne yazo min to ko Ahmed din baida ubane shegene da Abba ke fadin baida asali ? Gabana ne ya fadin yin wa kaina wanan