Sashe 162
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kusan lokaci daya muka mike zaune muna kallon juna wani ihun ta sake sakewa wanda yafi na farkon da sauri ya sauka saman gadon yana fadin innace fa . Yana kokarin laluban riganshi dake gefe a falo ya karasa sakawa lokacin nida ya bari a ciki tsorone ya kamani nima riga na dauka nasaka nabi bayan shi zuwa waje da sauri. Tun daga nisa na hango inna tana faman nuna wajen da hannu tare da fadin gata nan tazo min a wani halitta zata zane ni ku taimakeni tana faman nuna wajen kofansu da hannunta. Ahmed ne ya karasa wajen yana fadin ku jaye nan ya rike hannun uwar shima a kidime yake lokacin ya fara fadin inna ba kowa wurin nan fa don Allah ki natsu ki daina hakan darene yanzu. Saiga inna na sambatu tana fadin to to zan bari amma ku rokan min ita don Allah ta rabu dani tunda ban mata komai ba. Inna ba kowa fa wajen nan killa mafalki kikayi haka kike ganin kamar mutum ne a wurin wallahi ba mafalki bane itace ta tayar dani daga barci tana fadin in tashi ciwon da nayi kadan ne bai isheni ba tunda banda tausayi . Ina jin hakan a cikin tsoro don ina ganin kamar abinda take gani din muma zamu ganshine lokacin nace to inna ki bar fadi kiyi ta addua a bakinki shine makarin bawa. To naji zanyi tace dani kamar wata yarinya karama Aisha za a samu garwashin wuta yanzu gidan nan Ahmed din ya fada yana kallon kanwar tashi. A,a yaya yau bamu hasa wuta ba a nan na karba da fadin saidai a jona Bonner idan zaiyi tunda akwai wuta yace a dauko a gwada mu gani. Saidai na kaaa motsawa zuwa dauko abin a dakina sai can ya juyo yana fadin ina abin baki dauko ba nace wa zai rakani part din mu din kuje da Aisha mana idan kina jin tsorone. Tare muka tafi na dauko mashi muka jona a dakin sai ya zagaya baya zuwa can ya dawo dauke da bawan tumfafiya a hannunshi irin wanda ke bushewa a jikin iccen ya dan barbasa a cikin abin. Dakin ya dauki hayakin maganin daya turara mata din lokaci guda Asmau banda kuka ita da Aisha babu abinda takeyi lokacina. Ita kuma inna din sai wuri wuri takeyi da idanuwanta kamar me ganin wani abin tsoro a lokacin gabanta ya rike mata kai yana addua . Muna tsaye cirko cirko muna kallonsu zuwa can mukaji kamar motsin tafiya a wajen gidan muka kalli juna da Aisha kowa na signal da idanu a tsorace . Ya kara mika hannu ya kara zuba hayakin a wuta kowa dake dakin yaji tsoki kamar a fusace an nufi baya inda dabbobin gidan suke hanyar makewayin su. Sai ga inna din ta mike shambal a jikin dan nata sai kuma wani barci mai nauyi ya dauketa lokaci guda haka bai hanashi karanto mata adduan da yake karanta mata ba lokacin. Ku dan kama min ita mu kaita a shimfidanta ya fada nida Aisha muka kama kafafuwanta zuwa saman katifan da take kwana a sama. Aka kwantar da ita saman katifan tana barci sai lokacin muka dan zauna gefen katifan su Aisha din muna mai kurawa inna din dake kwance idanu. Ganin ta samu barci sosai a lokacin yasashi dago kai ya nisa yana fadin fadin Djje ina ganin inna gamo tayi tunda har maganin nan yai mata amfani yanzu don bayan iccen tumfafiya na debo na turara mata. A dan firgice Dije din tace dashi gamo kuma na dauka zafin ciwon ne haka yace bashi bane saidai idan dama haraswan da gudawan nada nasaba da hakan ne. Kowa dakin yayi shiru karfe uku saura yacewa kowa ya kwanta tunda ta samu barci abari aga abinda Allah zaiyi zuwa safen kuma. Mu zamu kwana da ita ke nan Aisha tayi saurin tambayan yayan nata a dan rude lokaci guda tana kallonshi. Kai ya girgiza cikon takaici yace to menene tunda abin ya lafa a yanzu yana da wuya ta tashi ai kuma ciki wanan daren. Saidai mu kwana da Dije hakan zai danfi muna sauki da a barmu da ita a nan haka yace dama aida Dije din zaku kwana a nan dakin. Ba zance tunda muka dawo dakin ba ya kara runtsawa har zuwa safe don ko masallaci da yatafi ban tsanmani ya tsaya yin addu,a ba ya dawo gida ranan kai tsaye part din su ya nufa yana duba mahaifiyan nasa wace a dan lokaci guda kamaninta gaba daya ya sauya a yanzu. Abin duniya baya boyowa kafin ace haka labarin ciwon inna ya karade gari musanman unguwar namu nan mutane suka fara shige da fice a gidan namu wurin gaida ita tare da ba idonsu abinci su samu na karaswa gaba wurin bada labari. Sai da Ahmed ya fahinci hakan ya dauketa a dakin nasu ya dawo da ita part din mu koda mutane sun shigo sai ace dasu ai sun tafi wurin magani bata nan don abin ya zama mata kamar tabin hankali. Don saita fara kokarin cewa zata bada labarin yadda matar tazo mata tace ke dai bari kawai ina kwanche sai ji nayi an tayar dani ina bude ido naga wata bakar mace da tunda nake duniya ban taba ganin mutum mai bakinta ba sai ranan. Kaiwai tace min tunda baki da tausayi da jin kai zanyi maganin ki gobe baki kara ganin wani rayuwa na ciwo kiki tausaya masa kinyi karshen yin hakan a kaina. Jin irin maganganun mahaifiyar nasa da in yana kusa sai ya kwaba mata yasashi shiga wani hali don bashi kadai ba koni dake tare dasu yanzu hannu a gaba yake da ita. Ganin ba shiri ko banza a tsakanin mu yasa nake kara kama kaina da ita yanzu don sai inga kamar tana hararata idan na gilma a inda take zaune. A rana na biyu da faruwan hakan na dauki waya da safe na kira ummah ina fada mata abinda ke faruwa a gidan namu ta tausayawa inna sosai har tayi min fadan ban fada mata da wuri ba ai ba a haka. Sam bansa zatazo gidan ba don ta kira Ahmed din tayi mai jajen abindake faruwa tare da fatan samun lafiya gareta. Washe gari sai gasu a gidan namu shine karon farko da har ummah din tazo gidan namu tunda nayi aure a gidan sai wanan zuwan. Duk yadda ake bata labarin talaucin gidan sam ummah bata ga hakan ba indai muna zaune lafiya hakan ba komai bane a wurinta don ko yawan maganan da mama kan sake mata a gida sharewa takeyi bata amsa mata. Don su ko yaushe suna gida tare da mama su kwasa zuwa unguwa ko wani wajen ba zakace sunyi aure ba a lokacin. Mama kance rashin jin dadi ko rashin samun waje da walwala yasa ban fitowa nima aiko yaushe din don ina kunyar agani lokacin. Ga Aisha da tsohon ciki a jikinta haihuwa ko yau ko gobe itama Rukaiya din nada ciki saidai baikai na Aisha din tsufa ba. Kamar a mafalki naji sallaman su ummah din duk da naje gida sau biyu da aurena amma hakan bai hanani bin jikin ummah ba ina murnan ganin su. Haba ki natsu mana mahmah gaida mara lafiya mukazo fa ummah ta fada min da dan rada sai jin hakan yasana natsu na kaisu direct dakin da inna din take ciki. Ina shiga bata farga da baki a bayana ba tace yarinyar nan bansan me kika daukeni ba tun dazun nake jiran abinci shiriritan ki yasa baki gama ba da uwarkice a wanan halin aiba zaki barta da yunwa ba. Sallaman su ummahne ya katseta ta fara binsu da idanu tana kallon su har suka karaso cikin dakin suna gaida ita lokacin ne Aisha tace Lah ummah kune tafe ashe inna ga mahaifiyar matar yayan mu nan tazo gaidake. Sannuku da zuwa ashe kuma kun samu labarin abinda ya sameni din kunzo kedai bari ina tsaka da barcina saiga matar nan ta shigo min ta tayar dani wai kasheni zatayi. Koda yake sunce wai nabar fadi kingansu nan wai mutane zasu dauka na tabune a hakan don na fadi gaskiya. Tana fara fadin hakan Aisha ta mike ta fita nima nabi bayanta muka barta dasu tana basu labari kamar yadda takeyi idan wani ya shigo gaida ita din. Hawaye na samu Aisha nayi tana fadin yanzu matar yaya wanan abinda inna keyi haka za a saka ido abu sai gaba takeyi kafin na bata amsa Ahmed ya shigo fuskan shi a kan mu yana fadin . Ummah ce tazo da kanta ashe kin fada matane yana don jiyama ta kirani tana min ya mai jikin ya fada yana kallona . Nace eh jiya na fada masu inna ba lafiya kada taji daga baya taimin fadan hakan yace hakane yana kokarin wucewa zuwa dakin . Gatacan ta fara zuba masu ai Aisha ta fada a dan kuntace sai ya nufi dakin da sauri yana sallama nan ya samesu suka fara gaisawa bayan sun gama gaisuwanne ummah tace wanan abin sai kun dage da addua sosai a kanshi don kamar bana asibiti bane kawai ? Eh ummah yanzuma daga can nake na amso rubutu da za a bata tasha da hayaki don sunce ba shiganta sukayi ba sun dai shafatane kawai don ta tabasu suma sukace. Ai abin ke nan tunda muba ganin su mukeyi ba sai sunyi hakkuri rashin sanine ya kawo hakan Tani mai aikin ummah ta fada tana kallon inna din dake wuri wuri da idanu tana sauraren su. Kafin tace in na sani aiba zan tabasu ba ko in takasu har wanan bakar macen na barazan daukan raina lokaci guda haka. Basu jima ba suka fito na zata zasuje dakine sai naga ba haka ba don suna fitowa suka fara muna sallama muka rakasu har kofa suka tafi don haka bamu samu maganan komai ba da ita a lokacin. A wurin Aisha yaji abinda ya faru shigan mu dakin itin fadan da inna ke min a lokacin gaban mahaifiyata sai ranshi ya baci da hakan har yake fadawa Dije abinda ya kawowa inna din ciwon ta lokacin. Yace irin wanan halin ne yajawa inna matsala