← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 286

Sashe 122

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ana kama a duniya haka ? Wallahi shekaran jiyan nan wani matashi yazo shegona sai ka rantse da Allah yasir din gidan nan ne sai dai idan yai magana zaka gane bashi bane. Wani kallo jabbi dake gefe yayi mashi amma ya basar don maigidan ya dan daga a lokacin ya shiga ciki zai daukowa aminim nasa sako tellan ke fadin haka. Mikewa tayi tana daukan kayan tare da fadin jeka zakaji alert tayi tsaye har saida taga fitanshi daga gidan ta juya ta shige ciki sai jin wani abu takeyi a zuciyanta na tashin hankali da fargaba. Kayan ta jefa a gefen gado ta jawo waya ta fara neman layin wata yar uwanta dake Gembo cikin tashin hankali take fada mata abinda ke shirin faruwa dasu. Mikewa tayi kamar a gaban yar uwan nata take ta soma fadin wanan karyane wallahi irin abinda mukayi muka bizzine za ace yanzu wai yaron nan yazo ya baiyana. Wanan ma karyane wallahi in ko har haka sai mu canza mu koma wani hanya me zamu tsaya jira dama kin daiji abinda ake fada cewa muddin ya baiya zai doke duk zatin da taurarin diyan ki ga baki daya zai dushe. Shi nakewa tsoro ya Lantana idan ina kaunan mutuwana ina kaunan yau in bude ido inga wani da a gidan nan da sunan dan Alh ne shima koda kuwa diya macece ita bana kaunan hakan. To kingani inda mukaje aka bawa kare mahaifar wanan gajan kishiyar taki aka daureta can zamu koma mu kara matsesu a saka masu duhu a tsakanin su har abada. Don haka kiyi dubaran da zakiyi ki fito gobe mu sanu muje wanan kauyen don kinsan wuyan zuwa ke dajin arnan nan don hawan dutsen nan dake wajajen . Na sani idan ba dole ba wallahi ban son zuwa wanan wajen saidai ba yadda na iya tunda ina son biyan bukata in sha Allahu gobe din dai zansan yadda nayi nafito muje wurin. Allah ya kaimu ta fada suka dan taba hira aka kashe wayan kowa ya zauna yana cicika a zuciyan shi tare da tuna irin kudin da suka kashe a baya. Yallabai ina zuwa zanje in dawo yanzu jabbi ya fada yana saurin tashi daga inda yake zaune Alh ya bishi da kallon mamaki yana tunanen inda zaije haka da sauri har yana tunanen ko lalura ya kamashi. Allah ya taimakeshi ya samu wanda yake son gani din a lokacin har ya tare mashin zai hau ya tare shi don haka ya tsaya . Ya sanshi farin sani don customer shine a wurin dinki sosai bayan sun kara gaisawa ne ya dan duba baya kafin ya fara fadin. Ka gafarceni kan maganan da nake son muyi yanzu in har hakan ya zama kamar katsalandan a garejku don zakaji maganar kamar ina son maka kutse a cikkn sa yanzu. Kan isa tella din ya daure kafin yace Alh lafiya dai ko don ban dahinci inda zancen ka ya dosa ba yanzu yace eh hakane gaskiya ba zaka gane ba sai na fada. Dama game da maganan nan danaji kana fadawa hjy shine a yanzu na yaron da ka gani sunyi kama da yaron wurin Alh don Allah ko ka san inda zamu sameshi. Kallon mamaki isa din yai mashi kafin yace dashi Alh wallahi ban sanshi ba nima haka kuma ban san daga ina yake ba illa abinda na sani shine. Sun kawo dinki shagona munyi dasu su dawo gobe jumma,a su karba da karfe hudu na yamma shine kadai abinda na sani game dasu din. Amma bayan haka bansan komai a game dashi ba wallahi zaka taimakemu don Allah nan dai ya fada mai abinda yake son yai masu na taimako kuma iya shi yasan da wanan zancen ya kama bakin shi. Insha Allah in har ya yaimaka masu akwai goron da zai samu kuma ba zasu taba yarda hjy tasan da zancen ba don kada su hana mashi hanyar samu daga gareta da diyanta. Basu kai ga kare maganan ba kiran hjy ya shigo a wayan isa din ya dauka ba sallama ta fara fada dashi kan baida hankaline ko wayau zai fada mata magana irun haka a gaban wani. Hakkuri ya fara bata saida kyar ta yarda tayi shiru tare da fadin to ka iya bakin ka don nasan wanan munafukin zai bincike ka akan maganan nan watarana duk daya nuna ba komai a hakan daya nuna a falon dazun yace insha Allahu zaiyi yadda tace din. Kallon juna sukayi ya kashe waya ya dan murmusa yana fadin aina fadama wanan marar akwai abinda take boyewa wanda bata son asani. Sun dai gagauta tsayar da zancen sukai sallama ya tafi shi kuma ya juya ya koma ya samu Alh yana fadin ya dan kewayane sukaci gaba da hiransu a wurin. Hjy ta fito kamar tana neman wani abu a lokacin shi jabbi ya gane me take nufi da haka yai kamar bai fahinci komai da hakan ke nufi ba. Kamar yadda suka shirya da isa din hakan ya faru bayan dan bayaro yazo yake tambayanshi ina abokin shi yake fadin ai bayanan ya koma garin su ko. Daya karbi dinkin ne ya hau mashin shima ya hau yabi bayan shi har zuwa unguwar su dan bayaro din yaga gidan da yashiga din. Ya juyo ya dawo shagon shi ya zauna ya kama bakinshi har zuwa tashi ya samu wuri ya kira wayan Alh Jabbi yai mashi bayanin unguwan da siffan dan bayaro din. Yai mai godiya ya kashe wayan yana kiyasta yadda zai bullo idan yaje unguwan don wanan lamarin yana son taka tsantsan a cikin sa.
Chapter 122 · 0% Book details