← Book details Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 286

Sashe 130

Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa na mamakin ji ance ai bukin da nine alhalin sunsan ban tsayar da mijin aure ba lokacin asalima ina karatune a yanzu duk da suma sunata spell a karatun su har lokacin ba wace ta rike kwalin shedan karatunta. Wayana gaba daya na kashe ban daukan kiran kowa haka ko falon mu bana fita balle zuwa makaranta ganin haka yasa ummah ta sameni a daki tana min fadan rashin fitana zuwa makaranta. Inda tace dani kaina zan kullawa sheri don shi Abba baisan ina yiba ma don haka gara in natsu insan abinda nakeyi zaifi. Wanan fadan da ummah tayi min yasa na shirya washe gari na fita zuwa school nasha tambaya saidai ganin yadda na rame lokaci guda yasa suka dauka banda lafiyane. Sunan nazo school daine amma ban fahinci komai da akeyi ranan ba don hankalina daya tafi wurin tunane lokacin ba abinda nake tunawa sai irin matsalolin da rayuwana zai fuskanta a irin gidan da ban saba rayuwa a cikin shi ba tun tasowana. Nakanyi hawayen da bazan fadi dalilin fitashi ba lokaci guda gashi zance ya gama karade dangi cewa wani dan talakkawa mara asali da baida galihu nace ina so. Su kuma Aisha da Rukkaiya sai faman rawan kai da sukeyi suna ta zirga zirgan ganin bukin su ya kawatu kamar bukin ko wace yar gata. Inda a bangaren ummah banga wani shirin da takeyi ba ita ko don zancen yazo mata girshine ko kuma irin nata fushin ke nan oho. Don har an fara gulman ba aga tana wani shiri ba akan aurar dani din kamar ba yarta na fari zata aurar ba wanan gulman kuma ya fara fitowane daga bangaren mama har dangin mu suka dauka suna yadawa. Na dawo school a gajiye rana ina shiga gida wayana na ringing ban daga ba sai kusan karshe na daga ina kallon lamban dake kirana din layin kamar na kasan wajene na gani. Dauka nayi ba tare da magana ba nake sauraren shi naji ana gaisuwa cikin muryan turawa tare da tambayan nice Zahra na amsa da eh naji yace ko zan iya tuna mutumin da muka taimaka a baya wanda muka tsunci walet din shi muka kirashi ? Har shima ya kira yana rokon mu nace na tuna yace shine ai yanzu yana Canada ya koma kasan su ya zama C E O na wani company nasu a dalilin wanan number da muka taimaka mashi dashi. Don hakane yake gaiyatar mu zuwa kasan Canada wurin shi don ya gana damu yana son yai muna wani abu muma a rayuwan mu. Jin abinda ya fada nasan abune mai wuya hakan ya kasance yasa na dan sake murmushi ina fadin nayi mai murna sosai da jin hakan. Amma zancen zuwa Canada a yanzu gaskiya bamu da karfin hakan don muna nan tallakawa lis kuma a yanzu ma few weeks ya rage muyi aure. Dan fito naji yayi yana tafi tare da fadin yayi muna murnan hakan da yana da dama da zai shigo Nigeria don mu yazo bukin mu. Yanzu shike nan zai bari sai bayan bukin zai shirya muna shigowa canada din amma mu turo account zai turo muna da gift din bukin shi nayi mai godiya muka yi sallama na kashe waya tare da mamakin hali irin nasu. Kamar da wasa na tura account dina dana Ahmed na juya na bar wayan a gefena karshe na gama abinda nakeyi na fito falo nan na samu ummah a zaune tare da Tani mai aikin mu suna zaune suna magana. Na gaishe na mike zuwa dining din mu don inci abinci naji muryan ummah na fadin ke zo nan na juyo da sauri don nasan ni ummah ke kira da hakan wani lokaci. Daki nawa yaron nan yace dake ya tanada don muna son sanin komai kada ai min girshi da yawa sai nace Tani din tace walle hakana na hjy gara dai din a tambaya shiyahi. Ummah bamuyi wanan zance dashi ba na bata ansa tare da noke kaina a kasa naji Tani ta sake fadan Allah sarki uwar dakina Allah dai ya shige muna gaba keji. Wadda aka son gani gareku Ubangiji Allah Allah ya shi maisuwaar da wanga aure alheri a gareki kada Allah ya nunawa makiyan ki ke wullakanta kada Allah ya nunawa makiyan ki kasawan ki a dakin mijin ki keji. Amin naji ummah tana fadi itako taci gaba da fadin ki zaman ki kiba marada kumya ki zauna lahiya da mijin ki keji mama. Wanga abu anyishina don aga karshen ku mai ganin haka ga bawa sai Allah komai mukadarine kejiya shima zan ganai inja mai kunne keji. Nidai abinci na diba na dauka na nufi dakina a saisai lokacin da zan shigane naji sakon massage na shigowa a wayana ban duba ba sai kokarin zama nayi don in fara cin abinci naji wayana ya dauki kara lokaci guda kuma. Tsuki naja ina dubawa ga mamaki Ahmed ne ke kirana wanan lokacin gab da magariba haka sai mamakin hakan ya kamani na mika hannu na dauki wayan. Sallaman shi naji na amsa yana fadin ya school nace lafiya kin koma gidane ko nace tun dazun na dawo sai yayi dan shiru nima shirun nayi mai yace dama tambayan ki nake son nayi don na rasa wa zan kira in fada mai abin mamakin dana gani yanzu a wayana. Gabana ne ya fadi jin abinda ya fada din lokacin yaci gaba da fadin yanzu na dawo zan shiga gida naga wani James daga canada ya turo dz kudi a account dina masu yawa duk da bansan yawan su ba da kudin Nigeria. Har ya turo maka kudin ke nan nace kinsan da zancen ke nan ya tambayeni nace eh nan na kwashe yadda mukayi dashi James din na fada mai komai shiru naji yayi na dan lokaci kafin yace dani. Dama kuna waya dashine wanan wace irin tambayane kake min bayan yanzu nayi ma bayanin yadda mukayi dashi amma ai da baki fada masa ba don kinga gashi yayi abinda bai tashi yiba garemu. Ok ka mayar mashi da kudin idan baka so sai naji yace uhumm wai zahra fushi kikeyi dani ke nan don ban taba jin kina magana da zafi irin haka ba ? Wayan na kashe gaba daya don nasan bai fadi karya ba don a yanzu laifin shi nake gani don shiga rayuwana da yayi shi yaja muna bacin rai dani da mahaifiyata. Wanan tunane zuciyana ke bani ko wani lokaci na tunda da auren da za a lakaka min a yan kwanaki masu zuwa insha Allah. Shima Abba wani irin bahagon mutum ne dake da murdaden zuciya amma akan dakin mu kadai nake hango hakan . Don abu ba abu ba kowa zaiyi yadda yake so a gidan mu amma mu dan kuskure kadan zai hau zancen ya zauna yace anyi hakan . Why mu kadaine Abba ya tsana hakane wai a gidan nan nasan da Aishace ko Rukaiyya zancen ba zaiyi zafi haka ba har ya dauki zuga irin haka. Abincin da banci ba ke nan na mike zuwa bandaki na dauro alwala nazo na tayar da sallah don lokaci yayi na sallah magariba lokacin. Na idar na nemi wuri na in kwanta sai lokacin idona yakai kan abincin dake gefe da banci ba na mike na dauka nakai kitchen muka hade da ummah . Nan ta fara min fadan rashin cin abinci kafin ta juya fadan da banci ba naki daukowa tun Tani bata wuce ba ta dauka ta tafi dashi. Ni dai banyi magana ba sai narai narai da nayi da idona ina son inyi kuka lokacin taja tsuki ta shige na kai abincin na aje nazo zan shige naji muryanta tana fadin haka zaki kwanta bakici komai ba ke nan. Shiru nayi naji kanina yazo ya rikeni ta baya yana fadin nazo nakai mai tashan cartoon suyi kallo kije ki duba akwai sauran madaran su a daki gobe na bayar a sayo wani ki hada tea kisha Na juya zuwa dakinta na duba na dauko don yanzu kiri kiri Abba ya daina saya gashi kuma tunda safe saita hada muna tea munsha kafin mu fita. Ni bansan dalilin da yasa a yanzu Abban ya daina sayo muna wasu abubuwan amfani ba kamar da can baya da yake saya muna ko zuwana abuja ga kayan tea nan nagani wanda keso yazo ya diba ya hada amma mu nan ya dai saya . Saidai ummah din ke bayar da kudi a dan sayo mata ta aje shine dalilin da yasa take ajewa a dakinta yanzu don in an aje a falo yaran sha sukeyi. Na fito naje wurin tv na kunnawa yaran naji ummah na fadin kunsan dai gobe akwai school duk wanda ya tsaya min murzan ido dukan shi zanyi. Na wuce kitchen na kunna gas na dora ruwa yayi zafi na juye na fito zuwa dakina dashi shina na danji karfin jikina nakewaya na fito nayi shirin kwanciya. Wayata na dauko don in kashe naga massage ya nuna na bude don in karanta naga sakon Ahmed ne ke ban hakuri na dauki waya muyi magana. Sai na biyun sakone daga james ya turo min da kudi a account dina nima gabana ya yanke ya fadi don ganin yawan Europe din daya turo min din. Kasa hakkuri nayi na danna kiran layin Ahmed din yana jin kirana ya dauka yana hamdala tare da fadin har na shiga damuwan kashe min waya da kikayi din. Ni ba kashe ma waya nayi ba nadai ji kana son ka zargeni don bansan abinda zan fadama ka yarda ba tunda kasan ba halina bane hakan. Ba haka nake nufi ba zahra mutum yau ba abin saurin yarda bane amma ai maganan ya wuce tunda na gamsu yanzu nace bai wuce ba kan don in zaka mayar mai ka hada da nawa don yanzun naga ya turo min kidin nima. What wallahi yanzu na daga waya naga sakon shine na duba nagani yace zanso kiranshi gashi kuma banda layin shi a wayana. Ummah tace in tambayeka daki nawane ka tanada shiru tayi kafin yace Zahra kinsan komai ba hali nake dashi ba da zanyi gina na alfarma. Daki dayane sai falo da toilet sai kitchen ta waje
Chapter 130 · 0% Book details