Sashe 269
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe takwas na safe duk mun gama shirin mu a lokacin don ina kitchen dina na sabon gidan mu tun karfe biyar da yan min tuna bayan na idar da sallah mu shiga hada abincin da zamu kai asibitin na safe. Mun kare akan lokaci mukayi wanka har yaran da yan aiki muka shirya gaba daya gidan zuwa asibiti duba jikin Abba din dake kwance a nan. Still dai su baba dasu ummah ne akansa har lokacin suna dubanshi mukai sallama muka shigo dakin ya dauki murna da ganin mu kamar ba mara lafiya ke kwance ba harshi Abba din sai daya dan dago yana kallon mu a cikin fara,a. Sama sama na gaisa da mutanen na nufi wurin gadon ina aje nasa abincin dana ruguma a wani dan carving dake gefenshi tare da fadin sannu Abba ya jikin nakai kasa idanuna cike da hawayen ganin Abban mu daya koma hakan lokaci guda don ciwo. Zakace shi dim wani tsohone tukuf a lokacin lalai mutum ba a bakin komai yake ba idan bawa ya gane yabi duniya a sannu shine alheri ga bawa mai ganewa. Yayin da su kuma suke min kallon mamakin ganin yadda na canza na zama wata mai class abin sha,awa a cikin dangi a lokacin. Master ya shigo dakin dauke da yaranshi su biyu da basu yarda da kowa idan bashi ba saiko dije dake tafe a bayan shi suna gaida mutanen daki kaina a duke saman cinyan ummah ina kuka ya kalleni yace a harshen turanci wanan ai tayarwa mutane hankali kikeyi hakan be strong kamar yadda addinin mu ya koyar damu don Allah. Kamar yadda Abban Ahmed yaso yaran suzo sukaki hakana kowa na dakin yaso daukan su sukaki zuwa gunsu dole ubansu da bai gajiya ya rike su hakana. Ya koma daidai kan Abba suna magana lokacin na dago ina sauranransu bayani yakewa Abban cewa idan likitan ya fito zu a nemi refer zuwa wani wajen either Abuja ko zuwa indiya dasu don a dibashi asan takamaimain abinda yake damun shi. Lokacin su mama suka shigo tana fadin gamu sai yanzu motan ne bamu samu ba duk motocin ba lafiya ta Alh kuma shashanga ya tafi sokoto da ita tun jiya bai dawo ba sai yanzu. Ganin bakin fuska yasa suka tsaya suna kallon mu har na juyo duk kallon su waye suke muna sai dana mike don in karbi jakkar ledan kayan Abba dake hannunta Aisha tace wai Zahrace dama saukan yaushe kuma ? Jiya muka zo na fada a cikin muryan dakushewan kuka a gareni suka bini da shu,umin kallo tun daga samana zuwa kasa sai can Rukkaiya tace wai dama zahra ce saukan yaushe amma bamu da labarin zuwan ki kasan ma nace shekaran jiya muka sauka. Muna Abuja gidan daddy jiya muka karaso nan din ina yaran ta tambaya na nuna mata su inda yake tsaye a kan Abba duk suka kai kallonsu gareshi. Saye yake cikin shadda ta maza mai tsada da take maiko shining din ta kadai zai fadawa mutum tsadanta a lokacin sai yar hulan dara baka itama mai tsada a kansa. Ya dauki Amir a hannunsa ya goya Bananh a bayansa amma cikin hakan ya nuna bai damu ba kowa da abinda ya darsu mai azuciyan shi lokacin don dole tunanensu yaje bambam a kan mu. Shigowan likitan ya sa kowa dakin natsuwa yayin da aka fara fita daga dakin a lokacin saidai banyi yunkurin hakan ba kamar da can baya da ake korani daga dakin ace anyi yawa. Mamace sai ummah damu muka rage yayin da Ahmed din yakewa likitan bayanin abinda yakeson anyi sai likitan yace ko an raina da nasa aikin ne ake gani yace wallahi a a aiyayi kokari kawai dai ana son fita dashi din ne don ya samu hutu a can . Amma idan ya kara samun sauki za ai hakan suka juya zuwa waje tare inda akarshe suka gane juna ashe sunyi karatu a secondary tare dashi dan wani mai kudine a nan zamfara aka turashi karatu kasan waje. Shima ya fara sheda Ahmed din kafin yai mai bayani ya ganeshi nan tsohon abota ya tashi sosai a tsakaninsu har sukai musayan number juna jin ai kusan aikinsu daya a yanzu. Fitansu yasa mama fadin Alh ga faten waken an dafa maka sai dai ba a samu alaihu ba yau haka nayisa tana budewa don ta nuna mai abincin. A raina nace humm,umm, ashe har yanzu barkadon na mama yana nan dai ga Abba din wai tayi hakane kada hankalin Abba din ya koma kanmu tunda daga mu sai shi da itane kawai muka rage a dakin lokacin. Amma kuma sai naji muryan Abban irin ta mai ciwo yana fadin mijin uwata ya sayo min kayan gwagwani da zanci insha ita kuma ga abinci nan ta daho min daga gidansu shi zanci yau ya fada yana kawar da fuskanshi gefe daya. Saukin abindai da namu din da ba a so yau aka samu lafiya bana ita zahran ba don ummah kada ta mayar da zancen wani abu tace fada mashi dai hjy namun dai aka saba dashi ai. Abba a zuboma abincin ne yanzu tunda likitan ya shigo yace eh mamata zuba min kadan ina budewa dan warmer din idon mama yana kai tana bi da kallo taga ko meye a cikin kulan na dafo. Tayi tozali da hadaden abincin irin hadin ganye din nan na gwangwani na salad wanda zallah diyan icce akai amfani dashi da kifi na dan zuba masa kadan. Da kaina nake bashi yana dan karba ina masa sannu a haka su Aisha suka fado dakin suka samemu wuri suka samu suka zauna ana dan hira jefi jefi har lokacin na fahinci akwai wanan akidar. Ta halin kishi kyashi da hassada irin tamu ta matan hausawa da ake samu a mafi yawan gidajen muna hausa irin gidan daya hada mace biyu zuwa uku ko hudu. Zaki samu babu komai sai zama na hassada da kyashin juna komai hadin kan gida wanan akidar kamar a jinin mu mata yake na kyashin wanda kuka hada alakan aurataiya da ita daya shafi dangantaka na auren abu daya. Saidai a wasu gidajen abin kan danyi sauki sosai in daya ta kwanta ta danne nata tanayi a boye sai ki dauka ba wani hamaiya a gidan idan kin shi dan yadda ake ganin suna al,amura a tare din. Niko yaya musa fa da yaya jafar suna wani kasa yanzun don ko a waya na daina samun su yanzun mu gaisa wanan abin yana damuna wallahi. Cabdi wai yaya musan mu kike tambaya aikuwa yanzun zaki ganshi wanan dan buga bugan tun jiya daya samu kan motar Abba ya dafe ya shiga sokoto sai yau din nan daya dawone. Shinema ya dauko mu aida tun dazun munzo babu mota a gida tana fadin hakan wani iri naji a zuciyana saidai na dake ban nuna komai ba a lokacin ga kowa sai cewa da nayi Allah sarki. Ashe yaya musa yana kasan da rabon zamu gana dashi ke nan wallahi ya dade dana ganshi a idanuna zakiko ganshi yanzun ai tafada cikin rashin damuwa ashe hakan yayiwa mama a zuciyarta. Kamar hadin baki sai gashi yayi sallama ya shigo dauke da Amir a hannunshi master na bayansu yake fadin wai ashe mutanen turan nannsun shigo garin nan basu fadawa mutane ba. Da sauri na mike zuwa gareshi ina masa murna da haduwan mu nan muka shiga hira dashi da master dani kafin yace ai nasan wanan wajen sosai wallahi mukan je mama ai wuri dayane da inda Bisi yake aiki. Cikin wani basarwa tace oh lalai amma da yake su bisi manyane ai wata kila ba zasu san juna tunda gidajen manya dabanne dana kanana. Ai wurin nan ba wasu gidaje dasukafi namu girma nasan sa sosai kuwa ba dan lagos din nan ba ai yanzu suna a old side ne mu kuma muna senior quarters so muna haduwa sosai dashi a wurin sallah jumma,a kona idi. Itace ma ta ganeshi ranan da muka fara haduwa dashi gaba dayan su daga mama har Aisha fuska suka bata Rukkaiya tace yanzu ana nufin mijinki babbane bisa ga bisi Zahra. Ni dai nayu murmushi naji ya musa yace ke kauce wallahi wanan babban officer ne da turawa suke ji dashi kina ganinsa nan nima gun wani friend dina naji dan kasar Cameron da muke hira. Don kinsan musulmai acan kansu dayane suna da kungiyansu ta musulmai kowa na sanin wani din basu da yawa sosai a can . Dan Allah ka rufawa mutane baki hakana da wanan shirmen naku mutum yana kwance ba lafiya kai sai bakin zuba kakeyi a kansa kamar baka damu ba. To mama kuma yanzu me nace don Allah fira kawai mukeyi na mijin zahra na can shine kuma laifi don Allah barin fita dama nazo inga jikin na Abbane kuma yana barci. Ina waje saika fito officer ya fada yana nufar kofan fita daga dakin da sauri nace yaya tsaya mu gana zaka wuce kuma bari na biyoka kada dai kaje masa yawo da mota mama ta fada. Bin bayansa nayi don duk banji dadin yanayin danaga dan uwa nawa ba sam don na fahinci akwai wani matsala mumuna a tare dashi dayake faruwa. Yaya musa nasa masa kira don baisan ina ma bayansa ba a lokacin har ya tura hannu a cikin aljihun wandonsa na jeans daya dan kode sai wata bakar rigan t,shirt a jikin duk tayi dauda yana tashin tsamin dauda. Ya jirani yana murmushi yace kanwata kinganki kuwa kinga yadda kuka koma kamar wasu taurari daga ke har mijin ki wallahi duk inda kuka bi dole a kalleku sau biyu. Kingani ko kina mamakine don yaga wani irin kallo da nake masa lokacin na mamaki karara a fuskana nace yaya meke faruwa ne don Allah na tambayeshi kamar zanyi kuka a lokacin Zahra ki bari kawai abubuwa ma da dama wallahi bari zamu zauna dake ai kiji amma nasan koma meye alhakine yake bin mu a yanzu amma sun kasa gane hakansu. Me kake fadine yaya na sake tambayan shi muryan mamane naji a bayan mu tana fadin to sarkin surutu tunda ka mayar da kanka haka yanzu ni kazo ka kaini gidan Ashibi.