← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 224 OF 286

Sashe 224

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

daga dakin yana adduan Allah ya buda mashi ya bar masu gidansu. Zai shiga cikin part din mu yaro yayi sallama yace ance ana sallama da Ahmed idan yana gida yaja ya tsaya tare da tambayan waye yace wasu masu babban motane suke sallama akofa. Cikin mamaki ya juya ya fita zuwa ganin wanda ke sallama mashi a lokacin baiga kowa ba sai motoci guda biyu masu kyau da tsada zai juya yaga an bude kofan motan malam bala driver ya fito yana mashi sallama. Ya mika hannu cikin mamare duk lokacin ranshi yana bace da zancen da Dije din ta fada mashi ya faru tsakanin mu da inna din akai masa sallaman yafito don haka ya fito masu rai a bace lokacin. Mahaifinkane yazo yana mota ya bashi amsa da hakan banda mahaifi ya fada yana juyawa a daidai lokacin da dogon bafulatanin mutumin ya fito daga motan shima. Wayan shi dake ringin ya dauka sunan mama ya gani saida yaja tsuki ya daga wayan tayi sallama ya amsa suka gaisa ba wani damuwa da yanayin canjin muryan shi a lokacin tace dama zancen kudin nan ne naga baka turo ba yasa nakiraka yanzu din. Wai meyasa ku mata baku da hankaline meyasa duk halinku dayane komai shekarunku to banda kudi ki zo ki daukeni ki min wanka kikai kasuwa idan kin sayar dani sai ki dauki kudin. Alh daga tambayan kudi zaka hauni da fadan bakar magana haka inma wata ta bata maka rai ai bani bace na bata ma saikayi da maishi bani ba. An fada maki nace an fada maki zancen banza zancen wofi baku da wani zance ga mutum saina kudi kullun cikin turo maki kudi nake har yanzun baki gode ba to banda su kinji na fada maki ya kashe wayan yana huci. Ya dan dade a kwance kafin ya mike zuwa wanka don ranan jumma,a ce ranan yana son shiga sallah a lokacin yagama shiri zai fita wayan ta sake kara a zatonshi mamace ya bar wayan har ta katse. Andan dauki lokaci yana cikin mota ta sake kiranshi ya daga yana tsuki ba tare daya duba wake kiran nasa ba yaji muryan ummah tana fadin Alh ina kwana tun dazun nake kira baka daga ba. Ya amsa mata a darare suka gaisa tace baka jin dadine halan tun jiya ina jin muryanka wani iri yace kwana biyun nan bana jin dadin jikin ayyah Allah ya dada sauki na kirane dama mu gaisa Allah ya bamu Alheri ya kara lafiya yace amin yana kallon wayan. Tayi mai sallama ta kashe wayan yabi wayan da kallo yana sauke ajiyan zuciya tare da jin natsuwa yana shigan shi lokaci guda ya lumshe idanunshi har suka kai masalacin driver ya samu wuri yayi parking suka kulle motan zuwa cikin haraban masallacin. Mamako fada ta dinga yi dashi sosai tana fadin wai mata haka muke yanzun haka kilakiyar matarshi ce ta bata masa rai yake son fashe haushin hakan a kaina. Tayi fada sosai kafin yarta ta kirata tana fada mata angama aikin da suka bawa wani ba,are yayi masu akan yaranta dama ita mama din tace zata turo da kudin gobe. Zuwa yamma bata daddara ba ta sake neman layin Abba din kamar yadda suka saba kiranshi a kullun kirane ko yaushe zuwan hjy karima ce ma suka daina waya kamar yadda sukeyi dashi din. Bai daga wayan ba sai abin ya kara batawa mama din rai sosai ta hakeshi kan zai sauko zasu kwasa dashi idan ya kira ai ta jefar da wayan tana huci . Shigowan wayan Aisha ce yasaka ta dan bar zancen bawai abin ya fita ranta ba a lokacin Aisha din ke fada mata yadda sukayi da dangin mijinta taci masu mutunci don haka tasan manya na tafe zata shiryawa zuwan nasu suma. Kiri kiri yaki tsayi ya shige gida ya barsu da mamaki a kofan gidan don shi kanshi dan gaske bai taba tunanen zuciyan yaron yakai haka ba sai lokacin. Malam Tanimu aka sallamo masu ya zo yayi masu sannu da zuwa ya shiga gidan yana fadawa Dije zuwan nasu zo kaga kame kame a wurin su dije din lokacin. Na bar labari baya don wancan lokacin na fada maku da mahaifin master yazo yayi rabon kudi ga duk wanda rabon shi ya tsaga a lokacin . Bayan wuce wansu ne inna ta dinga cewa na ranto mata kudin duk ta karbe a hannu na da sunan aro har yanzu babu wanan zancen gareni. Ko Aishace don tafi Asmau dama sosai halinsu akwai babbaci don Aisha tafita sanin ya kama inaga itace ta fadawa Dije abinda inna din tayi min harda take fadin ai mahaifina bai taba ba ko Ahmed din wani abuba nima. Ni dai naji shigowan shi amma gaskiya bansan fitanshi daga gidan ba sai gashi naji ana sallama na fito baba tanimune a tsaye daga kofan mu yake fadin sallamo muna mijinki don Allah na juya da sauri zuwa ciki. Sai gashi na fito har kitchen na leka na juyo ina fadin baba baya gidan nan amma ina ciki naji shigowanshi bada dadewan nan ba gaskiya. Sai ga yayi murmushi yace mahaifinshi ne yazo kuma ya gansa ya boye ne wata kila sai abin ya ban mamaki don yana da karfin hali gaskiya da mace ce aiba sai an tsaya kiranta ba zata kawo kanta wurin. Wasa wasa har dije da kowa saida suka shigo nemansa suka tabbatar baya gidan lokacin hakan yasa suka san dai ya gudune don kada su gana da mahaifin nasa. Inda kowa yaji ba dadin hakan da yayi don ba sai ya tsaya yana nuna hakan ba za a san yayi zuciya ai amma hakan daya nuna tozarcine ga mahaifin nasa dama shi kansa ai. Ku kyaleshi wanan karon kwana zamuyi anan dole dai ya dawo gida ai idan ya dawo ku fada mai yayi hakkuri ya sauko daga fushinshi mu fahinci juna dashi don Allah. Bani kadai ba duk wanda ke wajen kalamin mutumin yabawa kowa tausayi don yadda a yanzu din ya damu da dan nasa gashi shi kuma ya nuna shi jinin fulanine wurin riko da zuciya. Ganin haka yasa na kirasa da kyat ya dauki wayan nake fadin kana inane kaiko don Allah bayan kasan muna da baki a gidan. Yace gani nan zan shiga zaria daga nan kuma gaba nayi kiyi hakkuri ban samu yin sallama dake ba don nasan zaki hanani tafiya a lokacin yasa na tafi ban sallameki ba. Kiri kiri mutumin nan ya tafi don a karshema kashe wayansa yayi babu mai samun shi don kawai dije ta soma mai fada tana nuna bacin ranta ga yadda yayiwa mahaifin nasa. Saida ya share sati uku masu kyau baya gida dole ya gaji ya dawo kwatsam da dare ya shigo garin babu alaman wahalan komai a jikinshi ya dawa a daidai lokacin bukin da za ayi a family house namu. Don haka washe gari nikan na shirya na fita zuwa gida don dama a matse nake da inje gida a lokacin don haka sai bayan fitanane Dije ta sameshi suka kwasa sosai dashi har tana fadin zata bar masa gidan tunda tona masu asiri yake sonyi. Yace tayi zaman ta dama shi yazo ne ya dauki matarshi su tafi don gab yake daya soma aiki a yanzu don haka zai tafi da matarshine can . Jin hakan daya fada sai kuma hankalinta ya tashi sosai nan kuma ta shiga lalashin shi tana bashi baki akan ya tsaya ya saurari mahaifin nasa kada Allah ya kamashi da laifin aikata hakan. Kace zaka dauke matarka ku tafi ni kuma idan kun tafi in zauna dawa Amadi ta fada tana kokarin sake masa kuka nan kuma ya soma magana yana fadin duk inda zani dake zan tafi dije amma sam hankalina bai kwanta da in yarda da mutumin nan ba a yanzu gaskiya. Kul ma karajin ka kira mahaifinka da sunan mutumi zan saba maka rai yanzu nan wai hankalin ka daya kuwa Ahmed ko kaima asirin ya shafekane wai ba a sani ba. Kukan akuyan su da kwana biyu kamar bata da lafiyane ya katseshi fadin abinda yayi niyar fada a lokacin.
Chapter 224 · 0% Book details