← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 282 OF 286

Sashe 282

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

kallonshi cikin mamaki tace ina kasamu kudi haka har kake kyauta dashi kai tsaye yace wurin zahra nakai ziyara ta ban kudi jiya shine na baki kema ki sheda. Wani haushine ya kama mama ta kalli kudin ta kallesa tace maula kuma kajeyi gidan kanwarka kome baba ? Yace maula kuma don naje yin zumuta ta ban kudi shi za a kira da maula yanzu mama kinsan tsakanin sufa dama suna shiri sosai da ita to ni dai banson zubar da girma da aji ka rike girman ka har ina abin yake da har sukewa mutane daga kai yanzu. Mama ke nan don kawai ita zahra har mijinta basu da rigimane aida yanzu gari an sheda wallahi mama akwai kudi yaron nan ba karamin kuru bane ya karatu sosai don babbane a can ma,aikatansu. Don Allah baba ka rufa min baki da abin takaici shine me don ya zama babba kaiba kasan waje kayi karatu ba ka shiririta kanka waikai dan maye a yanzu. Mama don Allah ku bar zancen ya isa hakana yaya kana da abin hawa tare da kaine ka saukeni gida yace eh ai na gyara motan Hjy dazun a cikin kudin yanzu haka ita nake dan dagarawa. Barin biyoka ka saukeni gida dare ya soma kada yara suyi barci ban koma ba haka yasa ta mike da sauri tayiwa mama din saida safe suka fita wanan kudin bai kwana ba mama ta aika aka sayo mata kati da kayan tea ta kashesu. Can kuma cikin mota Aisha ce tace wallahi ina son zuwa kodon naga gidan nasu ina tsoron bacin ran mama ya musa ya juyo da sauri yana fadin me zatayi maki kuje kawai idan kunyi niya. Ni ba gashi naje na samo ba kuma kudin yayi amfani tunda na gyara mota mu samu na hawa dubu dari fa zahra ta bani cas dinsu kai yaya dubu dari fa a wanan lokacin yace wallahi ko Aisha. Shine ranan da inna tazo bayan an dauke ruwa ina daki kwance Aisha tazo tana fada min anty ga yan uwankin nan sunzo su biyu suna falo. Na dago nace anty Aisha tace su kun basu abin sha tace na basu komai shine nazo fada maki nace kice gani tafe na sauko na gyara kaina na fito a cikin fara ata sune dai din kuwa sukazo. Suna zaune sai bin ko ina da kallon mamaki sukeyi na iso ina fadin manyan baki anty Aisha kune tafe a cikin sanyin nan ban zauna ba saida na karbi dan dake hannun Rukkaiya ina fadin kai malam ya kake nakai zaune tare da yaron a hannuna. Ina gaidasu da kwana suka amsa nake fadin wallahi yau mukaso zuwa gaida mama amma ruwan nan ya hana dama master ne bai nan tunda sukayi tafiya dasu ummah sai jiya ya dawo garin nan. Dama shiyace sai ya dawo muje tare kada yayi laifi gun mama din ai kuwa mama zatayi fushi idan bakuje ba nan muka zauna muka wuni dasu komai tare kyautan da nayi masu da zasu tafi saida sukai mamaki nasa mota ya kai su har gida. Washe gari kuma tunda munyi niya gida mukaje wuni don tani na gidan namu zaune da kanne na tana masu komai a part din mama din muka zauna mun dade sosai ta nuna ba komai a zuciyarta sai fira muke zubawa da ita kafin na fito na koma wurin kanne na nan master ya barmu sai dare muka koma gida. Amma bayan fitowan mu wurin mama ya sa a shiga mata da tsarabanta da muka zo dashi har da kayan abinci da kudi tunda Abba bai kasan wanan dole yasa mama tasowa zuwa part din ummah tana fadin tsarabace haka duk ni kadai. Nace a a mama Amir ne yace tunda Abba bai kasan yana son yayi masa kwace aka kwashe da dariya tanawa yaron sheri ta dan jima muna wani hiran kan ta fita ta koma part dinta a cikin bakin ciki da takaici dake cinta. Don saida muka cika mata falo da tarkace a ranan da kayan abinci wanda an dan dauki lokaci ba a shigo da irin shi ba a gidan mu sai ranan dai haihuwa tayi ranan ta. Duk da dacin da mama keji a kasan ranta hakan kuma bai hanata jin dadin ganin wanan alherin data samu a wurin mu ba don abune da yanzun yake mata wahalan samu a rayuwanta karfin hali kawai akeyi irin na rayuwa dama. Sai gashi washe gari yaran nata sunzo kamar yadda suka saba zuwa din sunga canji kwarai gareta ranan tun wurin kawo masu abinci datasa akayi sukaga abin miya wadatatace nan suke fadin yau kan mama da nauyin ki gaskiya. Saida ta tabe baki tace eh jiya wa yan nan sukazo suka kawo muna abubuwa wai tsara kayan abinci kuma don Alh baya gari ko yana garin ma yanzu ina zan samu wanan din tunda komai ya kare ga Alh yanzu. Kallon juna sukayi kafin uwar tace in kun gama ku shiga ciki ku duba kuga abinda suka kawo min ni super din ma su sukafi daukan hankali da kayan abincin nan wallahi. Mama muma fa mun tafi gidan kuma taji dadi tayi muna alheri sosai wallahi tsoron fada maki mukayi muje gulmane amma sai ta taremu cikin mutunci ta rasa inda zata sakamu tana ta fadin yan uwan tane na haihuwa sukazo mata wuni daga gidajensu. Wallahi mama dole muka sake jiki aikai sha,ani zamu tafi a motan mijinta aka kaimu kowan mu gida tare da abin arzikin mu tace idan an kwana biyu zatazo tayiwa kowan mu yini a gidan ta. Humm,uwar tace tana sauke ajiyan zuciya tace tayi gadon kinibibin tsiya kamar uwarta baka taba gane gaskiyan cikinsu sai suyi ta nuna haba haba a gaban mutum kamar su din na Allah ne. Mu ina ruwan mu mama muma sai mu dauka kawai kamar yadda ta dauka a rufe ayi ta sha,ani sai Rukkaiya take fadin amma mama gaskiya suna da hakkuri koma dai meye su suna nuna mu nasune gaskiya . Yanzun da kikaga wurin ci kika gane hakan tona rabaki da yan uba da yar kishiya don ba zasu taba son kici gaba ba saidai ki koma baya. Kamar yadda yanzun suke ganin muci baya sun koma gaba aini Alh haruna ya ban mamaki sosai daya hana waj aje dani indiyan nan kiri kiri dan uwanka yai maka bakin ciki. Mama shifa baba haroon haka yake waishi fadan gaskiya duk za ayi abu sai ya nuna rashin dacewan abin idan yaga ba daidai ba nan take zai fadi gaskiya ga mutum. Nifa mama kwantawa zanyi don in gane kan shegiya kwana biyu kafin in fito mata da true colour dina in fara cin ubanta a mumuke a dafa kifi da ruwanshi zan mata ku barni da shegiya. Zahrace fa kada ku manta haka take kamar mai ira izai dake fada mata wahayi yarinyar akwai shegen wayaun tsiya da ita tun da can da wuya ka gane takon zahra wallahi. Ni yanzu ba wanan shirmen da kuke karantowa bane a raina abinda ya dameni shine in banyi hankali ba muna kallo komai na gidan nan zai koma hannunsu nan gaba kadan . Tunda yanzu Alh dai badai shi wanan yar matsiyatan ta yaudareshi a banza taci kasuwan ta tayi wasa da hankalinshi ta tattra komai ta tafi dashi. Shima Abba ai yayi sakaci wallahi Aisha ta fada tana jan tsuki cikin takaici da bakin ciki tana kawar da kanta gefe daya haka sukai ta hira wanda bana alheri ba har yamma kafin kowansu ya kama gaban shi zuwa gida.
Chapter 282 · 0% Book details