← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 286

Sashe 22

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

lokacin ta juyo gareni tana fadin. Eh zan fitane har kun dawo tana kokatin shiga mota na bita da kallon mamaki daga hakan bata kara juyowa inda nake tsaye ba din sukaja mota suka tafi. Ajiyan zuciya na sauke tare da juyawa zuwa cikin gidan namu zuciyana da tunanen wanan sauyin da nake gani a gun mama din yanzu. Da sallama a bakina na shiga part din mu saidai babu kowa a falon mu lokacin haka yasa na wuce zuwa bedroom dina na fara kwabe kayan jikina. Sauyawa nayi zuwa wani dogon riga kafin na sake fitowa zuwa dakin ummah don na gaida ita kuma tasan na dawo a lokacin ban son ta shigo ta same ni a dakina. Zan shiga dakin ke nan naji motsinta a falo na juya zuwa falon na sameta a nan ummah na kira sunan ta tajuyo tana fadin ashe kin dawo ke nan to yaya kan naki bai tashi ba acan yau ko ? A, a ummah saidai nan gefe daya danaji ya daure min kamar zai fara min ciwo din lokacin saina shaka wanan maganin na jiya a masalaci naji ya bari . Kikuma dinga yin addua kina tofawa ai haka wanan yace min yau da muka hadu dashi a school yau din ma kun hadu ke nan dashi ummah ta tambayeni ? Eh yazo wurin motana yana duba da mamakin har naji sauki nafito yau makaranta shine yake fadin na kula da jikina da kuma addua don ni mace ce daba don Allah ya kawoshi jiya ba baisan yadda zamuyi ba a wurin. Gaskiya ya fada addua ya dace bawa ya tsare a kullun don ita kariyace ga mumuni don haka ki kara tsare addua sosai ya fada maki gaskiyan da nima iya nan zan iya fada maki ai. Ummah wai meya samu mamane naga zata fita ranta a bace ina gaida ita bata tsaya ta amsa min ba tana dauke kai gareni kamar nayi mata wani laifi. Yanzun nan zata fita da yamman nan haka ban jin nisa zata tafi don bata faye fita haka da yamma ba saidai in wani wuri mai muhinmancin zata tafi hakan yanzu a wanan lokacin. Amma ai mama bata daure min fuska haka irin yadda tamin yau din nan idan ta dawo anjima zan sameta a part din ta ai na gani.. Kice mata me idan kinje ki barta kawai idan wanan zaikaiki wurinta saidai idan wani abin zai kaiki gunta ban hana ba amma kada ki mata zancen hakan koda wasa. Kaina gyada mata alaman amsawa kafin na gyara zama ina tunanen abinda ummah ta fada daga haka mikewa tayi zuwa dakin ta a lokacin kannena suka shigo sun dawo daga islamiya. Nan nake tar dasu har akai kiran magariba muka watse zuwa sallah ban fito ba sai bayan salllah isha,i da muka fito na samu ummah na waya da Abban mu lokacin naji tana fadin da sauki sosai don yau din ma har taje schoon din ai kuma ba abinda ya faru. Banji meyace ba tadai miko min wayan na karba a hannunta muryan Abbane ke kiran sunana na karba mashi yake tambayana ya jiki ya karatu na amsa da naji sauki. Muka dan taba hira yace in ba ummah din waya a lokacin na mike zuwa part din mama da naji dawowanta ana bude mata get ina sallah isha,i a lokacin. Dukkan su basuyi zaton shigowa na part din ba a wanan lokacin sai ganina kwatsam da sukayi na shigo hakan yasa da sauri naga Aisha tana kokarin boye wani jarka karami dake dauke da wani ruwan rubutu a bayan . Nayi kamar banga haka ba lokacin wurin mama na nufa a sake ina fadjn mama ashe kin dawa andawo lafiya ya gajiya ta amsa a cikin dan darare da fadin lafiya tana kawar da kai gareni. Nan ta barni zaune tankar ba mama ba a ranan yadda ta nuna min din tankar bata san dani ba zaune a wurin ta kama harkan gabanta ta fita batuna ga baki daya. Saida na gaji da zama na mike nake fadin mama zan tafi dama na shigo na gaida kene don dazun bamu gaisa sosai ba zaki fita. Ta dan juyo gareni tana fadin OK zaki tafi zarah saida safe ke nan wani irin ba dadi naji a rain haka naja kafana na fice daga part din mama ba tare da kowa ya kulani ba lokacin. Ina shiga part din duk suna falon a lokacin ummah tana basu wani abu da bansan ko meye ba na daiga yaran na bata fuskansu alama abin da ake basu baida dadi ke nan a baki. Kokarin shiga dakina nakeyi a lokacin naji muryan ummah tana fadin maamah oya zo nan ki karbi naki kisha . Fuska na bata daga inda nake tsaye din ina fadin ummah bana sha a koshe nake na juya zanci gaba da tafiya wanan din ba wani abu bane maganine na ciwon zazzabi kawai. Ummah oya zoki karba ban son korafi Anty zarah sai kinsha dole ummah tace don maganin ba dadi kuma kanina ya fadi daga gefen ummah inda yake zaune. Dole nazo na zauna a gaban ummah ta debo maganin a wani silver ta miko min tare da fadin oya yi bissimillah kisha. Karba nayi ina bissimillah nakai bakina ba dadi abin amma haka na daure nasha maganin kafin ummah ta umurce ni da naci abinci. Na tsakwara na tashi zuwa lokacin duk jikina ya mutu tashi nayi zuwa dakina ummah ta dubeni tana fadin saida kika je gun maman taku din ke nan ko ? Kallon ummah nayi a dan shagwabe kafin na gyada kai alaman naje amma ban yi zancen komai da ita ba ai itama din kuma ko kulani batayi har yaranta
Chapter 22 · 0% Book details