← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 264 OF 286

Sashe 264

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sun dan darata da tsowo saidai basukai Abba din ba da alama uwarsuce gajera suja kwaso yanayinta a nan saidai akwai fari kan sosai gaskiya. Duk da nima farace mijinama farine sol amma hakan bai hanani ganin farinsu ba yayin da ita kuma hjy murja farace ba dai sol haka ba ita da nata yan matan yanayinsu daban ne a gidan hakan zaisa ka gane ba uwa daya bace ta haifesu ba a gidan don yanayin daya bambamta garesu. A cikin harshen turanci Yasir din ke magana yana fadawa dan uwansa ai mum bata nan sun samu matsala da daddy tana wani gida zaune ne yanzu ita . Jin hakan yasa master ya kalli mahaifin nasu ya dukar da kai kasa tare da fadin please Abba kayi hakkuri ku zauna lafiya da matar ka kada ya zamo dukkan mu bamu da uwaye a tare dakai su yarana kuma sun taso tare da uwarsu dakai a gidan nan sun bude ido da hakan . Yanzu zaman su ba tare da itaba zai iya jefa rayuwansu a cikin wani yanayi kun girma kunsan kanku mune zamu kwatanta hakan kuyi muna fada komai tayi ma taci albarkacin diyanta a gareka ai. Hannu ya dagawa dan nasa alaman ya dakatar da zancenshi a lokacin hakan yasa yaja bakinshi yayi shiru kowa a falon yayi shiru na dan lokaci kafin can ita macen ta mike tana jan tsuki ta nufi hanyar shiga part dinsu a cikin takaici. Muryan Dijece take fadin hakkuri akeyi da iyali yadda kuka kai din nan bai kamata ace wani abu mai muni haka ya fito a tsakanin ku ba ai ayi hakkuri ta dawo dakinta dai. Nagode mama ya fada ya mike don zuwa wurin cin abincin da aka tanada suna aje yake fadi da yaren fulatanci a kaiwa Dije nata a can part din mu. Yan matan nan suka mike suna kwasan wasu kuloli suka nufi can dasu master ya kalli dije yace ku koma can kuci abincin ina tafe idan na gama ni da yaran jin hakan yasa na riga kowa mikewa na fara tafiya dijema ta biyo bayana nasan magana zasuyi a tsakaninsu lokacin. Amma mahaifin nasa bai basa daman yin wani magana ba a lokacin don ya hana zancen gareshi nikan ba wai komai nake ci ba layin ummah na kira ta dauki waya nake fada mata bayan mun gaisa ai muna shigi jiya da dare. Tace tun shekaran jiya da dare nake kiran layin ku baya shiga in fada maku cewa jikin Alh ya kiya yanzu ma haka muna asibiti a nan cikin gusau dashi. Jin hakan yasa na mike zaune daga kwancen da nake ina salati a daidai lokacin ya shigo yana tambayan meke faruwa wayan na basa suka gaisa tayi mai sannu da zuwa. Nan take masa bayanin halin da Abba din ke ciki amma irin karfin halin hausawa sai cewa tayi ai yaji sauki ba kamar yadda suka kawoshi asibitin ba yake yanzu ai. Ok da sai jibi zamu shigo amma insha Allahu gobe idan Allah ya kaimu zamu shigo gusau din ummah a gaida muna shi don Allah dije ma tana gaidaku sai mun iso. Ya aje wayan ya kalloni inda nake kuka yana fadin meye haka kuma kamar baki da tauhidi a zuciyar ki makin ki bisa da addua zaki zauna kina masa kuka haka ? Master ba dole nayi kuka ba Abbane fa yaushe rabon dana gansa saidai a waya bana manta son da Abba ya nuna min a baya yanzu lokacine da zan dubashi nima yasan ya haifeni amma kuma ciwo yana son rabamu a yanzu dashi. Haba dai matar Amadi kibar wanan maganan haka shi ciwo ba mutuwa bane manzone na ibada ga bawa mune bamu gane hakan insha Allahu zai samu lafiya. Yanzun kikaji Abban ku yayi magana a falo yake fadin idan gida baiyi a kaishi waje da yardan Allah zai samu lafiya . Yanzu ba masu maganin gargajiyane a kasan da ace daurine da ko a na gargijiya an samu maganin matsalan a saukake ba kamar yanzu ba da aka baci da asibiti komai ace asibiti. Kinga mijin ki gashi da kinsan wani ciwo da ya taba yi a baya ba zaki fadi hakan ba lokacin daga kuraje ya fara har ya kaishi kwance yana yaro. Duk kauyu kan nan na gusau daya dayane ban taka dashi ba a lokacin don mu samu magani amma abu yaci tura ga mahaifansu bako mutum daya a kusa don a shekaran ne uwarsa ta koma can cikin naija da zama. Sai fa da Allah ya kawo min wani bawan Allah irin mutanen nan masu sayar da magani suna yawo tsoho dogo haka dashi da dan buhunshi da sanda yana dogarawa a wurinshi ne na sama mashi magani don kamar sihiri ina amfani dashi ya warke sumul. Tun lokacin kuma ya zamo mai mu,amula da tumfafiya don shine ganyen danayi ta dafa mai a lokacin har nake tunanen ko yana zaton tumfafiyan maganin komai yakeyi da yake yawan debo minshi a daki kamar yadda na baki labarinshi a baya dai da ganyen tumfafiyan. Wani kallo gaba dayan mu muke mata yada ta daina magana da takeyi din tana kallon mu itama a cikin mamakin kallon da muke mata din tace wallahi tun wanan lokacin nayi neman mutumin na kara amsan wani sani a wurin shi tunda ba mai zama bane ban kara ganin shi ba . Lokacin tun fa Amadi yana yaro wanan hiran da nake maku a ina zangansa yanzu kuma ta fada a sanyaye cikin bata rai a karshe kai maza sun kwanta dama tare da sanin su wallahi yanzu sai makaryata da yan sheri aka barmu dasu. Dije wanan mutumin yana yawo da irin buhun nan na dacan goye a bayasa tare da dogara sanda yana tafiya a duduke har ya rankwafa ko ? Ke ina kika sansa Master din ya katseni da wanan tambayan ita kuma dijen tana fadin kwarai kuwa Allah ya barki haka yake dogo dashi nace da saje farin gemu a fuskanshi ko ? Tace Allah dai ya barki yar nan haka yake yadda kika kwatantashi din nan sosai wallahi shine har inkinsan shi to shi din daine toni ko yau na gansa a cikin mafalkina haduwan mu kuma na farko dashi a hanyar makarantane da safe na fito zan tafi school ranan muka hadu dashi na dan tsaya ina tunane kafin nace. Ina ganin that was day da muka fara haduwa ai dakai a school din a ranan na fara ganinsa sosai ranan nan ne na fada ina lumshe idanuwana. Ke kin sansa ke nan dai na bude ido ina fadin indai shine nasan sa sosai don ko yau din nan saida nayi mafalki dashi da asuba din nan. Kuma a fili kin taba ganinsa nace kwarai kuwa na fadama a wanan ranan da muka fara haduwa har ka taimaka min a ranan ne na fara ganin shi kuma a yanzu sai nake yawan mafalki dashi lokaci lokaci. Shiru yayi yana tunane can naga ya mike yana fadin zan je gidansu Nabil yayi aure muna can idan na dawo zamu shiga mu kara tsaraba a nan wanda zamu gida dashi don mutane. Na gane Nabil abokinshi yake fadi nace ya gaidasu ina mashi fatan alheri ga zamansu kiba babana maganinsa tasha in sha biyu yayi ban dawo ba.
Chapter 264 · 0% Book details