Sashe 181
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
kafin yace gwaggonane daga Gembo daga mambila suke ita da mummy ku na can. Wani irin faduwan gabane ya ziyarci zuciyar hjy yabi lokacin har jiri na neman dibanta zuwa kasa sai da Allah ya gyara bata kai kasan ba a lokacin wa yan nan fararen yaran fulanin suka shigo daga waje suna jan akwatinan su zuwa ciki. Mamakine karara a fuskan hjy yabi saliman ta kara tambayan uban da cewa so she now live in Abuja with us ? Yace of course a nan zata zauna tare damu itama da yaranta ok she is welcome ta juya zuwa cikin ya bita da kallo kafin uwar dake tsaye kamar gunki tabi bayanta a fusace itama irin ga mace ta hasala da miji a lokacin. Bai tsaya binta kanta ba ya juya wurin tsohuwar nan suka shiga ciki suna magana dashi. Mataimakinta ta jawo watau waya ta dannawa yarta kira a cikin tashin hankali akai sa a kira biyu ta dauka tana fadjn yanzu naso kiranki dama sai gashi kin kira. Naji gari ya dauka cewa kishiyar ki ta koma Abuja da zama jiya suka bar garin nan tace shina kira in fada maki yanzu. Yanzu na gane inda barnan ya fito min yanzu na gano me min bandar kasa ashe nayi sake ina daukanta sakarai tana min kallon wawiya. Tunda har yau Alh ya iya dawo da ita garin nan kusa damu mu zauna tare a nan da ita yanzu wasan zai fara a tsakanin mu dama ashe itace ke min saran boye ban farga da hakan ba ? Yanzu shi meya fada maki yau din nan ya dawo da safe ko ganinsa banyi ba sai yanzun nan na ganshi a falo suna magana da salima yake fada mata a nan zasu zauna damu wai. To kinji ki natsu don Allah kada ki yarda harta gane cewa akwai matsala a tsakanin ku yanzu ki bita da basaja ke inama ruwanki da itane wai kowa yayi harkansa kawai zaifi don ba wani shiri tsakanin ka da kishiya kowa naciki na cikine a tsakani. Ke ni Alh ma ya ban mamaki wai yau shine harda daukan Murja ya tafi da ita Abuja yarinyar da abaya yake fadin baisan yadda zai kwanta da itabama. Ohh ke kika saura rakiyan maza ki barshi kawai yanzu nuna masa ba komai a ranki ko zamu samu ta hakan mu koma daidai dashi inyaso daga baya sai mu san abinyi. Anya kuwa zan iya yau nice na bude ido tare da wata mace a cikin gidan nan da sunan zamu zauna tare wai ? Yanzu dai dole kibi sannu kamar yadda na fada maki in yaso daga baya sai muyi tunanen abinyi nan gaba muna can munata zaton ko iyayyen yaron nan nasane ke asiri ashe ga inda barna yake bamu sani ba. Haka dai sukaita kulla tsiya a tsakaninsu har dai suka gaji suka kashe wayan suna sallama da juna akan sai ta kirata fada mata halinda ake ciki a gidan. Da sallama a bakina na shiga gidan a waje duk na samesu Dije tana alwala su kuma suna zazaune nayi sallama tare da gaidasu daga can ban karaso ba. Yar nan ina kika shiga haka har dare hankalin mu duk ya tashi baki dawo lokacin da kika sababa jin hakan yasa na dan dawo baya ina fadi. Ayyah Dije wallahi naje gidan mu daga makaranta wanan yarinyar da akai suna jiyace Allah ya karbi abinsa ba dijeba kawai gaba dayansu har inna suka saka salati lokaci guda. Inna dince ke fadin dama bata da lafiyane sai dije ke fadin gashi tana fadan ankaita asibiti ba wanda yasa rancewa ma zai ai sunan ga jiya amma uwartace ayi kawai. Eh to uwar nada gaskiya aiko banza taiwa uwarta bara kinga da batayi dabaran hakaba da shike nan ai bata samu gudun mawar data samu a jiyan ba. Nikan ina jin ta fara babatun ta na juya kawai zuwa kofana nasa key na bude na shiga duhu ya fara don haka na tsaya na lalubo wayata nayi amfani da haskenta na kunna wuta. Na saka ki na bude kofan na shiga don ko,ina ina rufewa idan zan fita don da farko ban rufe part din amma yanzu dana fahinci ana min barna na fara rufewa idan zan fita din inna tayi korafin hakan ta gaji ta barni. Jakata na wurga saman kujera na shiga uwar daka har na nufi bayi na tuna da kudin da Abba ya bani na fito na dauka nakai cikin wardrobe dina na boye. Ruwa na watsa a jikina na dauro alwala na fito na tayar da sallah bandaga ba har akai isha na gabatar san na na mike na jawo rigata na dora sama. Zan juya naga jakar na sake tunawa da kudin na dauko na zauna na kirga dubu darine cif a ciki wanan ne kyauta na farko da Abba yai min tun bayan aurena da Ahmed din. Nayi mamakin hakan don a gaba yayi warning din kowa akan kada ya bani kudinshi sai gashi yau shiya bani kudin nasa da kanshi. Dubu ashirin na zare daga ciki don na bawa mutanen gida suma su taba su lakaci arziki kamar yadda na samu nima don haka na debewa kowa biyar biyar na mike na fito da kudin a hannuna zuwa part dinsu. Yadda na barsu a zazaune haka na dawo na samesu sai Dijece ke cikin dakinta lokacin nace to Dije sallah akeyine har yanzu shin naji tace na sallame dama yanzu nake shirin fitowa zuwa wurin ki in maki gaisuwa. Kai ji dije mutuwar yarinyace sai kin wani binta kuma kin mata gaisuwa akanshi yarinya ai rayuwa gareta kuma jinintace ko ta fada tana fitowa daga dakin tana cin karo da kwanon da suka aje mata a kofa. Kai masu wutan nan Allah ya shirya muna su ace tun jiya ba wuta mutane na zaune cikjn duhu da zafi haka yanzu dana kara dan dayan kafar mai dan lafiyan. Da za a samu wani ya sayo muna mai da sai mu kara a tayar da injin din nan ko chajin waya mu samu da sauri Asmau tace indai akwai kudin kawo yanzun nan zanje gangare nasayo maki. Nace to bari inzo a lokacin ne na mikawa Dije dubu biyar saina nufi wurin inna mai fadin kullun suna yar mai kudi a gidansu amma har yau ko kwandala basu taba ciba naji hakan ne a makwabtan mu rana dana shiga gaidasu tun ranan ban koma shiga ba kuma master ya hana. Na mika mata ina fadin inna gashi jin gashi yasa ta juyo da sauri tana kallon hannun nawa ta karba Dije ko tana can sai zuba mjn addua takeyi na nufi inda Aisha suke suma na mkka masu nasu . San nan na dago nace Abban mune ya bani kudi dazun shine na basu ai nan suka shiga godiya inda yaran ke ihun murnan samun kudin. Na juya na dauko kudi dubu daya naba asmau ta sayo muna mai mu kunna injin din muga haske ta fita tana godiya bayan ta dawone muka fito da injin din muka zuba mai nika ba karfi amma haka na gwada don sun gwada sun kasa tayarwa dole muka kira wabi yaro yazo ya kunna muna gidan ya gauraye da haske lokaci guda.