← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 197 OF 286

Sashe 197

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance yake ya lafe zakace barci yake a lokacin saidai a zahiri ba barci yakeyi ba tunane fam a zuciyar shi da suke hanashi sukuni a wanan lokacin tun bayan da hankalinshi ya dawo gareshi. Irin wanan yanayin yake damun shi har yakanyi kokarin fita hayacinshi wani lokacin a cikin hakane yana kwancen wayan shi ya dauki kara lokacin guda. Hakan yasa ya motsa har zaka gane ba barci yakeyi ba a lokacin damuwane kawai yai masa yawa na tunanen dansa da yake ganin ya mutu a lokacin kamar baya raye. Wanan ya jawo mashi damuwa har yanayinsa ya nuna kamar yana cikin rashin lafiyane yanayinsa ya nuna ya mika hannu ya dauki wayan yana duban mekiran nasa alokacin. Daya daga cikin yan uwansa kuma abokin nasane daga gida yake kiranshi a lokaci ya dauka suna gaisawa tare da tambayan iyalin juna a tsakanin su. A karshe yake tambayanshi ko lafiya yaji muryanshi haka yake fada masa damuwan shi shiru yayi yana sauraron bayanin da yake masa a lokacin. Bayan sun gama wayan da shi jabbi dinne yaga rashin kyautawansu na rashin sanar dashi gaskiya akan dan nasa da yanzu ya kwallafa rai a tunanensa fiye da komai lokaci guda. Hakan ya kara tabbatar masu cewa asirine tun farko akanshi kan dan nasa yanzu kuma da taimakon ubangiji kamar komai ya karye a kansa din a yanzu. Shiryawa yayi ya fice daga gidanshi sai gidan jabbo ida ya sameshi da maganan tare da shawara akan lokaci yayi da zasu sanar mai da gaskiyan al,amarin kada Allah ya kamasu da laifin hakan a kansu. Shima Jabbo din yace dashi nasa tunanen ke nan don ya fahinci cewa aminin nasu yana cikin wani hali a lokacin a nan dai suka yanke shawara kanshi cewa zasu sameshi a abuja akan zance biyu na ya mayar da hjy matarshi dakin ta da kuma zancen baiyanan dan nasa garesu. Sun aje magana kwana biyu mai zuwa zasu sameshi can abujan ba tare da sanar masa ba daga can sai asan abinyi zuwa wurin iyayyen yaron tare dasu. Yau asabarce bana fita ko ina a ranan nakan zauna inyi dan gyare gyraren gida nayi wankin yan tufafin dana saka a cikin satin in goge duk wanan aikin aurena a gidan Ahmed na koyesu a yanzu. Don da can baya wanan aikin saidai duk masu aiki suyi min iyakata na dauka in saka idan an wanke an kawo min su dakin wanda tanice take karbo min ta jera min su a wardrobe dina. Sai gashi yanzu nice da kaina nake wanan aikin wanda yakin mata ya saka min hakan nayi wanki na dafa abinci naci kuma irin hakan sai duk abubuwa su taru suyi min yawa a lokaci daya wanda duk sanadin aure na riski kaina a cikin hakan yanzu. Saidai duk da hakan ban faye damuwa da wanan yanayin da nake cikinsa ba a yanzun din don na fawalawa Allah komai game da rayuwan nawa a yanzu din. Saidai banda kuzari wanda ban fahinci hakan rauni bane a gareni saida inna ta fara korafin hakan a gareni idan ina girki zatace ba zasu girka ba tunda na dora da rana tafi yin min hakan idan ina gida ban fita ba. Saidai kafin na gama korafine hakan ne yakan biyo baya zata fara yada magana ta yadda zanji tana fadin mace kamar ba jini a gareta aiki sai kace tsohuwa na aiki ? Kamar wace ba lakka a jikinta ai tsiyan abin ke nan a nunawa yaro gatan da baida rana a gareshi yanzu gashi me gari ya waya a hakan ace diya mace ba zata iya aikin da karamar yarinya zatayi shi ba cikin sauri. Tun ban damuwa da hakan har yakai na fara damu ina nuna bacin rai har wani lokacin nakan kare aikin ina kuka na bakin cikin irin yadda inna ke nuna min kiyayya a fili. Dondai shida ya ajeni bai taba nuna min hakan ba illa ma ya taimaka min da wani aikin irinsu wanki da sharan gida amma ita inna ga yaranta bata ganin laifinsu saidai laifina zata gani a lokacin . Na samu nagama da kyar nakai masu tunkan na dawo part dina naji inna nafadin ai mukan mun shigesu da cin yaji kan agidan nan sai kaga mace har mace fes a waje amma ka bincika bata iya aikin daya dace ba wai a haka ake auren ? Itako Asmau cewa tayi ai inna yajin yayi daidai gishiri daine ba a sakaba a cikin girkin tana fada tana kai cibi abinki da zafin shi yadda na kawo masu shi lokacin. Wani bakin ciki da takaicine ya rufe min idona lokaci guda na juya na wuce ina hawaye sai yau nake tabbbatar da zancen ummah a gareni idan tanayi min fada lokacin da nake gida takan ce dani. Gara ki koya tun a gida dan zaki je gidan wasu kiyi kigama kuma ba a gode maki ba karshe ma kiji wullakanci ga hakan don wasu dangin miji bala,ine. Nakan ji haushin wanan kalamin na ummah lokacin sai inga ina ruwana da dangin mijina tunda basu zasu aureni ba a haka har na koyi dan abinda na iya a gida. Ko kallon abincin banyi ba duk da yunwan da nake ji haka na fada saman kujera ina hawaye ni kadai a daki ba mai bani hakkuri kan wullakancin inna da diyanta da nake gani a lokacin. Firgigit na dago daka yadda nake kwance don jin kukan akuyan nan da yanzu nayi noticing din kukanta idan tayi wani sign ne a garemu da cewa wani abu mai muhinmanci zai faru a gidan ke nan. Bansan koni kadaine nayi noticing din hakan ba amma tun bayan faruwan mafalkina da ita da har na kwanta ciwo din nan na fara gane hakan akanta damuma dake gidan. A hankali na dinga jin dan magana daga cikin gida yana tashi sai tarin da nake ji na muryan inna din a lokacin banyi niyar fita ba dole din jin hayaniyan yayi yawa na fito zuwa sashen nasu. Innace wai ta kwarai da abincin tana ta faman tari har tana kwalla daya dan lafa taje yin magana sai tari ya biyo baya nima na shiga cikin masu mata sannu a lokacin. Ta wahala sosai a ranan dole tana ganin abincin ta barshi nan data samu ya lafa mata takai kwance sai barci nan Dije ta soma fada tana fadin aiga irinta nan. Yarinyar nan taga aiki a wahalce ta kawo maku amma ke da yarki mara kunya kuka dinga musgunawa kuna fadin abinda kuga dama akanta ga abincin nan cinshi ya gagareki a yanzu ai. Nan Asmau ke fadin ji Dije da wani magana don Allah anga abinda baiyi daidai ba ba za a fadi ba ke nan ni ai gishirine nace baiji ba inna tace yayi yaji kuma ? Da yake kuna munafukan Allah ba wanan abincine za ace yana da matsala inji dije din sai Aisha tace nidai wallahi banji matsalan komai ba a girkin nan banda dadin da yayi kamar na sayarwama. Murmushin yake nayi na juya zuwa part dina wanka na shiga na fito bayan na daura alwala nayi sallah Azahar kafin na saka kaya a jikina bayan na shafa mai na koma kuryan dakina na kwanta don indan samu hutu a lokacin. Cikin ikon Allah sai barci ya dan fara daukana har da dan mafalkin gidan mu da yan uwana can cikin barcin nake jin kukan akuyan kuma again haka yasani bude idona a lokacin. Wayata na samu tana ta kara a lokacin ina dauka naga number kasan wajene a zatona Ahmed ne yake kirana da sauri nakai hannu ina danna dauka. Muryan bature ne a layin yake magana tare da fadin koshi waye mai karatu idan baki manta ba kin tuno da wanan dai baturen da sanadin sayar da gwanjon Ahmed yasa muka sanshi a baya wanan karon ma shine dai me kiran layin nawa don da shine mukayi amfani lokacin muka kira layin shi da muka gani din a baya cikin kayan gwanjon. Shine yake min bayanin cewa shine a layin lokacin na nuna farin cikin sake jin ya nememu yake tambayana Ahmed din nan nake fada mai cewa yana nan yazo US yin wani interview. Wani turancin nasa ba ganewa nakeyi ba duk da nima a cikinsa zance na taso don duk karatuna a private schools masu tsada na Abuja nayisu har na soma hada digree dina a nan kafin mama tasaka a dawo dani nan zamfara da kaddaran aurena da Ahmed ya kirani a nan din yanzu. Don sam ban kawo zancen aure haka a rayuwana ba koda nan da shekara biyar masu zuwa amma kaddara ta riga fata gareni. Ina da burin inga na taimakawa rayuwan ku duk da bansan ko baku bukatan hakan a addinin ku ya fada cikin yi da muryanshi kasa alaman damuwa karara a muryan nasa. Zanyi shawara da mijina zan fada mashi komai game da kai duk abinda ya fada kabamu nan da two days ka kira kaji yace ya gode ya kashe wayan nayi ajiyan zuciya a bangarena ina aje wayan a gefena. Idona rufe a hankali ina ci gaba da tunanen abinda zan fada masa gashi tun bayan tafiyan shi bamu samu waya ba balle nasan halinda ake ciki a can gashi ba wanda yasan inda ya tafi saini dashi da ummah data san da zancen. Gabanane ya fadi lokaci guda don shedan daya kawo min wani tunanen cewa wai idan brother Bisi yayi wani tsafinsu na yarbawa dashi fa a can me zan fadawa iyayyen shi ke nan. Nan hankalina ya kara tashi na jawo waya na kira ummah hankali a tashe bayan mun gaisa nake fadin ummah har yanzu fa tunda ya tafi bai kirani ba. Tace Ahmed din nace eh ummah hankalina ya fara tashi kada wani abu ya sameshi a sanadina iyayyen shi suyi kuka dani duk da ba wanda yasan da zancen tafiyan a cikinsu don yace kada in fadawa kowa sai idan zancen ya tabbata a sani. Addu,a zakiyi masa a duk inda yake Allah ya tsare shi ya dawo muna dashi lafiya gaskiya ya fada na rashin fadin komai a yanzu din don yadda yanayi ya koma a yanzu. To amma rashin sanar dasu
Chapter 197 · 0% Book details