← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 270 OF 286

Sashe 270

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gidan Ashibi kuma mama don Allah me zakije yi gidan wanan yar borin matan yanzu kuma kudin ku kawai take ci banza fa wallahi da sauri mama din tayi mai dakuwa tare da fadin kaci ubanka nine zakayiwa wa,azi. Na gane meke shirin faruwa yasa nace to yaya saika dawo ke nan ma hadu yace to zahra harna juya naji yace don Allah ko kina da dubu daya ki ban na samu abinda na karya dashi. Innalillahi na ambata a kasan raina tare da wani irin shock nace dubu daya kuma yaya me dubu daya zai isheka yi don Allah ? Barin zo na juya na tafi na dauko jakkata na fito can na hango mama da Aisha suna faman zazaga mashi bala,i ya rugume hannuwan shi cikin bacin rai yana sauraren su. Ban karasa wurin ba wanan yarinyar mai mun aiki na kira na bata takai masa naji tace dani wancan mahaukacin na gidan su hjy ? What me kikace tace nace wancan mahaukacin mai shaye shayen na gidan su hjy ko eh shi kai masa kice injini na tsaya har ta mika masa naji raina ya kara baci sosai. Shiko yana daga can yana dago min hannu irin na ya gode din nan sai ya dawo wasu irin hawaye naji sunzo min na kara gane da matsala dai kenan babba a gidan mu yanzu. Karfe daya yace zamu gidansu mu gaidasu mukayi sallama bani cikin walwala zuciyana a bace yake da abinda nake gani a wanan zuwan nawa gida. Shiru nayi a cikin motan kafin shehu yace zahra na ganki da Musa ai kuna magana ina shigowa na boye kada ya ganeni ya tsareni. Bari shehu amma akwai abindake faruwa dashi ko yace sosai ma kuwa ke bakiga alaman haka ba ai ruwane ya karewa dan kada bai gama wanka ba. Ya dade da shiga wanan halin ba a kula ba sai yanzune abin yake baiyana sosai gareshi uwar tana nan tana yawon malamai wai hjy namuce tayi masa ya koma haka. Kiji wani bata don Allah batayi masa ba tun yana karami sai yanzun daya girmane zatayi masa Master ya fada ba tare da ya juyo inda shehu din yake ba ya bashi amsa yana kallon hanyar unguwan nasu yace. Yarima fa yayi kokari sosai da jahan nan amma ku baku gane hakan sai zaginsa akeyi wai bai maku aiki ba kasan halin mutane mu ba godiya. Wai yariman bakura kake nufi yace kwarai kuwa shi yayi aiki a fakaice amma an kasa gane hakan sai zaginshi da mutane keyi kawai muna ji a kafafen redio ai. Har suka kai suna hiran siyasa ina zaune nida dije da bamuce komai ba kowa da abinda ke zuciyarshi muna shiga unguwa tasu tun daga nisa na hango gidan nasu yadda ya yakuce a rashin shi na yan shekarun nan da baya nan. Ikon Allah kangon mune ya kara yakucewa haka kamar ba mutane zaune a cikin gidan nan yanzun kai jama,a ta fada cikin takaici. Muka sauko a motan malam tani yana zaune ya kara tsufa sosai yanzu ya kuro muna idanu yana son yasan kosu waye sukazo. Dije ta taka zuwa wajen sa tana gaidashi nan danan mutanen unguwa suka shedamu aka fara taruwa a kan mu ana muna sannu da zuwa, nidai da kyat nake iya amsawa don abinda ke damun zuciyana lokacin. Gaba dayan mu muka dunguma zuwa cikin gidan muka samu suna barcin rana Aisha kuma tana school muke ta sallama can Inna din tafito daga daki. Kanta babu dankwali tana fadin wai wake sallama hakane da rana tsakan nan sukai arba damu tsaye yana bin ko ina na gidan da idanu ta fito a lokacin. A a a umma kune ashe kuna tafe Asmau Asmau ke fito ga su umma sun zo ta tasa yadda zatayi sai faman kame kame da takeyi a gidan lokacin. Ta fito da wani tsohon tabarman dije dana bata tun na kwanciyan zafi waje danazo gidan naga tsumman tabarman da take amfani dashi lokaci. Bai zauna ba sai zagayawa bayan da yayi zuwa wurin dabbobinsa yaga wayau babu komai ga iccen nan na tumfafiyanshi ya bushe yayi wani irin ja duk wurin tarkacene da sauran kayayyaki yashe a kasa. Ido ya runtse ya juyo ya dawo zuwa cikin gidan wai bisashe kaje duba ai babu ko daya tunda sukai ciwo na kwashesu na sayarwa rumjawa dasu. Baiyi magana ba sai dijece ke fadin wai dabbobin nasane kuka sayar Rashida akan me kuka sayar mashi da bisashe bai baku bakin haka ba. To me zayayi da kudinsu yanzu inji Asmau take ba dije din amsa a hasale kekan kin biyo halin uwarki da battalancin banza shekara nawa yaron nan yana kiwo abinsu sai a yan shekarun nan da bai garin kuka sayar masa da abu. Dakinta ta leka ta ganshi a gyare saidai da alama na cikin dakin ya canza fasalin dakin muna zaune nace sallah zanyi don lokacin yin sallah yayi. Part din mu ya nufa ya shiga yana dan dudubawa kafin ya fito yanawa she bayanin yadda za a gyara ginan ya koma don wai a nan dije zata zauna. Don tace bata zama sabon gidan mu ita inda mijinta ya mutu ya barta take son ta mutu junsan matan hausawa da wanan camfin a zuciyarsu. Sallah nayi a nan tsakar gidan na koma na zauna bayan na idar din ina bin ko ina na gidan da kallo kamar ban taba rayuwa a cikinsa ba a baya.
Chapter 270 · 0% Book details