Sashe 206
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
take fadin shiko master ai hakkuri ya kamata yayi bawai ya rike mahaifin nasa ba haka. Nima abinda nake fada mai ke nan ya hauni da fada har yau din nan bai kirani ba waishi yayi fushi ke nan nayi alkwari kuma ba zan sake masa magana kan zancen mahaifin nasa ba duk abinda zasuyi nan gaba kuwa. Ya zakiyi wani abin aiba zaki san lokacin da zaki sa baki a ciki ba ke dai kawai kibi zancen a sannu tunda baison kina sa baki a cikin zancen. Bayan mun tashine daga school din muka rabu a hanya da ita ni kuma na nufi gidan mu ummah tana ciki bata falo don haka na bita daki na sameta zaune a kasa tana waya. Wuri na samu nima na zube a kasan ina ajiyan zuviya na fahinci da kawarta na Abuja aminiyar ta take waya a lokackn don maganganun da suke fada a wayan tasu. Magana ce data shafi Abban mu da hjy karima kamat sunyi wani case da itane har da yan sanda a cikin zancen nasu lamo nayi ina sauraren su har yakai na fada wani tunane a lokacin. Ta gama ta juyo tana fadin ke kuma daga ina haka ko mijin naki ya dawone a lokacin na dago ina kada ksi nace bai dawo ba ummah daga school nake na biyo nan in gaida ku. Asha mahmah da ilimin ki zaki hakan bayan kinsan cewa wanan yana cikin babban abindake halaka mata a yanzu shine ke zaki hakan. Mijjn ki baya gari ba waya kukayu dashi yace kizo ki dubamu ba amma sai ki dauko kafa kizo bada saninsa ba mahmah kada ki kara wanan halin da yawa mata ayanzu suna halaka kansu ta wanan hanyar bayan sun sani suke taka sanin. Annabi yace dana miji yai tafiya ya dawo gida bai sami matarsa a gida ba gara akawo mashi gawanta ko nasa zaifi sauki haka kuma duk macen data tafi wani wurin bada umurtan mijinta ba duk rakon da takeyi mala,iku suna tsine mata. Ina kikaga ina fita ba tare da sanin mahaifin ku ba maza ki mike ki koma dakinki idan ya dawo sai ki nemi izininsa kizo tafi min da inga zaki dauki hanyan halaka. Ko kuma so kike ki koma irin yan uwanki da kullun suna gidan nan tun safe har dare ba a ma gane cewa aure sukeyi a yanzu ko hakan ke baki sha,awa kema ? Na mike daga inda nake ina fadin ummah tunda yau nazo a bari naga su datti don Allah kan natafi dacewan kannena tace oh na kyaleki ki ci gaba da halaka ke nan ko ? Haka na mike jkki a sabule ba don naso ba na fara shirin tafiya gida naji tace ko akwai wani abinda kikesone da sauri na dago kai nace a,a banson komai ummah kawai nazo nagaida kune dama. Daga nan ki koma gida kada inji kinsake irin hakan idan ba haka ba ranki zai baci dani bandai yi magana ba na figi hijjab dina na saka a kaina na dago nace sai anja idan sun dawo a gaida min su. Zasuji ranan asabar da safe zansa shehu ya kawo makisu wuni ina shike nan ko nace nagode ummah har nakai kofa lokacin ita kuma ta dago daga inda take zaune na juyo ina fadin . Mahaifin shi yazo shekaran jiya shida yan uwanshi saidai basu samu Ahmed din a gida ba shine suka tafi amma idan ya dawo zai dawo yace. Ikon Allah dama bai kasan ne ko kuwa ta tambayeni nace ummah bai fasan mahaifin nasa ba ko sau daya shima haka bai san dan nasa ba har yanzu. Me ta fada da karfi cikin mamaki nace gashi kuma yazo bai gari amma yace zai dawo ikon Allah wanan abin da mamaki yake jeki dai wata rana idan kinzo makarasa hiran ki gaida tsohuwar nan don Allah. Na kara mata sai anjima nasa kai mm a fice raina a bace don yadda ummah din tayi min taki in zauna a gida ni kuma naso indan zauna sai dare so kkmawa gidan amma taki hakan gareni. Haka na juyo na dawo sukuku na bude part dina na shiga ba wanda yasan a lokacin na dawo gidan cup mm a fito waje da niyar na dauraye naji muryan inna da wata mace suna magana daidai kofan shigowa part din nawa suna fadin. Ita wanan wani irin unguwane haka tun shigowa na gidan nan har yanzun bata dawo ba sai naji inna tace ke dai bari kawai inno ai ina ganjn abu gun yarinyar nan. Da ace ita din wata me gatace ko a gidansu da bansan yadda zamu kwashe da ita ba ai saukin abjn ko a cikin gidan nasu uwarta borace bata da power. Wai fa makaranta ta tafi tun safe har yanzun bata dawo ba kamar kantane aka fara boko abin dan yaune kawai da shirme ni ina namiji me zai kaini kwaso wanan na aje a gidana. Abu haka da fari kamar zabaya babu dadin gani ko kadan wallahi tunda na farga irin diyan masu kudin nan ne marasa kunya na daure mata mara tam a gidan nan ko kadan bata ganin fuskana a gidan nan . Daba haka ba sai yace mu muyi mata girki ita tana kwance haba dai keko Rashida ina hakan zai yuyu wallahi ko ina fada maki idan kinga abinda yaron nan yakeyi wallahi sai kin raina masa. Keko dai rashida kika sani ko ubanta yana bashine gakufa yanzu baku cikin wahala duk garin nan abinda ake fada ke nan cewa mahaifinta yana taimaka maku yanzu. Da sauri naji inna tace Allah ko zai saka muna ko kwandalan su bamu taba ci ba a gidan nan ke na fada maki diyar borace fa a gidansu din mena gaba yaci balle na baya. Shine dai son a sani yake faman kashe kanshi a kanta ko kwanaki datayi ciwo bakiga rawan kan daya dinga yi ba sai kice yar gwal ya dauko muna. Ni wallahi dana san yadda zanyi inga na rabashi da ita wallahi da nayi na aura mashi zabina kina da wata zabin ne akanshi matar ta tambayeta tace ga diyar kanwata nan tana mutuwan son shi kamar ta mutu. Amma umma ta hana a tayar da zancen wai kada taji ko ta gani zamu batawa yaro tsarinshi a,a a kinfa san dama mutumin Dijene shi sosai . Ai nasan maganin su jira nake ya gama wanan karatun daya saka kanshi sanan na bulo mashi da zancen don inga ko wace mace ce suke zagina da ita sai kawai na turo kofan part dina na fito. Da sauri suka juyo suga ko waye sai suka ganni nace sannu ku ina wuni cikin iiiniya inna ke fadin dama kin dawone ashe nace eh na shiga sashen su na barsu a wurin ban dade da shiga ba naga inna ta shigo nasan dayan matar ta gudune lokacin.