Sashe 68
Tumfafiya Uwar Kwankwamai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kuka wiwi na fado part din ban tsaya ba sai a jikin ummah dake zaune a cikin yanayin damuwa da takaicin hali irin na da namiji da bamu da yadda zamuyi dasu a rayuwa sai zaman hakkuri. Kalah ummah batace min ba asalima kamar bata san inayi ba a lokaci sai can naji muryan ta tana fadin tun farko na fada maki kibi komai a hankali gidan nan don nima hakkurin nakeyi nakai ga samun ku a yanzu. Ban san me hjy maimuna ta fadawa Abban ku ba har ya hau haka da zafi kan wanan maganan don ba zanyi tunanen cewa hjy karima bace ta zugashi tunda a gaba data fuskanci rashin gaskiya a cikin maganan suka rikice dasu a wurin . Jiya kuma hjy maimuna a dakin Alh ta kwana bansan ya sukayi ba sai yau danaje gaisheshi yake min maganan wai tunda yaron nan kike so a turo shi yazo naso fahintar dashi gaskiya ya hauni da fadan hakan. Don haka komai ma ya faru nasan itace ta kullashi don taga ta wargaje min farin cikina a gidan nan dama kuma a cikin hakan muke da ita kullun. Salamu alaikum aka fada hjy karimace ke sallama daga kofan ta shigo itama ranta a bace yake lokacin da gani sin kwasa da Abba din kan zancen nawa ke nan. Au kuka kika tsaya yi kan wanan zancen ke ina kina son yaron dai ba shike nan ba saiki turoshi din kamar yadda ya fada ya bincikeshi don naga an zugashi sosai ya zugu kan zancen. Za a hana budurwa yin saurayine ko macece zata kira maza zuwa gareta ni wanan maganan banga ya kai wani abin tsayawa a tayar da jijiyon wuya ba hakan nan. Amma saina fahinci zancen da akwai lauje cikin nadi tun farko so kawai ake aga an kuntatawa wani a wanan zancen sam Alh baiyi tunane ba ta yaya mace zata fada ma zance ka tsaya ka haushi haka ka zauna wai shine gaskiya. A gaskiya hjy salma kinyi kokarin zama a haka cikin mutanen nan wallahi ni sam ba zan dauki wanan irin rainin wayau ba tunda bana wa yayanta hakan nan ni don me wasu mutanen basa tunanen mutuwansu ne wai ? Na fahinci komai a gidan nan yanzu don haka mu zuba dani da matan nan zata gane cewa karyan iskaci takeyi a baya yanzu ke zarah ki turo yaron wa Alh muji me zai masa. Shike nan kuwa ai wuya baya kashe bawa idan kayi hakkuri sai ya zamo maka alheri wata rana idan anyi hakanne don a tozarta mu na roki Allah ya mayar muna dashi alheri a rayuwan mu ummah ta fada. Insha Allah sai kunyi alfahari da hakan ban son ki nuna sarewa ko gazawa kan wanan zancen a yanzu ki daure din ga duk hukkuncin da zai yankewa yarnan a yanzu ki bita da addua da sadaka hakan ya zama mata alheri a rayuwan ta. Ina a jikin ummah gurfane na lafe ina jin abinda suke fadi a gaskiya ba zance ban son Ahmed ba da sunan so ba kuma zance bana son shi ba don halinshi dana sani a yanzu na jajircewa rayuwan shi. Haka kuma har in hakan ne meyasa ake son kashe mu da ran mune mu da mahaifiyar mune idan hakane gara nabarwa mama gidan na huta da wanan ukuban da suke nuna min ita da diyanta zaifi min sauki hakan ma. A ranan ina kuka na kira Ahmed a cikin tashin hankali na fada mai neman shi da Abba din keyi tunda umurni Abbah ya bani kan yin hakan don haka ya zama dole in kirashi in fada mai hakan. Shima a rude yake tambayana kome ya faru Abba din ke son ganin shi haka don yasan ba zancen soyayya a tsakanin sai mutunci da girmamawa. Ban iya mashi bayanin komai ba don banda karfin halin iya magana a lokacin don haka na kashe wayata kawai shima ya shiga tashin hankali irin wanda na shiga din a lokacin. Don haka da yamma karfe hudu ya fitowa sallah ya shirya ya fito zuwa gidan namu ba tare daya fadawa kowa inda zashi ba don baisan dalilin dayasa Abba din yake neman shi ba. A iya tunanen da zaiyi kan shawara guda ta yanke zancen shi shine kuma Abba zai mai iyaka dani kan ya rabu mai da diyanshine. Yanzu in an mai kashedi a kaina anya zai iya daukan hakan a yanzu kuwa yadda ya saba da yarinyar tana daukan shi da mutumci takar dan uwanta najini neshi a gareta yanzu don zarah ta zame mai wani bangare na rayuwan shi yanzu. Da wanan ire iren tunanen ya kawo har kofan get din gidan namu ya sauka ga mashin ya biya dan achaba kudin ya tafi shi kuma ya kalli gidan yana addua a zuciyarshi da neman kariya daga wurin ubangiji. Maigadi yaiwa magana don ya bude mashi get din gidan saida maigadin ya kalleshi da kyau duk da yasan shi yana zuwa suna gaisawa kuma yana dan maj ihisani daidai karfin shi kuma maigadin najin dadin hakan. Yaron arziki kaida kanka kake son ganin Alh yau anya bakayi karanbani ba kuwa ganin Alh fa sai manya ko manyan sai ka amsa sunan ka . Kai Ahmed din ya daga ya kalli gidan namu cikin second yadawo da kallonshi ga maigadin yana fadin yasan da zuwana don shi yace nazo yau din a daidai wanan lokacin. To to to aishike nan bari na tashi naje nai maka iso dashi din tunda yasan da zuwanka din ai dama na dauka ko zuwan kankane kayi da sai in baka shawara kawai ka hakura da ganin nasa ka koma inda ka fito zaifi ma sauki. Ya mike kata kata ya nufi kofan falon Abba din dake dan saye hakan ya nuna ba wanda zai shigo a lokacin gidan saishi da iyalinshi ko wasu shakikai nasa na jikin shi. Wucewan maigadin yasa Ahmed din kara tsarguwan kanshi duban jikin shi yayi yaga duk da yayi shiri irin wanda bai taba yin irinsa ba a jikin shi amma sai yaji ya raina kanshi a hakan. Bai dade ba maigadin ya dawo da sauri yana fadin yace kashigo daga ciki yasan da zuwan ka din haka yasa ya dufari inda yaga maigadin yaje duk dabai gama tabbatar dako nan ne hanyar shiga cikin gidan ba yadai sakai ya shiga da sallama a bakin shi . Sanyi da kamshine sukai mashi maraba da zuwa lokaci guda har saida ya dan lumshe idanun shi kadan don irin abinda yaji bai taba jin irinshi ba a rayuwa. Sallama yayi cikin muryanshi mai taushi da izza da gadara bai shigo ba saida aka amsa daga ciki tare da bashi izinin shiga falon shiga ciki ta hanyar fadin bissimillah shigo mana ciki . Yana dan dukar da kai yasa kafa ya shigo falon tare da dan gurfanawa can daga nisa yana fadin ina wuni Abbah shima Abban kai ya dago yana kallon dan matashin saurayin daya baiyana a gaban shi. Sau daya Ahmed din ya dago kai ya kalli Abba din kwarjinin Abban din yasashi saurin dukar da kanshi kasa da sauri ya fara gaida dattijon dake gaban nashi watau Abbah . Dan shirune ya biyo bayan hakan tsakanin su bayan gaisuwa kafin Abba ya kawar da shirun da fadin yaya sunan kane yaro Abba ya fada yana kallonshi ? Ahmed nake ya fada sunan mahaifinka fa Sama,ila ya bada amsa kafin ya kara noke kanshi kasa kamar kunkuru. Meye hadin ka da yata Abba ya tambayeshi tare da tsureshi da ido yana son jin amsan da zai bashi a lokacin lafin yasan hukuncin yankewa . Shiru Ahmed din yayi kafin Abba yace dashi bakaji band meye hadinka sa yata zarah ne ?. Abba wallahi ba komai tsakanina da ita sai alheri mun hadune a makaranta da ita ranan da wani matsala ya faru da ita kowa ya kewayeta yana kallon halinda take ciki na neman taimako. Naga rashin dacewan hakan tunda mace ce shine na taimaketa har ta dan farfado daga yanayin da take ciki din na fitan hankalinta. Tun wanan ranan ne hakan yasa muka shaku da juna muke zumunci da ita nake kuma taimaka mata wurin karatu don ina gaba dasu da shekara biyu a school din. Ka tabbatar wanan ne kawai atsakanin ku shi kawai na sani tsakanin mu Ahmed ya fada yana kara soke kanshi kasa. Abban yayi gyaran murya yace ji nan nayi binke nagane cewa duk makarantan nan dakai zarah ke mu,amula fiye da kowa sai kuma kawayen karatun ta mata da maza da kuke zama tare kuyi karatu dasu duk an binciko min hakan. A yau din nan nasa aka bincika min komai game daka saidai na samu feedback maikyau game da halayeb ka abu dayane ya daure min kai sai zancen mahaifin ka da akace ya barka tun kana shan nono bai kara waiwayo ka ba har yau din nan ? How do you see kaida baka tare da mahaifinka zakazo wanan irin gidan neman auren yata in baka alhalin kaima kanka baka san mahaifinka ba ? Ahmed ya lankwashe yan yatsun hannunshi cikin juna a ladabce ya dago kai ya kalli Abba din ya kara dukarda kanshi kasa yace. Abba saukin abindai bincike ya nunama cewa nidin ba shege bane mahaifina kuma da matsalace tsakanin shi da mahaifiyata da bata bishi zuwa kasansu ba yasashi fushin haka har ya wofitar dani na tashi mara galihu hakan baisa na watsar da tarbiyan da akeson samu ga ko wani daba . Zancen Zarah kuma ban taba tsayawa da zarah da sunan soyayya ba ko wani abu makamancin hakan a tsakanin mu ba don ko nasan nidin ba dan kowa bane ban kuma kai matsayin da zance zai nemi diya irin zarah ba. Don hakane alakan mu ya tsaya a iya mutumci kawai a tsakanin mu ba kuma sai don banson zarah din ba don sanin haka a gareni kawai da nayi. Kallonshi su Abba suka karayi da kyau shida dan uwanshi dake zaune falon a lokacin kafin yayan Abba din yace dashi sana,an me kakeyi a yanzu kuma meka karanta a karatun ka ? Wanan ma duk bai taso ba a yanzu ai Abba