← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 217 OF 286

Sashe 217

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan kamun ya cika da mata yan zuwa buki ga al,ada ranan kamu yakanfi ranan buki cika don wasu idan sunzo kamu ko basu samu zuwa sauran event din ba ya wadatar dasu da mai bukin. Daya daga cikin atamfam aurena na saka don shi master yafi son in saka kayan da yai min idan zanfita wani sha,ani na buki cikin family mu bansan meye manufansa hakan ba. Korene da adon fari da baki jikin manyan ganye da aka zanawa atamfan sai dinki three quarter da akai mun dashi hannatu cema takaiwa tellanta yai mun dinkin. Bazan ce duka ba amma tunda muka shigo nida hannatu idanuwan mutane ke kan mu bansan meyasa hakan ba ko kuma nice me tsarguwa da hakan oho ? Gaisawa muka farayi da idon sani wasu na min korafin sun dade basu ganni ba wasu kuma kallon dai gayanan dai yadda suke minshi a wurin. Har muka kai inda yan gidan mu suke zaune muna gaisawa sai naga suna wani kawar da kai gefe kamar basa son su gaisa dani a lokacin. Nan na barsu na ketara wani dan fili dana gani a bayan su naja hannatu muka ketara wurin muka tsaya muna kallon wasan da akeyi mata nata kwasan rawa ga mai Dj na sake kida garesu. Mutane kiri kiri suke zuwa kaga mace komai girmanta ta tsugunawa Aisha da Rukkaiya suna gaida su niko bama wanda yasan Allah ya aikoni wajen a lokacin. Ada idan naga hakan farkon aurena nakan damu amma yanzu abin yabar damuna saiga hjy tsohuwa an fito da ita dungwi dungwi har inda suke zaune din ana kokarin kafa mata kujera a tsakiyan su. Kai duniya abin tsoroce gaskiya watau kadai idan baka dashi dakai da babu duk dayane a wurin mutanen yanzu zan iya cewa zurian mu kaf a wurin gwaggo shafa nake jin dan sanyi saiko matan baba iro dake gwada min kawaici cewa ni diyan baba Iro dince . An fito da amarya ana likin kudi gwaggo shafa ta matsa dayi min hannu wai in fito dole yasa na fito din nida hannatu na fara zuba yan dari biyu nan mai kirari ta dan wasani tana fadin ai bansan kina wajen nan ba yar gidan Ali custom ruwan sanyi masu aiki sannu ance bel,bela cikinta baki saman ta fari toke bel,belace ta masar cikin da wajen ki duk farine sai mai hankali yake gane hakan . Wanan kirarin ya kara jawo hankalin mutane a gareni da akace yan gida su fito zalla su fanshi amaryan su ma na fito na zuba dari biyar biyar sabbi fil dasu sai abin yabawa mutane mamaki kuma. Ni da nake matar fakiri ina na samu wanan kudin nake famsan kaina nazo zan koma inda muke tsayene naji anty Aishan mu ta jawoni na dawo baya na gane magana take son min don haka na dan tsuguna a gabanta take fadin. Wai zahra meyasa yanzu kike son mayar da kanki yar kauye ne ji wanan shigar da kikayo zuwa wanan wajen kin kyautawa kanki ke nan duk kin koma wata bagidajiya yanzu dake. Kai Anty Aisha me shigana yayi mijinane fa ya dinka min su don haka dole in saka ji don Allah ke wakikafi miji idan ana magana saikiyi kokarin jefowa mutane zancen miji mikin ki bakauye da bai san komai ba don Allah ja can kina zubarwa mutane da aji kawai. Rukkaiyace ke fadin hakan a hasale mutum ma ai sai yaji kunyan nuna ta yanzu hjy dake tsakiyansu ta fada dama jira nake tasa baki in fada masu magana don nakai wuya. Ba sai nayi wani shiga ko nuna hali za a san cewa niyar Abba bace don jini ya rigada ya gaurayu da anta yanzu ko anki ko anso dole a lissafani a cikin yayan abba dai kuma ace ni din jikanki ce. Wa zaki fadawa magana Rukkaiya ta fada a hasale don ma ita anty Aishan ce data tsaya wani maki magana indonni ki fito fiye da hakan bai dameni ba wallahi. Nace koni hakan don na tsaya a iya inda Allah ya ajeni banje roko a wurin kowan ku ba kudin kuma ba fina kukayi da komai ko kunfini kuma bani bakin cikin da hakan saidai na kara godewa Allah na. Wanan ya jawo hankakin mutane a wajen don har su gwaggo shafa suka jani ita Rukkaiya bata bar zancen ba sai fada min bakar magana mai cin zuciya takeyi. Haka aka tashi baram baram da akazo gida ana magana kuma mama ta dinga daga murya sama tana fadin maganganu munana akan mu jin hakan yasa ummah tace dani bukin ya isa kada ki dawo jibi tunda abin hakane. Jin hakan Tani da hannatu sukace wa ummah idan anyi min hakan ba ai min daidai ba ai Allah bai raba daya ba dama ke in gajarce maki naga abubuwa ba ga yan gida ba baga yan waje ba saboda ana min kallon matar tallaka ko yaushe. Bandashi balle nabawa wani yaci a karkashina hakan kuma bai hana inbi yan uwan nawa ba haka kuma na dawo gida cike da bacin rai yaushe ne zanyi farin ciki a rayuwanane wai. Ba kowa yaja min haka ba sai mahaifin mu daya nuna nida uwata bamu da muhinmanci a gareshi a gaban kowa zai nuna ra,ayinshi na wariya don abin ba a iya boyeshi ma. Balle yanzu daya kafa min doka da Allah ya isa ga duk wanda yabani wani abinshi don kawai bacin rai dayayi dani kan wai na nace Ahmed nakeso da akai min kazafi kuma na hakkura na zauna dashi hakana. Duk kuwa da gallazawan da mahaifiyan shi ke min a fakaice amma naba kaina hakkuri bantaba kai karan hakan a gida ba ina zaune ina hakkuri da duniya da abinda ke cikinta. Wanan fitinan yasa ranan ina kwantawa nayi mafalki wai ina zaune gidin iccen tumfafiyan nan na gidan nayi tagumi sai kawai naga Ahmed a gabana ya baiyana. Hannu ya miko min na dago kai na kalleshi ganin hawayen dake bin fuskana yasashi kada kai ya mikar dani tsaye maimakon inga munbi hanya shiga gida sai naga ya nufi cikin tumfafiyan nan dani saiga wani haske fau ya baiyana ya kashe min ido a daidai wanan lokacin na falka ina salati. Yana gefena ya zabura yana kiran sunana tare da fadin ke zahra lafiya ko mafalki kikayine wai yana lalubo torchlight din shi ya haska min hawayene fam a fuskana ke nan hawayen da nakeyi a cikin mafalki har a fili ke nan. Ga kukan uwargarke nan mai ban tsoro dake tayar min da tsikan jikina tanayi a lokacin hakan yasa na dan koma gefen shi na kara lafewa ina sauke ajiyan zuciya. Wani lokaci mafarki yakan zamo gaskiya saidai mutum ya kula akan abinda yake zama kamar bushara agareshi idan yai mafalkin dashi don akwai wasu dake gane cewa wani abu zai faru dasu idan sunyi mafalkin dashi dolene sai wani abu ya faru da mutum a lokacin. To nima dai hakan nayi tunane don in baki manta ba lokacin da nayi mafalki da uwar garke da wanan tumfafiyan saida nayi ciwo sosai a baya yanzu kuma gashi na sakeyi wanan ne ya daga min hankalina tundai da naji kukan wanan dabban mai firgitarwa a lokacin sai na kara shan jinin jikina. Yayi min tambayan duniya ban bashi amsa ba yasa ya kyaleni saida safe ya kara tayar da zancen gareni ya tambaya wai me kikai mafalkine ya daga maki hankali jiya ? Shiru na sakeyi yace oh yanzu na gane kinyi mafalki ke nan dani cewa na mutu ko shine baki son ki fada ya zama gaskiya. Jin hakan yasa nayi magana nace a,a wallahi nidai kawai mafalki da wanan akuyan da kuma dan iccen tumfafiyan nan na gidan nan shine banso don yana zama min matsala idan nayi. Au kema kina mafalki dasu ke nan ashe na dauka ni kadaine nake mafalki dasu ai a gidan nan don in fada maki gaskiya duk abinda kikaga inayi wanan abin yasa naki yarda mu hadu da mahaifina har yanzu don abinda akai masa a kaina har yanzu bai fita a jikinshi ba duk akwai saura a jikinshi game dani amma an kasa gane hakan . Gashi ba dama in fadawa wani wanan maganan sai a dauka shirmene kawai irin na kurciya nakeyi don hakane naja bakina nayi shiru saidai ban yarda mu hadu sai lokacin da abinda suka fada ya faru zan yarda in tsaya dashi din. To shine ko Dije ba zakaiwa bayanin haka ba ita zata fahince ko kowa bai yarda da hakan ba nasan ita zata fahinci me kake nufi shiru yayi na dan lokaci kafin yace wai zahra kodai kaddaran mu dayane dake dama ? Kaddara kuma kamar yaya kaddara mu daya dakai dama ki barshi kawai ya fada ya mike zuwa kitchen ya dauko ruwa ya dawo yana sha kafin ya zauna yace. Cikin Matan da mahaifina ke aure akwai muguwa a cikinsu duk da bansan su ba amma ana nuna min a mafalkina cewa sune matar farace gajera mai dan jiki tana da tsaga irin na fulanin asali a jikinta. Abinda kawai zan iya shedata ke nan a fili dashi ke kadai na fadawa wanan zancen don ina yawan ganinta sosai a cikin mafalkina don haka nake son na shiryawa tunkaranta kafin mu hadu. Shiru nayi tare da nazarin maganan shi a cikin zuciyana haka kawai zancen gidan mu ya fado min a rai nan nake bashi labarin abinda ya faru a wurin buki dani. Baiyi magana ba saidai idon shi ya ja sosai a lokacin kiran wayanshi ya watsa mu wurin don nadaga na tafi dora girki a lokacin shi kuma naga ya fita bayan ya amsa wayan. Yadda ya dawo a cikin damuwa yasa ta kasa tunkaranshi a ranan do baiba da kofan da kowa zai shigo wurin shi saboda ya rufe dakinshi. Washe garima sai rana sosai ya bude dakin ya fitp don neman abinda zaiciwa cikinsa don yunwa daya dameshi saboda rabonshi da abinci tun safiyan jiyan da sukayi karin safe a gidan ubangidanshi da yanzu tsofa ya kamashi sosai kuma arzikin ya tafi baida komai sai hakkuri da tawakkalin ubangiji. Yaji dadin zuwan yaronsa a lokacin wanda da kyat ya ganeshi
Chapter 217 · 0% Book details